FATIMA Aliyu, wadda aka fi sani da Fatima Mai Zogale, za ta yi aure a ranar Juma’a mai zuwa.
Fatima, wadda ta samu ɗimbin fice da kuma farin jini a soshiyal midiya a faɗin ƙasar da sauran duniyar Hausawa sakamakon waƙar da Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) ya yi mata kwanan nan, ta tabbatar da hakan ga wakilin mujallar Fim a yau a Abuja.
Za ta auri wani mazaunin Kano ne mai suna Kabiru.
Ta ce sun jima suna soyayya, tun ma kafin Rarara ya yi mata waƙa.
Sai dai kuma ba sojan nan ba ne wanda a da za ta aura saboda shi sun samu matsala da shi.
Haka kuma ba uban ‘ya’yan ta biyu za ta koma mawa ba.
Za a ɗaura auren Fatima da sahibin nata a gidan su amaryar da ke Mararraba, unguwar da ke bayan garin Abuja, hanyar Keffi.
Wakilin mu ya samu labarin cewa a Abuja Fatima za ta tare, domin shi mijin nata ya na yawan shigowa garin saboda harkokin sa.
Haka kuma Rarara ya cika alƙawarin tallafa mata, har ma ya kama mata wajen da za ta yi sana’ar ta ta sayar da zogale. Amma za ta haɗa da sayar da wasu abubuwan na ci irin waɗanda mutane ke buƙata.
“Wurin yana nan a Central Area,” inji wata majiya ta kusa da mawaƙin.
A yanzu Rarara ya kasance kamar babban yaya kuma mashawarci a wajen matashiyar matar, domin hatta maganar auren akwai hannun sa dumu-dumu a ciki.
Mai ba mu labarin ya ce bayan an gama tarewar ne Rarara zai jagoranci ɗan ƙwarya-ƙwaryan taron buɗe shagon sayar da abinci na Fatima Mai Zogale.
Mujallar Fim ta gano cewa hanyoyin alheri da dama sun buɗe ga Fatima, a dalilin waƙar da aka yi mata mai taken ‘Fatima Mai Zogale’.
“Ga shi kuma za ta auri miji mai fahimta, wanda ke son ta kuma ta na son shi,” inji majiyar.