Fitaccen darakta Al-Amin Ciroma ya ɓara a kan yadda rikicin siyasa ke neman ɓarkewa a tsakanin ‘yan fim na Jihar Kaduna a kan batun zaɓen ƙungiyar MOPPAN.
MOPPAN ita ce haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa a Nijeriya.
Tuni ya kamata a yi zaɓen sababbin shugabannin ƙungiyar a reshen ta na Jihar Kaduna, kuma ‘yan takara sun firfito, to amma hakan ba ta samu ba.
‘Ya’yan ƙungiyar sun kasu kashi biyu tsakanin magoya bayan ‘yan takarar zama shugaban ƙungiyar na jihar, wato Hajiya Fatima Lamaj da Muhammad Isƙil.
Rarrabuwar ta jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya bayan, waɗanda kuma sun rarraba a tsakanin wasu manyan sansanonin biyu, wato na shugaban MOPPAN na ƙasa, Abdullahi Maikano Usman, da na Al-Amin Ciroma wanda shi ne ya gwabza da Maikano a zaɓen shugaban ƙungiyar da aka yi a bara.
A yayin da Ciroma ke goyon bayan Lamaj a zaɓen, shi kuma Maikano ya na goyon bayan Izƙil ne.
Lamaj ce ake kyautata za ta ci zaɓen idan aka yi shi, to amma ‘yan kwamitin shirya zaɓen, waɗanda ake ganin cewa Izƙil su ke so ya ci zaɓen, sun ƙi yarda a yi zaɓen. A maimakon hakan, an bar ‘yan ƙungiyar su na faɗa wa juna baƙaƙen maganganu tare da ƙoƙarin ɓata wa junan su suna.
Ciroma ya ɓara ne kan wannan cacar bakin da ake yi kan batun zaɓen, musamman yadda siyasar al’amarin ta ke ta ƙazancewa.
Ya ɓara ne a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ya aika wa shugaban ƙungiyar MOPPAN na jihar, wato Malam Muhammad Adamu Bello Ability mai taken “Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Yaya Na Ability”.
A wasiƙar, Ciroma ya yi kira ga Ability da ya taimaka ya ceto masana’antar fim ta Jihar Kaduna, inda ya ce siyasar masana’antar ba ta da kyau.
Ga abin da wasiƙar ta ƙunsa:
“Salaam ran ka ya daɗe sir, ina fatan wannan wasiƙa za ta iske ka cikin ƙoshin lafiya.
“Farko tukunna, ina roƙon Allah da ya saka wa duk wanda ya taimaka wajen karɓo waɗannan bayin Allah, tun daga kan shugaba na ƙasa (na MOPPAN), har kai shugaba Alhaji Adamu Bello Ability da shugaban producers da shugaban artistes da Hajiya Fatima Lamaj da Alhaji Magaji, Gidaje, Ɗandolo da dukkan waɗanda su ka taimaka, Allah ya bar zumunci.
“Yallaɓai, a gaskiya harkar Kaduna ta na ba ni tsoro wallahi!
“Ya kamata mu farga, duk abin da ka yi sai an fassara shi da siyasa, haba jama’a!
“Shin siyasar ce ta haɗa mu da ma? Me ya sa mu ka zama haka?
“Na saurari wani faifan murya da shugaban producers ya aiko, gaskiya ban ji daɗi ba!
“Ina kira a gare ka yaya na Alhaji Ability, don Allah da son Manzon Allah (s) ka taimaka ka ceto jihar Kaduna, siyasar mu ba ta da kyau wallahi.
“Har kullum ina son gudanar da abubuwa gami da batutuwa da dama, amma tashin farko ba wanda zai kalle ka sai ta fuskar siyasa!
“Yallaɓai, mun zauna tare tsawon shekaru 15 zuwa 20, ban sani ba ko an taɓa samun wani yanayi da mu na ƙasa da ku mu ka riƙa kallon ku da wani ido na siyasa? Na tabbatar ban da girmamawa da ‘yan’uwantaka babu abin da ya wakana a tsakanin mu.
“Don haka, yallaɓai idan wannan yunƙurin siyasar zai haddasa ruɗu da rashin fahimtar juna da rarrabuwa, ni ina kira da babbar murya cewa a haƙura da ita kawai, a nemi wata hanyar, ko kuma a sake lale!”
![]()







