BABBAN Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana goyon baya ga matakin da Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jahar Kano ta ɗauka na ɗage lasisin dukkan masu sana’ar fim a jihar kwanan baya.
Daurawa ya yi kalamin ne a lokacin da Babban Sakataren Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya kai ziyara masa ziyara a ofishin sa a ranar Laraba da ta gabata, 9 ga Agusta, 2023 don jaddada aniyar sa ta yin aiki da duk hukumomin da su ke da alaƙar aiki da hukumar sa domin cimma nasarorin da ya sa a gaba.
Tun da aka naɗa shi shugaban hukumar kwanan nan, ya na ci gaba da ziyarar ƙulla alaƙa da hukumomin tsaro ga kula da al’amuran da su ka shafi jama’a.

A lokacin ziyarar da ya kai wa Darakta-Janar na Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, El-Mustapha ya gabatar da kan sa tare da nufin kulla alaƙar aiki a tsakanin hukumomin biyu.
A jawabin sa, ya ce: “Hukumar ta tace finafinan ta kawo wa Hukumar Hisbah ziyara ne domin neman shawarwari tare da ƙulla alaƙar aiki ta yadda hukumomin biyu za su samu fahimtar juna tare da kawo wa Jihar Kano cigaba a fannin tarbiyya tare da bunƙasar al’adu wanda kawo yanzu su ke neman zama tarihi.”
Ya kuma gode wa shugaban Hukumar Hisbah ɗin saboda lokacin da ya ba su na ziyarar tare da karrama su da aka yi.
A lokacin da ya ke mayar da jawabin sa, Sheikh Daurawa ya nuna farin ciki da zirar da aka kai masu, kuma ya gode wa El-Mustapha bisa yadda hukumar sa ta ƙwace shaidar izinin yin aiki ga duk wani abokin hulɗar ta, ya ce hakan zai taimaka tare da bai wa hukumar damar tantancewa tare da cire baragurbi a cikin masana’antar.
Daurawa ya ƙara da cewa, “Hakika akwai gurare da dama da ya kamata Hukumar Tace Finafinan ta kalla domin a yi masu gyara. Ga misali, yadda ake samar da gidajen kallo da gidajen nishaɗi, da kuma batun shigo da ƙananan yara da kuma ɓangaren waƙoƙi da raye-raye a tsakanin maza da mata.
Ya ce saboda haka Hukumar Hisbah za ta haɗa hannu da hukumar domin kawo sauyi tare da tsaftace ɓangarorin ta yadda jihar za ta samu cigaba.
Ya kuma yi alƙawarin ba da wakilci daga Hukumar Hisbah domin lura da yadda ake tace finafinai don taimaka wa hukumar ta yadda za ta inganta ayyukan ta tare da cimma nasarorin da ta sa a gaba.

Haka nan Daurawa ya shawarci El-Mustapha da ya kafa wani sashe da zai riƙa lura da harkokin mawaƙa masu yabon Annabi Muhammadu (S.A.W) da ‘yan TikTok, da masu harkokin YouTube domin kawo gyara tare da tsaftace kalaman su ta yadda za su yi daidai da shari’ar Musulunci.
Ya ce: “Don haka mun ƙudiri aniyar bai wa Hukumar Tace Finafinai dukkan gudunmawa tare da goyon baya ta yadda Jihar Kano da al’ummar ta za su samu cigaba.”
Comments 1