A farkon wannan makon ne haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya, wato MOPPAN, za ta gudanar da gagarumin taron ƙara wa juna sani kan wani tsarin kula da kiwon lafiyar masu ruwa da tsaki a cikin masana’antar ta Kannywood.
Wannan tsari na kiwon lafiya zai ba duk wanda ya yi rijista damar a riƙa duba lafiyar sa da ta iyalin sa a duk asibitin da zaɓa.
A ranar Litinin ɗin nan, 16 ga Afrilu, 2018 za a fara taron na kwana uku, a gama a ranar Laraba.
Za a yi taron ne a otal ɗin Chimcherry da ke Titin Aliyu Makama, a unguwar Barnawa, cikin garin Kaduna.
Shugaban ƙungiyar MOPPAN na ƙasa, Alhaji Abdullahi Maikano Usman, wanda shi ne ya shirya wannan taro, ya yi wa mujallar Fim ƙarin haske game da wannan taro da ya shirya.
Ya ce, “Na farko dai ranar 16 ga wata, wanda ya kama ranar Litinin kenan, da ƙarfe 4:00 na yamma za mu ƙaddamar da tarsi ne na kiwon lafiyar ɗaukacin masu harkar fim a arewacin Nijeriya.
“Saboda haka duk wanda ya ke cikin harkar fim ya na ciki, kuma zai iya cin gajiyar wannan tsari na kiwon lafiya.
“Tsari ne wanda idan mutum ya yi rijista, shi kenan zai ci gaba da zuwa asibiti da shi da iyalan sa. Amma kuma ya danganta da irin matakin da ka yi rijista a kan sa.
“Saboda haka na ƙirƙiro da wannan shiri ne a ƙarƙashin ƙungiyar MOPPAN. Saboda ganin yadda wasu daga cikin mu su kan shiga cikin halin ha’ula’i, idan Allah Ya jarabce su da rashin lafiya, sai a koma ana ta faman yaya za a yi.
“Shi ya sa a ƙarƙashin shugabanci na na ga ya dace, kuma Allah Ya yi mani jagora, Ya taimake ni, domin Allah ne, ba ni ba ne. Kuma yanzu haka ‘service providers’ ɗin ma sun riga sun iso Kaduna tun ranar Juma’a.
“Kafin zuwan nasu, sun zo da tsarin N20,000, N30,000 da N40,000, amma a cikin daren na yi mitin da su, kuma za a yi mamakin yadda Allah Ya jagorance mu, kuma ya taimaka ya ba ni fiƙira da basira, har na yi masu magana su ka rage kuɗin ba ƙaramin ragewa ba. Kuma mu ka fito da tsari na biya, ta yadda ba za a sha wahala wurin biya ba. Saboda na san yadda rayuwar ta ke.
“In Allah Ya yarda a ranar Litinin zan sanar da wannan sabon kuɗin da za a biya. Wannan shi ne abin da zai faru ranar Litinin da yamma ƙarfe 4:00.
“Sai kuma ranar Talata, 17 ga wata, za a fara gudanar da ‘seminer’. Maƙasudin shirya wannan taro na ƙara wa juna sani shi ne ‘Film Making: Opportunities and Challenges in Nigeria’.
“In Allah Ya yarda finafinan mu za su ƙara inganta. Kuma za a ƙara faɗakar da masu harkar fim gaba ɗaya.
“In Allah Ya yarda akwai ƙasida da Bank of Industry za su gabatar. Na yi magana da su a kan dukkan dabarun accessing kuɗi domin mu shirya finafinai, wanda a da ‘yan Kudanci ne kaɗai su ke cin moriyar wannan abu.
“Saboda haka na kira su na faɗa masu mu ma nan ‘yan fim ne, saboda haka su zo su faɗa mana tsarin gaba ɗayan sa, mutane su zama sun ilimantu ta yadda su ma za su iya accessing waɗannan kuɗi domin shirya finafinai.
“Sannan akwai lead paper, wanda sunan ta ‘Fundamentals of Film Making’. Ita kuma za ta ƙara fito da dabaru ne da fasaha na shirya fim, wanda darakta zai ci ribar ta, furodusa zai ci ribar ta, ɗan wasa zai ci ribar ta da duk wani mai ruwa da tsaki a cikin harkar zai ci ribar ta.
“A dunƙule abin da zai faru kenan tsakanin Litinin, Talata da Laraba in Allah mai kowa mai komai Ya kai mu.”
![]()







