FITACCEN darakta Kabiru S. Yaro (Kokobi) da waɗansu ‘yan fim har 27 sun shiga hannun wasu ‘yan sanda a garin Zariya, Jihar Kaduna, a bisa zargin wai ‘yan Shi’a ne.
Wannan al’amari ya faru a ranar Litinin, 9 ga Afrilu, 2018 da misalin ƙarfe 4 na yamma, a lokacin da ‘yan fim ɗin su ke ɗaukar wani fim.
‘Yan sandan sun yi masu dirar mikiya ne a yayin da su ke tsakiyar aiki.
Idan kun tuna, gwamnatin Jihar ta daɗe da zartar da dokar soke ƙungiyar ‘yan Shi’a mabiyan Sheikh Ibrahim Zakzaky tun bayan da sojoji su ka yi wa mabiyan kisan gilla a Zariya a cikin 2016.
Kokobi ya shaida wa mujallar Fim yadda abin ya faru, inda ya fara da cewa, “Wallahi tallahi an yi mana wulaƙanci sosai! Wallahi ban san hawa ba, ba mu san sauka ba, ba mu san fari ba, ba mu san baƙi ba.
“Abin da ya faru: mu mun je kawai shutin ne, mu na tsaye mu na shuin sai ga motar ‘yan sanda mu na tsakiyar aiki a Zariya, kawai su ka zo su ka kama mu mu 26, su ka ce mu ‘yan Shi’a ne.
“Amma a cikin mu ni kaɗai ne sananne, sai kuma ‘yan Zariya, a ‘yan Zariyan ma babu wasu sanannu, da yake fim ne mu ke yi irin TV series ɗin nan, ka san ba dole ba ne sai sanannu.
“Abin ban haushi ma, da su ka kama mu sun ga shaidar cewa ‘yan fim ne mu, don ga kyamarar mu da ‘script’ ɗin mu a hannun mu, sannan kuma sun duba sun ga sinasinan da mu ka yi, har DPO ɗin ya ke cewa waɗannan ‘yan fim ne. Amma kuma sai ya ce ba zai bada belin mu ba, gobe zai kai mu kotu.
“Fim da mu ke yi, irin ‘epic’ ɗin nan ne, su ka tara ‘yan adduna da garkuwa da mu ke amfani da su, da ya ke fim ne irin na sarautar da, su ka ɗauki waɗannan kayan hoto, wai ‘yan Shi’a, ‘yan ta’adda.
“Da safe mu na jira a zo a kai mu kotu, ba a kai mu ba sai misalin ƙarfe 6 na yamma. Kuma da ‘yan sandan su ka tashi kai mu, sai ba su kai mu da kyamarar mu da script ɗin mu ba. ‘Yan sanda su ka ce mu ‘yan ta’adda ne. Mu ka musa.
“Alƙali ya ce belin N250,000.
“Sannan kuma ‘yan sandan su ka ce mun ɓalla masu ƙarfen mota, wannan kuma aka ce N200,000. Ka ga N450,000 kenan.
“Amma abin da mu ke zargi abin da ya sa su ka yi mana haka, akwai wani ɗan sanda wai shi Mai Gidan Sama Alhaji Kabiru, ya sari wata yarinya ‘yar Zariya, Maryam, a agara, jini ya na ta zuba, aka ɗauke ta aka yi asibiti da ita.
“To, sai mu ke tunanin ko sun ji tsoron kada wani abu ya faru, shi ya sa su ka ƙulla mana wannan abin.
“Daga nan kotun sai aka ce a maida mu siteshin, washegari a dawo da mu.
“A washegarin mu na ta ƙoƙarin yin beli, bayan ni na fito don su Hajiya Fatima Lamaj, Alh. Adamu Ability, Alh. Magaji, Cashman, Sulaiman Sha’ani, Sabi’u Gidaje, Nura Ɗandolo da sauran su sun zo, su kuma sauran aka kwashe su sai gidan yari.
“Akwai wasu ‘yan mata da Jidda da Samira wai sun zagi ‘yan sanda, alhalin kuma babu wanda su ka zaga.
“Bayan mun je wurin mu na wasa da dariya da sauran su, a tunanin mu ai ba wani babban al’amari ba ne, tunda mu ga abin da mu ke yi, kuma shi ya kawo mu, har su na cewa su za su nuna mana, ba mu ‘yan fim ba. Abin da ya faru kenan.
“Amma ni babu abin da zan iya ce wa ‘yan’uwa na da su ka tsaya mana kai da fata sai Allah Ya yi masu albarka, Ya kuma saka masu da gidan Aljanna. Na yi matuƙar farin ciki da irin gudunmawar da su ka ba mu. Allah kuma Ya yi mana sakayya.
“Amma kuma ya kamata gwamnati ta shiga wannan al’amari. Ya kamata a yi mana halacci, domin aiki mu ke yi, ba yawon banza ba.”
A ɓangaren ‘yan fim na Jihar Kaduna kuwa, sun yi namijin ƙoƙari don ganin sun ceto ‘ya’uwan su daga halin da su ka shiga. Hajiya Fatima Lamaj ta yi bayanin yadda al’amarin ya kasance a wani guruf a dandalin sada zumunta na WhatsApp mai suna Harkar Film, inda ta faɗi duk wani shige da fice da su ka yi, da kuma gudunmawar da kowannen su ya bada.
Duk da cewa su Lamaj ɗin sun yi ne saboda Allah, wasu kuma sai su ka danganta abin da siyasa domin ita Lamaj ɗin ta na takarar kujerar shugabar ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Kaduna.
![]()







