A SAFIYAR yau Alhamis, 16 ga Maris, 2023 Allah ya yi wa mahaifiyar darakta a Kannywood, Sadiq Hussaini Jeep, rasuwa a gidan ta da ke Fagge layin ‘yan taya, Kano.
Hajiya A’isha Salisu, mai shekara 85 a duniya, ta rasu ne bayan ta sha fama da rashin lafiya.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya takwas – maza huɗu mata huɗu. Daga cikin ‘ya’yan nata ne akwai darakta Sadiq Jeep.
An yi jana’izar ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar da misalin karfe 10 na safe. ‘Yan fim da dama ne sun halarta, kuma sun haɗa da Jamilu Ahmad Yakasai da Sani Sule Katsina.
Da fatan Allah ya jiƙan Hajiya A’isha, ya sa Aljanna ce makomar ta, amin.
![]()







