• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Hukumar tace finafinai ta ƙasa ta hana sayar da fassarar finafinan Indiya

by DAGA ABBA MUHAMMAD
November 16, 2022
in Labarai
0
Alhaji Umar G. Fage

Alhaji Umar G. Fage

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Tace Finafinai Da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta haramta bugawa da fassarawa da kuma sayar da finafinan da ake fassaro su daga harsunan ƙasashen waje irin Indiya a dukkan faɗin ƙasar nan.

Jami’in hukumar mai kula da shiyyar Arewa-maso-yamma, Alhaji Umar G. Fage, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim a ofishin sa da ke Kano.

Tuni dai finafinan ƙasashen ƙetare da ake fassarawa zuwa Hausa, musamman na Indiya, su ka cika birni da ƙauye a Arewa. 

To amma Alhaji Umar ya ce: “Shi wannan abu ba sabo ba ne, da man dokar Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa ta 1993 ta samar da hakan, don haka ya na daga cikin dokokin hukumar hana wannan fassarar, musamman a wannan lokacin da mu ke samun ƙorafi daga jama’a a kan yadda wannan fassarar ta ke gurɓata al’adun mu da kuma yaren mu wanda za ka ji ana wasu kalamai na ɓata tarbiyya ko ɓata shi kan sa yaren na Hausa.

“Ita wannan hukumar an kafa ta ne domin ta kare al’adu, addini da kuma yarukan da ke ƙasar nan, don haka mu ka duba yadda wannan fassarar ta ke kawo illa ga yaren mu da al’adun mu.

“Sannan ita kan ta masana’antar Kannywood ta samu koma-baya ta dalilin wannan fassarar da ake yi, don haka a yanzu kasuwancin finafinan Hausa ya durƙushe saboda zuwan fassarar Indiya.”

Alhaji Umar ya yi nuni da cewa haƙƙin hukumar sa ne ta tashi tsaye domin ta yaƙi wannan fassarar, tunda da man haramtacciya ce a hukumar, “don su na satar fasahar wasu ne su na sayarwa ba tare da haƙƙin su ba.”

Ya tunatar da cewa da man duk wani fim da za a yi a ƙasar nan sai hukumar ta ba da izini ta yarda a shiga da shi kasuwa ko a nuna shi a sinima. 

“To kuma duk wannan fassarar da su ke yi bai hau wannan mataki ba, don haka mu a wajen mu haramtacce ne.”

Ya ƙara da cewa, “A matsayin mu na hukuma shi ya sa mu ka ɗauki mataki, don haka tun a satin da ya wuce mu ka shiga kamen duk wani da ya saka kan sa a cikin wannan harkar ta fassarar Indiya, kuma a yanzu mun kama mutum uku, su na hannun hukuma, wanda a yanzu mu na ci gaba da neman wasu mutane 14, kuma da zarar an kama su za a gurfanar da su a gaban kotu domin a yi musu shari’a.

“Don haka a yanzu ma mun tura babban ofishin mu na Abuja don ya sanar da lauyoyi da kuma jin shawarar da za su bayar a game da shari’ar.”

Alhaji Umar ya ce yaƙi da waɗannan masu satar basirar “ba abu ne mai sauƙi ba”, ya ce: “Ko a kan Titin IBB a nan Kano da mutanen mu su ka je aiki sun samu turjiya daga su masu wannan fassarar inda har su ka fasa mana mota.

“Don haka ne mu ka nemi jin ta bakin lauyoyi a kan masu wannan aiki tunda a yanzu mutane uku an kama su ana tsare da su a sashin binciken manyan laifuka na ofishin shiyya ta ɗaya (ta ‘yan sanda) da ke nan Kano.”

Jami’in ya yi kira ga jama’a da su ba hukumar haɗin kai, “saboda wannan aikin na duka jama’a ne, domin kare ƙasar mu daga wannan baƙin al’adun da su ke lalata yaren mu da kuma tarbiyyar yaran mu.”

Loading

Tags: fassaraharamciHukumar Tace Finafinai ta ƘasaIndiyakarya dokaNFVCBtace finafinaiUmar G. Fage
Previous Post

Shawarwari ga sababbin zawarawa

Next Post

Abin da ya sa na zama mawaƙin siyasa – Bashir Ɗandago

Related Posts

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 
Labarai

MOPPAN ta yi wa al’ummar Kano ta’aziyyar Aminu Ɗantata 

June 29, 2025
Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Next Post
Malam Bashir Ɗandago

Abin da ya sa na zama mawaƙin siyasa - Bashir Ɗandago

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!