TSOHUWAR jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, Fauziyya Sani (Maikyau), ta shirya wata ƙwarya-ƙwaryar walima ta murnar cikar ‘yar ta Fatima Yakubu (Nihal) shekara shida da zuwan ta duniya.

An yi taron a gidan Fauziyya da ke Kano a ranar Talata, 8 ga Nuwamba, 2022, kuma ya kasance na yara ne sai wasu ƙawayen ta kaɗan da ta gayyata.
An yi wasanni na yara tare da raba kyaututtuka, aka ci abinci da abin sha tare da rufe taron da yanka kek.


