• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Thursday, July 3, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Mawaƙiyar bege kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Farida Jalal, ta yi aure na 3 a asirce a Katsina 

Zan ci gaba da waƙoƙin yabon Manzo, inji ta

by DAGA EL-ZAHRADDEEN UMAR a Katsina
January 20, 2024
in Ranar Murna
0
Mawaƙiyar bege kuma tsohuwar jarumar Kannywood, Farida Jalal, ta yi aure na 3 a asirce a Katsina 

Sayyada Farida Jalal

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN ɗaura auren tsohuwar jarumar Kannywood kuma mawaƙiyar bege, Sayyada Farida Jalal, tare da mawaƙin yabo Shariff Ibrahim Gombe jiya Juma’a a garin Katsina..

Shaidun gani da ido sun bayyana wa mujallar Fim cewa Babban Limamin Masallacin Juma’a na Katsina, Liman Malam Ɗayyabu Ratibi, shi ne ya ɗaura auren a kan sadaki N100,000.

Da ta ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani game da wannan aure nata wanda kuma shi ne na uku, Farida Jalal ta ce auren kawai aka ɗaura a Katsina amma daga baya za a yi shagalin bikin a Kano.

Ta ci gaba da cewa mijin nata shi ma sha’iri ne saboda haka mawaƙiya ta auri mawaƙi kuma duk na yabon Ma’aiki SAW.

Ta ce: “Mun haɗu da wannan mijin nawa a Kano sakamakon waƙoƙin yabo da mu ke yi tare. Kuma zan ci gaba da yin waƙoƙi na kamar yadda na saba yi bisa amincewar miji na.”

Haka kuma tsohuwar jarumar ta ce ita kaɗai ce a gidan mijin nata, saboda haka za ta sakata ta wala.

Ta ƙara da cewa insha-Allah wannan aure mutu ka raba ne, takalmin kaza.

Wannan aure dai an yi shi ne ba tare da gayyatar ‘yan fim na Kano ko na Katsina ba, sai dai Farida ta faɗa wa mujallar Fim cewa za a yi gayya idan an fitar da lokacin da za a yi shagalin bikin a garin Kano.

Allah ya ba su zaman lafiya, amin.

Loading

Tags: ɗaurin aureFarida JalalKatsinaLiman Malam Ɗayyabu RatibiShariff Ibrahim Gombe
Previous Post

‘Yar jarumin Kannywood, marigayi Aminu Mai Chemist za ta yi aure gobe

Next Post

Furodusa Mukhtari Isah PRP zai aurar da ‘yar sa Sumayya

Related Posts

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida
Ranar Murna

Al-Ameen, Haidar na shirin Daɗin Kowa, ya zama angon Walida

June 29, 2025
Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani
Ranar Murna

Haihuwa ta 14: Mawaƙi Abubakar Yarima ya samu Muhammad Sani

June 19, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Next Post
Furodusa Mukhtari Isah PRP zai aurar da ‘yar sa Sumayya

Furodusa Mukhtari Isah PRP zai aurar da 'yar sa Sumayya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!