HUKUMAR Hisbah ta Jihar Kano ta gurfanar da mawaƙi Al-Ameen G-Fresh da ya shahara a soshiyal midiya bisa zargin wasa da sallah a wani faifan bidiyo.
A lokacin da jami’an na Hisbah su ka gurfanar da shi a ofishin su bayan sun kamo shi, sun yi masa nasiha tare da ba shi shawarar ya koma makaranta, inda kuma nan take ya miƙa wuya.
Mujallar Fim ta gano cewa kama mawaƙin dai ya biyo bayan wallafa wani faifan bidiyo da ya ɗora a TikTok inda ya ke sallah amma maimakon ya karanta Ƙulhuwallahu sau uku kamar yadda ya nuna, sai ya zama ya kasa karanta ko guda ɗaya. Hukumar ta ga yin hakan wasa da addini ne.