SHUGABAN Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa (NFVCB), Dakta Shaibu Husseini, ya musanta rahotannin da aka yaɗa cewa ya ce Gwamnatin Tarayya ta haramta nuno yadda ake kuɗin tsafi da kuma shan taba a finafinan Nijeriya.
Idan kun tuna, yawancin kafafen yaɗa labarai, ciki har da mujallar Fim, a jiya sun ruwaito cewa shugaban hukumar ya bayyana wannan haramcin a wani taron masu ruwa da tsaki na ƙasa kan daina saka shan taba a finafinan Nijeriya wanda aka yi a Inugu.
Hukumar NFVCB ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar cibiyar Accountability and Public Participation Africa (CAPPA).
Furodusoshin finafinai da daraktoci da ’yan fim da aka zaɓo daga sassa daban-daban na ƙasar nan, da kuma shugabannin ƙungiyoyi daban-daban na masana’antar finafinan Nijeriya sun halarci taron.
Sai dai kuma a sanarwar da ya fitar a yau Alhamis, Husseini ya ce, “Ban ba da sanarwar hana shan taba ba, ko nuno taba ba, da kuma al’amuran tsafi a cikin finafinai (a taron yankin Kudu-maso-Gabas) na masu ruwa da tsaki su na shiga cikin ingantaccen allo da kuma kamfen a kan a samu smoke-free Nollywood wanda aka gudanar a Inugu tare da haɗin gwiwar CAPPAfrica. A’a, ban ce ba.
“Ko kaɗan BAN ba da sanarwar hana nuno ‘shan taba da nuno tsafi a finafinai’ ba a taron masu ruwa da tsaki (na yankin Kudu-maso gabas) domin tattaunawa kan kyautata kiwon lafiya a finafinai tare da yekuwar daina nuno shan taba a Nollywood, wanda aka yi a Inugu tare da haɗin gwiwar @CAPPAfrica. A’a, BAN ce haka.
“Abin da na a ambata a cikin jawabin da na yi wanda na raba shi a nan shi ne akwai doka (wato Dokokin NFVCB na 2024) da su ka ce kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya an hana TALLATA ko ALKINTA tsafin kuɗi, kisan tsafi, tsafin kuɗi, taba, kayan taba, kayan sinadarin nicotine a finafinai, bidiyoyin rawa da waƙa, da guntayen bidiyon wasan barkwanci.
“Manufar dokar ita ce ta nuna rashin dacewar yawan nuno ko kwaɗaita ko tallata taba ko kayan nicotine a cikin finafinai, bidiyon rawa da waƙa, da guntayen bidiyon wasan barkwanci.
“Dokar na so a riƙa nuno gargaɗin kare lafiya a duk inda ya kama lallai sai an nuno shan taba cikin fim wataƙila saboda tabbatar da wani tarihi, ko don dalilan ilimintarwa, kuma a nuno rayuwa maras kyau a finafinai, bidiyoyin rawa da waƙa, da guntayen bidiyoyin wasannin barkwanci.
“Za a nuno gargaɗin kare lafiyar ne a farko da kuma ƙarshen aikin, wato fim ɗin.”
Ya ba da tabbacin cewa hukumar ta NFVCB ba za ta aiwatar da duk wani shiri da zai dakushe basirar ƙirƙira ba.
Ya ƙara da cewa, “Duk wani fim, guntun bidiyon wasan barkwanci, ko bidiyon rawa da waƙa da ya nuno taba ko kaya masu nicotine, haja, ko ya kama tilas a nuno abin domin a fi gane labarin za a saka shi a wani aji na musamman da ya dace, wato classification (ko rating) Kuma ba za a nuna shi ga mutane ‘yan ƙasa da shekaru 18 ba.”