• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, August 26, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Maimunatu, tsohuwar matar mawaƙi Ado Gwanja, ta yi aure na 3

by ALI KANO
May 25, 2024
in Ranar Murna
0
Maimunatu, tsohuwar matar mawaƙi Ado Gwanja, ta yi aure na 3

Maimunatu Ɗan'auta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MAIMUNATU Kabir Ɗan’auta, tsohuwar matar shahararren mawaƙi kuma jarumin barkwanci a Kannywood, Ado Isah Gwanja, ta yi aure a karo na uku jiya Juma’a.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta tabbatar wa da mujallar Fim labarin auren, wanda aka ɗaura a asirce a Kano a daidai lokacin da hankalin jama’a ya raja’a kan tataɓurzar da ake yi kan sarautar Sarkin Kano.

Majiyar ba ta faɗa mana sunan angon ba domin Maimunatu ta ce ba za ta bayyana shi ba har sai lokacin da za ta yi bikin tarewa. Maimunatu na kiran kan ta da “Mrs. A” a cikin ‘yan kwanakin nan a soshiyal midiya.

Wato kenan an ɗaura auren babu tarewa sai nan da wani lokaci.

Mai ba mu labarin ya ce: “Maimuna ta burge ni domin ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta kuma yin aure.”

Ita dai Maimunatu, auren ta da Gwanja ya mutu da saki uku ne a cikin 2021.

Sun haifi ‘ya guda ɗaya mai suna Asiya (Balaraba), wadda aka haifa a ranar Asabar, 17 ga Agusta, 2019.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa wannan auren da aka ɗaura jiya shi ne na uku da Maimunatu ta yi, domin kuwa ta taɓa yin auren kisan wuta a Abuja bayan rabuwar su da Gwanja.

Ta yi matuƙar son ta koma wa uban ‘yar ta, wato Ado Gwanja, shi kuma sai ya ƙi. An ce ya faɗa wa wasu makusantan sa cewa shi da Maimunatu ba za su taɓa komawa aure ba.

Don haka ne ma aka ɗaura masa aure da matar sa ta yanzu, wato Maryam Zubair Muhammad Paki, a ranar 21 ga Yuli, 2023 a Kano.

“Ganin ba zai maida ta ba ne ya saka Maimunatu ta yanke shawarar bari dai ta kama dahir,” a cewar majiyar mujallar Fim.

Maimunatu dai ta yi fice da sunan @munat_danautah a soshiyal midiya inda a kai a kai ta kan wallafa hotuna da bidiyoyin ta masu bayyana kyakkyawar surar ta.

Loading

Tags: Ado Isah Gwanjaaureɗaurin aureMaimunatu Ɗan'auta
Previous Post

Ban ce an hana nuno shan taba da kuɗin tsafi a finafinai ba, inji shugaban tace finafinai na ƙasa

Next Post

Rasuwar tsohuwar jaruma Fati Slow a ƙasar Chadi ta girgiza Kannywood

Related Posts

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji
Ranar Murna

Mawaƙi Abdool-Gaya ya samu ƙaruwar ɗa namiji

August 24, 2026
An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki
Ranar Murna

An ɗaura auren mawaƙi Kawu Ɗan Sarki

August 23, 2026
Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51
Ranar Murna

Yadda marubuciya Aunty Baby ta yi bikin cikar shekara 51

August 19, 2026
Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira
Ranar Murna

Uwargida na ce ta biya sadakin aure na da amarya ta – darakta Aminu Saira

August 2, 2026
Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a
Ranar Murna

Bikin auren darakta Aminu Saira a Azare ya ja hankalin jama’a

July 31, 2026
An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Next Post
Rasuwar tsohuwar jaruma Fati Slow a ƙasar Chadi ta girgiza Kannywood

Rasuwar tsohuwar jaruma Fati Slow a ƙasar Chadi ta girgiza Kannywood

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!