HUKUMAR Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB) ta haramta shirya finafinan da ke nuna yadda ake kuɗin tsibbu, kisan kai, shan taba, shaye-shaye da wasu miyagun laifuffuka.
Shugaban hukumar, Dakta Shaibu Husseini, shi ne ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki da hukumar wanda aka yi a Inugu a yau Laraba.
Shugaban ya ce, “A wannan lokaci akwai buƙatar ƙara samun goyon bayan kowane ɓangare na al’umma domin cigaban masana’antun finafinai.”
Ya yi kira ga ƙungiyoyin jarumai, daraktoci da furodusoshi da su ba hukumar haɗin kai wajen tabbatar da dokar.
Taron, wanda NFVCB ta shirya taron ne da haɗin gwiwar wata cibiya mai suna Corporate Accountability and Public Participation Africa (CAPPA), ya samu halartar furodusoshi, daraktoci, jarumai, da shugabannin ƙungiyoyin harkar fim daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Husseini ya nanata buƙatar da ke akwai ta iyaye da masu kula da ‘ya’ya da sauran masu ruwa da tsaki da su ɗauki tsauraran matakai don magance matsalolin da ke addabar industiri a yau.
Husseini ya ce: “Lokacin da wanda ya gabace ni a wannan muƙami ya tattauna da tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed, kan buƙatar a hana nuno shan taba a finafinan Nijeriya, sai ya kasance ƙarara cewa su ma tsibbace-tsibbace da kuɗi ya kamata a duba su.
“A yanzu wannan dokar ta haɗa da kisa na tsafi, da kuma yawan nuna sauran laifuffuka domin a ƙara tsaftace masana’antar fim.”
Ya bayyana cewa Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa, ta amince da sabon umurnin a ƙarƙashin sashe na 65 na Dokar NFVCB ta 2004.
Sabon umurnin, mai taken “Haramcin Hana Tsibbun Kuɗi, Kisan Tsafi, Taba, Kayan Taba, Tallata Abu Mai Sinadarin Nikotin, Da Nuna Ayyukan Assha a Matsayin Burgewa Cikin Finafinai, Waƙoƙi, Da Guntayen Bidiyoyi, 2024 (“Prohibition of Money Ritual, Ritual Killing, Tobacco, Tobacco Products, Nicotine Product Promotion and Glamorisation Display in Movies, Musical Videos and Skits” Regulations 2024), an miƙa shi ga Ma’aikatar Shari’a domin wallafa shi a kundin doka.
Husseini ya ce manufar shirin na wayar da kai ita ce a ilimantar da masu ruwa da tsaki game da illar nuna shan taba a cikin finafinan Nijeriya.
Ya ce ban da haɗurra da ke akwai ga lafiyar mutum, nuna shan taba ya na shafar rayuwar matasa da ƙananan yara ta hanyar da ba ta dace ba, waɗanda kuma su ne masu kallon finafinan.
Ya ce, “NFVCB ta na nan ta na tsara manyan shirye-shirye na wayar da kai a makarantun sakandare, manyan makarantu, unguwanni, ƙungiyoyin addini, da sauran wurare.
“Masana’antar fim ta na taka muhimmiyar rawa a ɓangaren nishaɗantarwa da ƙirƙira, don haka ya na da kyau mu ɗauki cigaban ta da muhimmanci.
“NFVCB ta na goyon bayan shirya finafinai da babu shan taba a cikin su, kuma ta na so a yi haɗin gwiwa wajen shirya abin kallo wanda ya hana shan taba kuma ya na isar da saƙonnin samar da lafiya mai nagarta.”
Bayan tattaunawa mai zurfi, sai NFVCB, da haɗin gwiwar CAPPA, ta samar da ‘ƙananan dokoki’ a kan shan taba a finafinai, wanda wani abu ne da dokokin yanzu ba su fito ɓaro-ɓaro su ka yi hani a kan sa ba.
NFVCB ta ce ta ƙudiri aniyar tabbatar da wannan tsarin kuma har ma ta fara aiwatar da sababbin dabaru don gudanar da aikin da aka ɗora mata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa aikin hukumar ne ta yi wa dukkan wuraren sayar da ko nuna fim rajista a faɗin ƙasar nan, sannan ya kasance ta na da sunayen su a rubuce a ko yaushe, da dai sauran ayyukan ta.
Idan ba ku manta ba, mujallar Fim ta ba ku labari kwanan nan yadda ita ma Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya finafinan da ke nuna harkar daba da daudu.