• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, May 14, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda zan taimaki Kannywood da muƙami na a Arewa 24 – Wassh Waziri Hong

by DAGA ABBA MUHAMMAD
July 24, 2023
in Labarai
0
Wassh Waziri Hong (a hagu) tare da Sabi'u Gidaje

Wassh Waziri Hong (a hagu) tare da Sabi'u Gidaje

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FURODUSA kuma jarumi a Kannywood da Nollywood, Wassh Waziri Hong, ya bayyana yadda aka yi ya zama babban furodusa (Senior Executive Producer) a tashar talbijin ta Arewa 24.

Wassh ya yi wa mujallar Fim wannan bayanin ne a wurin taron da kamfanin Gidaje Films and Sound Studio ya shirya da furodusoshin jihar Kaduna a ranar Asabar, 22 ga Yuli, 2023.

Ya ce, “Alhamdu lillah, alhamdu lillah, alhamdu lillah. Wannan muƙami na ‘Senior Executive Producer’, ba ni aka ba wa ba, ba Jihar Kaduna ba, Arewa gaba ɗaya aka ba. Tunda wanda ya sauka ya bar wurin, ba ɗan Arewa ba ne, akwai waɗanda su ka fi ni ilimi, akwai waɗanda su ka fi ni jajircewa a wannan sana’ar, akwai waɗanda sun fi ni cancanta a ba su, ko daga cikin Arewa 24 ɗin akwai wanda ya kamata a ba su, amma Allah ya ba ni. Ni abin da zan ce kawai alhamdu lillah.

“Sannan kuma, wannan abin ba zan ce nema aka yi ba, saboda wanda ke wurin oga na ne zai tafi. A lokacin da na ji labarin, sai ya ce min in ba shi shawara, sai na ba shi mutane kusan takwas, a cikin takwas ɗin, sai mutum huɗu su ka ba da shawarar ni ma a ba ni, sai aka kira ni aka ce in zo ga abin da su ke tunani, ko ina da sha’awa. Ni kuma ina ta mamaki, ni akto ne, ina acting a Arewa 24 a ‘Kwana Casa’in’, ina fitowa a mataimakin gwamna, don haka ban ma yi tunanin in zo in nema ba, sai aka kira ni, kuma kiran daga sama ne.” 

Mahalarta taron

Wassh ya ci gaba da cewa, “Ina zuwa mu ka yi ‘interview’ na farko, mu ka yi na biyu, kawai sai na ji an ce min ‘congratulations’ aka tura min takarda aka ce kai aka zaɓa. 

“Kuma ba ma abin da na ke tunani ba ne; a tunani na za a ba ni furodusa na ‘Kwana Casa’in’ ne, sai kawai na ga an ba ni ‘Senior Executive Producer’, kuma ‘permanent job’. 

“Ana ba ni kawai, na farko sai na yi sujuda, sai na fashe da kuka, na ce wai me ke faruwa? Ko jiya na yi magana da wani, na ce ko na kusa mutuwa ne? Akwai matsala da na ke ciki, na kira sunan Allah na yi masa kirari. Ina zuwa Qausain TV, sai aka kira ni, inda na ke tunanin ba zan samu maimako ba, aka kira ni aka ce ya na ke so a yi? Ni ban kira su ba, ana cikin haka wani kira ni, ya ce min in turo da ‘size’ ɗin kaya na, yau ɗin nan kuma ina zuwa wurin nan kuma sai ga wani ya kawo min manyan riguna, ina ganin aƙalla sun kai kala biyar. Sani Danja ya yi min ɗinki wanda zan sa na wata ɗaya, haka ake tura min abubuwa wanda ban ma san su ba. Yanzu haka tayoyin mota na wani ne ya canza min. Ire-iren abubuwan nan, sai na ga ashe taimako ya na da rana, kuma da ma ban fasa ba.

“Kuma da zan bar Yola iya abin da mahaifiya ta ta ce min ka tabbata ka yi kyauta kullum, kuma ka tabbata ka yi don Allah. Kuma in-sha Allah zan ci gaba da yi har in mutu.”

A ɓangaren amfana da Kannywood za ta samu da wannan muƙami da Wassh ya samu, cewa ya yi, “Allah kaɗai ya sani, saboda mace mai ciki sai ta haihu sannan za a gane; ana iya cewa mace za ta haifa, sai a ga ta haifi ‘yan biyu duk maza. Ni dai kowa ya san ina siyan kayan aiki don in taimaka wa mutane, Yanzu haka ina ga kyamarori guda biyu da na aje, da na yi, bare ma yanzu, to zai ƙaru. Allah ya ba mu ikon yin abin da da mutane sun ji suna na su fashe da kuka.

“Ina kuma kira ga mutanen mu da a ji tsoron Allah. Duk abin ka ke yi, ka ji tsoron Allah, musamman maganar kan-ta-waye, in dai ka na jin tsoron Allah, ba za ka yi ba. Yanzu maganar fim ya kwanta, ina fatan zuwa na wannan ofis Allah ya ba ni damar da zan ɗan gyara shi. 

“Kano za ni. Abba El-Mustapha aboki na ne, mu na ‘Kwana Casa’in’, da mu ka gama ni na kai shi tashar mota, amma ga shi a cikin wata guda mun samu muƙamai. Sani Danja aboki na ne, mu na sa ran zai samu kwamishina. Allah ya sa mu dace. 

“Allah ya saka wa Fim Magazine da alkhairi, Allah ya ƙara mata daraja da ɗaukaka.”

Taron da kamfanin Gidaje ya shirya, ya shirya ne don muƙamin da Wassh ya naɗa Sabi’u M. Gidaje a matsayin karɓar finafinai a hannun furodusoshi zuwa gidan talbijin, bayan ya samu muƙami a Arewa 24.

Daga hagu: Haruna Gidaje, Murtala Aniya, Hamisu Kudan, Sabi’u Gidaje, Rabi’u Koli, Musa Muhammad Abdullahi, Maiwada Gwanki da Ibrahim Yalawa bayan taron

Wannan dalili ya sa su ka kira taro da furodusoshin Jihar Kaduna don sanar masu da kuma wannan ci-gaba da aka samu.

An fara taron da misalin ƙarfe 12:00 na rana a makarantar gwamnati ta ‘yan mata da ke Tudun Nufawa.

Wassh Waziri Hong ya yi wa halarta taron bayanin abin da ya tara mutane, ya ce ya naɗa Sabi’u Gidaje ne muƙamin wanda zai riƙa karɓar finafinai a hannun furodusoshi, shi kuma ya gabatar da su a gaban sa a matsayin sa na ‘Senior Executive Producer’ a Arewa 24. Daga nan kuma su za su duba, idan fim ɗin ya yi, sai su biya.

Sannan Wassh ya ce a wannan lokacin duk wanda bai yi arziki ba, shi ya so, domin akwai tsare-tsaren da za a yi wanda mutane za su samu arziki. 

Bayan ya gama jawabin sa, sai aka ba sauran mutane dama don su tofa albarkacin bakin su.

Da farko, Malam Musa Muhammad Abdullahi shi ne wanda ya fara magana, inda ya nuna farin cikin sa game da ci-gaban da aka samu, sannan ya ba da shawarar ya kamata a haɗa kai, domin sai da haɗin kai za a samu nasara a duk al’amurra.

A taron, mahalarta irin su Hajiya Fatima Lamaj, Shehu Garba PS, Abayomi Alade, Murtala Aniya, Dikko Yakubu, Femi Koka, Fati Haske duk sun nuna farin cikin su tare da ba da shawarwari. 

Daga nan kuma sai aka rantsar da Sabi’u Gidaje. Amma kafin a rantsar da shi, sai da lauyan Wassh ya karanta takardar yarjejeniya a tsakanin kamfanin su Sabi’u, wato Gidaje Films and Sound Studio da kuma Huba TV Africa. Sannan Sabi’u ya saka hannu, shi ma Wassh ya saka hannu.

Bayan wannan, sai aka ba sauran mahalarta taron dama su ma don su ce wani abu. Su ma kuma sun yi addu’o’i, sannan sun ba da shawarwari.

An tashi daga taron da misalin ƙarfe 3:35 na yamma.

Bayan taron, Sabi’u Gidaje ya yi wa Allah godiya da muƙamin da ya samu a yayin  tattaunawar sa da mujallar Fim, inda ya ce, “Alhamdu lillah, alhamdu lillah, alhamdu lillah. A lokacin da oga na, Sir Wassh, ya faɗa min wannan muƙami da ya ba ni, tsakani da Allah na ji daɗi, kuma na yi wa Allah godiya, sannan na faɗa wa mahaifiya ta, ita ma ta yi murna. Babu abin da zan ce sai dai godiya.”

Gidaje ya ci gaba da cewa, “Ina kira ga yayye na, iyayen gida na da ƙanne na da su sani, wannan muƙami da Allah ya ba ni aiki ne a gare mu baki ɗaya. Saboda ci-gaban mutum ɗaya bai kawo ci-gaba, wannan aiki ne gagarumi a tsakanin mu. Don Allah mu haɗa kai, mu faɗi tare, mu tashi tare. Kuma don Allah duk abin da na yi ba daidai ba, a kira ni a faɗa min. 

“Sannan ina yi kowa albishiri, ba ‘yan Kannywood ba kawai, har da ‘yan kallo, za a samu ci-gaba a Arewa 24, yanzu za su fara ganin sababbin finafinai masu kyau in-sha Allah.”

Sabi’u Gidaje riƙe da takardar yarjejeniya bayan an rantsar da shi

Sai dai kuma wani abin mamaki, taron an shirya shi ne domin furodusoshi, amma kuma a cikin kashi ɗari na furodusoshin Jihar Kaduna, ko kashi ɗaya ba su halarta ba, duk da irin yaɗa sanarwar taron da aka yi.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun haɗa da Yusuf Gidaje, Sulaiman Sha’ani, Nura MC Khan, Yaros Khan, Zaharaddin Mando, Tukur Musa Ɗankulla, Ubale Shu’aibu, Jameel Aji, Malam Musa Toron Giwa, Hamisu Kudan, da Abdul SD.

Loading

Previous Post

Hotuna: Mahaifiyar El-Mustapha ta sanya masa albarka kan muƙamin da ya samu a gwamnatin Kano

Next Post

Masoya na ku daina zagin Davido tunda ya goge bidiyon cin zarafin Musulunci – Ali Nuhu

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Daga hagu: Davido, Ali Nuhu, da Jamilu Yakasai

Masoya na ku daina zagin Davido tunda ya goge bidiyon cin zarafin Musulunci - Ali Nuhu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!