• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, October 13, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasheeda Maisa’a, Mansurah da Muhibbat sun yi wa K-WAN kishiya, sun kafa ƙungiyar mata ‘yan fim

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
July 11, 2022
in Labarai
0
Wasu daga cikin shugabannin AKAFA lokacin da su ka gudanar da taro a gidan Mansurah Isah da ke Unguwar Badawa Layaout a Kano

Wasu daga cikin shugabannin AKAFA lokacin da su ka gudanar da taro a gidan Mansurah Isah da ke Unguwar Badawa Layaout a Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

WASU tsofaffin jarumai na  masana’antar Kannywood da kuma wasu daga cikin matasa da ake damawa da su sun kafa wata sabuwar ƙungiyar mata ‘yan fim mai suna ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA).

Ƙungiyar, wadda ta mata zalla ce, ta ƙunshi matan aure da zawarawa da ‘yan matan da su ke harkar fim ko su ka taɓa yi a baya.

Haka nan ƙungiyar za ta yi tafiya da ‘ya’ya da kuma jikokin duk wata jaruma waɗanda iyayen su su ka rasu, da ma waɗanda iyayen su ke da rai.

Sabuwar ƙungiyar dai ta na ƙarƙashin shugabancin Rashida Adamu Abdullahi (Maisa’a) da Mansurah Isah a matsayinf sakatariya, yayin da Muhibbat Abdussalam ta ke a matsayin jami’ar yaɗa labarai.

A lokacin da ta ke yi wa mujallar Fim bayani game da ƙungiyar, Muhibbat ta bayyana cewar, “Duk da cewar ita wannan ƙungiyar  sabuwa ce, amma za mu iya kiran ta ba sabuwa ba, tunda tamu ce ta ‘yan fim da su ka ƙunshi na baya da kuma na yanzu har da mawaƙa da matan aure da ma duk wata mace da ta taɓa yin fim ko waƙa ko wani aiki a cikin masana’antar Kannywwod.”

Ta ci gaba da cewa, “Mun kafa wannan ƙungiyar ne domin mu haɗa kan mu, mu ƙulla zumunci a tsakanin mu har ma da yaran mu da su ke tasowa, domin mu waɗanda mu ka yi fim a baya da masu yi a yanzu mu na da kishin junan mu, dukkan mu mana kallon mu a matsayin ‘yan’uwan juna, don haka mu ka kafa ƙungiyar domin ƙulla zumunci a tsakanin mu, kuma yaran mu su haɗu su san juna. Domin a yau idan aka ce ba ma raye ‘ya’yan mu za su ci gaba da zumunci a tsakanin su. Kuma a yanzu abin da mu ke shirin yi a cikin mu duk wadda ta ke cikin matsala za mu haɗu mu taimaki junan mu, domin mu magance matsalolin mu a tsakanin mu.”

Da wakilin mujallar Fim ya tambaye ta ko me ya bambamta wannan sabuwar ƙungiyar tasu d sauran ƙungiyoyin mata ‘yan fim da aka yi a baya kuwa, sai ta ce, ” A gaskiya wannan ƙungiyar ta ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA) ta na da bambanci sosai da na baya, saboda ita wannan ba mu fara ba sai da mu ka yi wa juna alƙawarin cewa ba cuta babu cutarwa, kuma ba za mu bar wani ya cuci wani ba. Don haka za mu yi tafiya ta taimakon juna ne a tsakanin mu da kuma ƙulla zumunci.”

Ƙungiyar dai zuwa yanzu ta na da mambobi da su ka haɗa da Mansurah Isah, Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a), Muhibbat Abdulsalam, Samira Ahmad, Rahama Hassan, Asma’u Sani, Jamila Gamdare, Fati Slow, Fauziyya Sani (Maikyau), Fati S.U. Garba, Amal Umar, Maryam Isah Abubakar (Ceeter), Hadiza Gabon, Ruƙayya Umar Santa (Dawayya), Ummi Gombe, Halima Atete, Aishatul Humaira, Fati Washa, Momee Gombe, Fati KK, da sauran su. 

Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa a yanzu haka ƙungiyar za ta gudanar da  babban taron Sallah nan da sati biyu masu zuwa domin tabbatar da kafuwar ta.

A yanzu kenan an yi wa Ƙungiyar Matan Kannywood ta Nijeria, wato K-WAN, kishiya. A da K-WAN, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Hauwa A. Bello, ita kaɗai ƙungiyar mata ‘yan fim a masana’antar.

Loading

Tags: AKAFAHauwa A. BelloK-WANMansurah IsahMuhibbat AbdulsalamRasheeda Adamu Abdullahi Maisa'a
Previous Post

Rasuwar Nura Mustapha Waye ta sa mutanen da ba su magana da juna sun shirya, inji Lawan Ahmad

Next Post

Matan Kannywood ne matsalar masana’antar, inji dattijo Auwalu Marshall

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Matan Kannywood a taron da aka yi a Kano jiya

Matan Kannywood ne matsalar masana'antar, inji dattijo Auwalu Marshall

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!