• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, July 23, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

PDP kaɗai ce jam’iyya a Nijeriya, APC na kakarin mutuwa – Atiku

by DAGA WAKILIN MU
November 10, 2022
in Nijeriya
0
Atiku Abubakar ya na amsar gaisuwa daga magoya bayan sa

Atiku Abubakar ya na amsar gaisuwa daga magoya bayan sa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ƊAN takarar zaɓen shugaban ƙasa na PDP a 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa jam’iyyar sa kaɗai ce mai wani karsashin lashe zaɓe a yanzu.

Ya ce APC, jam’iyyar da ta kassara ƙasar nan har ta kusa durƙusar da ita, za ta ɓace, a neme ta a rasa bayan zaɓen 2023.

Atiku ya yi wannan tsinkayen lokacin da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen sa ya ƙaddamar da Kwamitin Matasa na Yaƙin Neman Zaɓen PDP (PDP-NYCN) a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce: “Maganar gaskiya, PDP kaɗai ce jam’iyya a Nijeriya. APC wani gungu ne kawai, kuma za mu yi nasarar korar su a ranar zaɓe. Mutuwa murus jam”iyyar za ta yi idan mu ka kore su daga kan mulki.” 

Haka kuma ya shaida wa matasa a wurin ƙaddamarwar: “PDP za ta bai wa ɗimbin matasa dama a ƙasar nan, ba tare da yin la’akari ko nuna bambancin gida, arziki ko talaucin iyayen kowane matashi ba. Ko ɗan talaka ko ɗan wanene kai, PDP za ta taimake ka har ka cimma kyakkyawan ƙudirin ka a rayuwa.

“Kai, ko da Atiku ya kammala wa’adin sa ya sauka, to wani Atiku ɗin zai hau.” 

Tsohon mataimakin shugaban kasar daga 1999 zuwa 2007 ya hori PDP-NYCN da su shiga ko’ina a faɗin ƙasar nan su wayar da kan matasa kafin zaɓe.

Ya ce: “Ku je ku ba su tabbaci, ku ƙarfafa masu guiwa da zukata. Ku nuna masu cewa duk matsalar da APC ta jefa ƙasar nan, har yanzu ana fatan maida ta kan turbar bunƙasa. Ku ɗauki wannan aiki da gaske, ku jajirce. Shi ne damar da za ku samu nan gaba, kuma shi ne damar iyalin ku da ƙasar ku.

“Saboda haka ina umartar ku da yin aiki tuƙuru domin ku ceto ƙasar nan, ta hanyar haɗa kan dukkan ‘yan Nijeriya, musamman musamman magoya bayan PDP.”

Loading

Tags: APCAtiku Abubakarmatasan PDPPDPZaɓen 2023
Previous Post

Walima: Nihal ‘yar Fauziyya Maikyau ta cika shekara 6 a duniya

Next Post

Dattawan Arewa sun ƙalubalanci Gwamnan Binuwai kan kalaman ƙyamar Fulani

Related Posts

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim
Nijeriya

Sanatan Kaduna: Yerima Shettima za mu yi, inji ‘yan fim

July 15, 2025
Nijeriya

Tinubu yana goyon bayan Ƙananan Hukumomi su ci gashin kan su – Minista

July 11, 2025
Nijeriya

Shirin Sabunta Fata na Tinubu yana samar da damarmakin cigaba — Minista

July 10, 2025
Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista
Nijeriya

Sauye-sauyen Tinubu suna taimaka wa farfaɗowar tattalin arzikin Nijeriya — Minista

July 10, 2025
Ministoci za su fara gabatar da rahoton ayyuka a taron manema labarai
Nijeriya

Tinubu ba zai yarda hayaniyar siyasar 2027 ta ɗauke masa hankali ba – Minista

July 8, 2025
Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano
Nijeriya

Ƙungiyoyi sun buƙaci bayanai daga ‘yan sanda kan harin da aka kai fadar Sarkin Kano

July 8, 2025
Next Post
Gwamna Samuel Ortom

Dattawan Arewa sun ƙalubalanci Gwamnan Binuwai kan kalaman ƙyamar Fulani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!