AN yi kira ga ‘yan Kannywood, musamman na Jihar Kaduna, da su yi amfani da irin wannan lokaci na shagulgulan Sallah don sada zumunci tare da ziyartar juna kamar yadda masana’antar ta ke a baya.
Sanannen furodusa a Kannywood, Alhaji Abubakar Musa Anka, shi ne ya bayyana hakan a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim don miƙa saƙon barka da Sallah.
Anka, wanda mazaunin Kaduna ne, ya ce: “Ina yi wa kowa barka da Sallah. Haƙiƙa masana’antar Kannywood a yanzu ta canza, ba kamar ta baya ba. A baya an fi mutunta juna tare da sada zumunci, musamman a lokutan shagulgulan Sallah.”
Furodusan ya ci gaba da cewa, “A baya a kan shirya wasannin Sallah. A wannan lokacin ne za a sada zumunci na haƙiƙa, domin sai ka haɗu da wanda ku ka daɗe ba ku haɗu ba. Za a ƙulla abubuwan alkhairi duk a irin wannan lokacin. A wasu lokutan kuma, har ƙulla kasuwanci da kuma ƙulla abubuwan da za su kawo wa masana’antar cigaba. Amma yanzu wasan Sallah ya zama tarihi a Kaduna.

“Amma a wannan zamanin abubuwan sun koma duk abin da za a aiwatar sai dai a yi don a burge wani ko kuma wata. Masana’atar ta koma harkar fadanci kawai, babu ganin mutuncin juna, sai wanda ke ba ka. Wannan ba daidai ba ne.”
Anka ya yi kira ga ‘yan’uwan sa na Kannywood, musamman shugabanni, da su yi ƙoƙari wajen ganin an dawo da martabar masana’antar, an dawo da zumuncin da ake yi kamar da can baya.
Ya ƙara da cewa lallai ya kamata manyan furodusoshin Jihar Kaduna su dawo da ƙarfin su, “domin wallahi duk sun yi bacci, babu mai motsi a cikin su. Sannan kuma su yi ƙoƙari wajen dawo da irin shagulgulan Sallah da ake yi a baya.”
Anka ya ce, “Zan yi amfanin da wannan dama in miƙa saƙon barka da Sallah ga ɗaukacin ma’aikatan mujallar Fim, musamman shugaban ta, Malam Ibrahim Sheme, abokai na fudusoshin Kannywood, daraktoci, jarumai da duk wani da ke cikin masana’antar.
“Allah ya maimaita mana, ya kuma karɓi dukkan ibadun mu. Allah ya ƙara haɗa kan ‘yan Kannywood, ya kuma sa martabar ta ta dawo kamar yadda ta ke a baya.”