ƘUNGIYAR masu shirya finafinai ta Jihar Katsina (Filmmakers Association) sun gudanar da taron addu’o’i domin neman rahamar Allah ga marigayiya Saratu Giɗaɗo (Daso), wadda ta rasu a ranar Talata.
Shugaban ƙungiyar, Malam Aminu Mannir K’eza, ya shaida wa mujallar Fim cewa sun shirya taron ne a ranar Sallah domin su roƙi Allah ya jiƙan jarumar.
Ya ce rasuwar Daso ta zo masu da wani irin tashin hankali duba da irin kyakkyawar mu’amalar da su ke da ita da marigayiyar, wadda ya ce za a daɗe ba su manta da ita ba.
Haka kuma Mannir ya bayyana cewa sun shirya wannan taro ne a ranar Sallah domin sun yi tawassili da ayyukan watan Ramadan da niyyar Allah ya jiƙan Hajiya Saratu.
Darakta Usman UNM da Aminu Mannir K’eza ne su ka jagoranci sauran ‘yan fim na Katsina wajen yin addu’o’in.

A taron dai an karanta sunayen Allah tsarkaka 99 tare da karanta wasu surori daga Alƙur’ani mai girma da sauran addu’o’i.
Da yake bayyana irin yadda su ka sami lamarin rasuwar jarumar, Usman UNM ya ce hakika an yi samu babban giɓi wanda za a daɗe ba a cike shi ba.
Taron ya samu halartar da dama daga cikin ‘yan fim da mawaƙa na Katsina da su ka haɗa da Aliyu Show, Usman UNM, Aminu Daggash, Lawal Ibrahim Bawan Mata, da sauran su.
Haka kuma ƙungiyar ta shirya za ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Daso a Kano.