• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Za a karrama Ali Nuhu da Rikadawa da Kyautar Gwarzayen Arewa ta 2023

by DAGA ALI KANO
September 8, 2023
in Labarai
0
Ali Nuhu (a dama) da Rabi'u Rikadawa

Ali Nuhu (a dama) da Rabi'u Rikadawa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMAN Kannywood biyu, Ali Nuhu da Rabi’u Rikadawa, su na daga cikin gwarzaye ‘yan Arewa waɗanda za a karrama da kyautar girmamawa mai suna ‘2023 Arewa Heroes’ and Philanthropic Award of Excellence’. 

Mujallar Fim ta ambato labarin da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya bayar cewar jaruman su na daga cikin waɗansu fitattun mutanen da masu shirya bikin su ka fitar a yau Juma’a a Abuja. 

Mashirya bikin, ‘MACA Peace Ambassadors & Unity Affair Africa’, sun ce za a yi bikin karramawar ta taurarin lardin a ranar 30 ga Satumba, 2023 a Gidan Arewa da ke Kaduna.

A cewar su, sauran waɗanda za a karrama ɗin sun ƙunshi mutane irin su kyaftin ɗin ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, wato Ahmed Musa, da Bishop ɗin Cocin Katolika ta shiyyar Sakkwato, Matthew Kukah, da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna; Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, da Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.

Har ila yau dogon jerin sunayen waɗanda za a karrama ɗin ya ƙunshi Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli;  Gwamna Hyacinth Alia na Binuwai; ‘yar kasuwa Hajiya Laylah Ali Othman;  Rabaran Mathias  Yashim;  Prince Bala Audu, Dakta  Emmanuel Omale, da wasu.

Shugaban shirya bikin, Nyam Terry, ya yi bayanin cewa za a shirya bikin na shekara-shekara ne don a karrama mutanen da su ka ba da gudunmawa ga ci-gaban yankin Arewa.

A cewar sa, an zaɓi mutanen a tsanake ne saboda ayyukan da su ke yi babu gajiyawa wajen sadaukar da kai ga agajin jama’a, da tasirin su mai kyau kan al’umma da ƙarfafa wa matasa gwiwa, da kuma samar da zaman lafiya. 

Ya ce: “Bikin karrama gwarzayen na bana mai taken ‘Taya Gwarzayen Mu Murna’, ya na da burin karrama masana’antu, ma’aikatu, jami’an gwamnati, ‘yan wasa, ƙungiyoyi, da ɗaiɗaikun mutane waɗanda su ka taimaki al’umma ta hanyoyi daban-daban.

“Waɗannan ‘yan Nijeriya daga lardin arewa sun ba da gudunmawa, ta hanyoyi daban-daban, ga cigaban ta da samar da zaman lafiya.

“Mun yi imani da cewa wannan karramawar a ko yaushe zai ƙarfafa masu gwiwa a ko yaushe domin su ƙara himma wajen aikin da su ke wa al’umma.”

Loading

Previous Post

Shugaban MOPPAN na Katsina, Lawal Lemu, na so ‘yan fim su cure su zama ɗaya

Next Post

Harkar rubutu: Abin da ka shuka shi za ka girba, inji marubuciyar onlayin Sanah S. Matazu

Related Posts

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta
Labarai

Ƙungiyoyin harkar fim, KAFIGAN da MOPPAN, sun yi wa Rahama Sadau ta’aziyyar rasuwar mahaifin ta

June 23, 2025
Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau mutumin kirki ne da son jama’a, inji Yerima Shettima

June 22, 2025
Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau
Labarai

Yadda mahaifin mu ya rasu kwana ɗaya bayan ya dawo daga Makkah – Abba, yayan Rahama Sadau

June 22, 2025
Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji
Labarai

Mahaifin Rahama Sadau ya rasu kwana 1 bayan ya dawo daga aikin Hajji

June 22, 2025
Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano
Labarai

Masanin harshe, Korao Hamadou ya gabatar da haruffan rubutun Hausa na asali a taro a Kano

June 20, 2025
Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza
Labarai

Kotu a Kano ta tsare Tsulange, matashin da ke tare titi yana wanka da yin shigar banza

June 20, 2025
Next Post
Malama Hassana Sulaiman Isma'il (Sanah S. Matazu)

Harkar rubutu: Abin da ka shuka shi za ka girba, inji marubuciyar onlayin Sanah S. Matazu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!