MAƘIRƘIRIN shahararren wasan kwaikwayon nan mai suna ‘Sawun Keke’ da aka riƙa nunawa a gidan talabijin na Jihar Kaduna (KSTV) a shekarun baya, Malam Ashiru Sani Bazanga, ya bayyana rasuwar jarumar shirin, wato Hajiya Balaraba Tanko, a matsayin mutuwar da ta buge shi fiye da duk yadda ake tsammani.
Bazanga, wanda shi ne jarumin diramar ta mako-mako kuma har yau ɗin nan ana yi masa laƙabi da ‘Sawun Keke’, ya ce: “Da na ji rasuwar ta, tamkar mata ta uwargida na ne na ji ta rasu, tamkar ya ta da mu ke uwa ɗaya uba ɗaya na ji ta rasu! Rasuwar Balaraba ya buge ni fiye da tunani.”
Ita dai Hajiya Balaraba Tanko, wadda sunan ta na yanka Sa’adatu Abubakar, Allah ya yi mata rasuwa ne a daren shekaranjiya Litinin, 24 ga Afrilu, 2023.
Tsohuwar jarumar, wadda ta yi fice da sunan Saro a cikin shirin na ‘Sawun Keke’, tsohuwar ma’aikaciyar Hukumar Rediyo da Talbijin ta Jihar Kaduna (KSMC) ce.
Hajiya Balaraba ta rasu da misalin ƙarfe 3:00 na dare a gidan ta da ke Tudun Wada, Kaduna, bayan ta yi fama da jinyar shekara ɗaya da wata ɗaya.
Marigayiyar, mai kimanin shekara 73, ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar – mata biyu, maza uku.

Malam Ashiru Sani Bazanga ya faɗa wa mujallar Fim tarihin dangantakar sa da ita, ya ce, “To ita dai Hajiya Balaraba Tanko, ko in ce Saro a cikin shiri na na ‘Sawun Keke’, wadda ta ke fitowa a mata ta, ba ita ba ce Saro ta farko; Saro ta farko sunan ta Bilkisu Mohammed. A lokacin da mu ka fara wasan kwaikwayon ta na da ciki, kuma ga shi ita na sa a matsayin Saro, sai Allah ya kawo mata naƙuda na haihuwa bayan mun yi rikodin kamar guda biyu, to a na ukun ba mu je da ita ba saboda wannan larurar, kuma idan ta haihu mu na tunanin za ta daɗe ba ta dawo aiki ba, saboda mu na yin aikin a matsayin ma’aikata ne na Jihar Kaduna, a gidan rediyo da talbijin na Jihar Kaduna, KSMC.
“Sai mu ka yi shawara a bar wa Balaraba Tanko. Ita da kan ta Bilkisun ita ta amince da hakan a sa Balaraba Tanko a makwafin ta, in ta dawo, lokacin ta gama hidimonin haihuwar ta, sai ta dawo ta ci gaba da aikin ta, amma ba a matsayin Saro ba.
“Ita kuma Balaraba da ta hau shirin sai ya fi dacewa da ita, domin haziƙa ce a wasan kwaikwayo da jarunta.”
Bazanga ya ci gaba da cewa, “Balaraba aminiya ta ce, kuma ina ɗaukar ta da girma da girmamawa, saboda matar maigidan mu ce, shugaba ne a Sashen Yaɗa Labarai, musamman babban edita ne na Sashen Watsa Labarai na rediyo da talbijin na KSMC, Alhaji Muhammadu Ɗantankon Sa’i. Ita ce uwargidan sa. Ka ga akwai girma da girmamawa tsakani na da ita tunda matar maigida na ce.
“Sannan ga dangantaka irin na kusanta, wadda na ke cewa yaya ta a cikin shirin ‘Sawun Keke’, Hajiya Hadiza Sulaiman, babbar aminiyar ta ce, kuma Hajiya Hadiza yaya ta ce, kuma mu na da dangantaka na zumunci ta ɓangaren uwa da ita a matsayin ta na ‘yar Zariya, ‘yar Unguwar Liman.
“Kuma Balaraba Tanko har mu ka gama wasan kwaikwayo ban taɓa ganin wani abu na cikas game da ita ba.
“Kuma Allah ya sani, da na ji rasuwar ta tamkar mata ta uwargida na ne na ji ta rasu, tamkar ya ta da mu ke uwa ɗaya uba ɗaya na ji ta rasu! Rasuwar Balaraba ya buge ni fiye da tunani.
“Balaraba ita ce ta ashirin da biyu ko da uku da su ka rasu a cikin ‘yan wasan kwaikwayo na.
“Allah ya jiƙan ta da rahama, ya gafarta mata.”
A nata ɓangaren, babbar ‘yar marigayiyar, Hajiya Halima, ta shaida wa mujallar Fim cewa Hajiya ta kai tsawon shekara takwas rabon ta da wasan kwaikwayo.
Da wakilin mu ya nemi ta ce wani abu game da rasuwar mahaifiyar tata, sai ta ce ba za ta iya cewa komai ba, don za ta yi kuka.
Amma aminiyar Hajiya Halima ɗin kuma abokiyar aikin ta, Hajiya Zara Mimi Ahmed, ta faɗi wani abu a madadin aminiyar tata, inda ta ce, “Gaskiya abin da zan iya cewa game da Hajiya Balaraba Tanko, mace ce mai haba-haba da mutane, kamar yadda ka gani cikin gidan nan cike ya ke maƙil da mutane. Ranar da aka jana’izar ya sai ka yi mamaki, don za ka ɗauka wani sarki ne ya rasu.
“Wallahi Allah ya ba ta, don ta na da mutane sosai. Mace ce mai fara’a, mai wasa da mutane sosai. Ita babu abin da ya yi mata zafi, don har surukan ta ba ta bari ba. Allah ya ba ta wannan. Gaskiya mun gode wa Allah. Allah ya jiƙan ta da rahama.”
To amin ya Allah.
![]()







