• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

El-Mustapha ya faɗi sirrin zaman auren sa da Fatima na tsawon shekara 14

by ABBA MUHAMMAD
June 13, 2024
in Ranar Murna
0
El-Mustapha ya faɗi sirrin zaman auren sa da Fatima na tsawon shekara 14

Abba da Fatima: Sai godiya

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BABBAN Sakataren Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa haƙuri da fahimtar juna su ne sirrin zaman auren su da matar sa, Hajiya Fatima Mohammed Shuwa.

Abba, wanda fitaccen jarumin Kannywood ne, ya auro Fatima ne daga Maiduguri, Jihar Borno, inda aka ɗaura auren a ranar 12 ga Yuni, 2010, don haka a jiya su ka cika shekara 14 cur a matsayin miji da mata.

A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da Babban Sakataren kan cikar su shekara 14 da aure jiya, El-Mustapha ya fara da sallama, inda ya ce, “Assalamu Alaikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu. Wannan rana ta 12 ga watan June, shekara ta 2024, wadda ta zo daidai da shekara 14 da yin aure na ko in ce ni da mata ta Fatima, ta zamo rana wanda da ma duk shekara mu na ‘celebrating’ ɗin wannan rana idan ta zagayo, mu na yi wa Allah godiya da ya bar mana rayuwar mu cikin lafiya, cikin fahimtar juna, cikin soyayya, sannan kuma cikin biyayya da ƙaunar juna.

“Haka kuma rana ce ta farin ciki, kuma rana ce ta tarihi a Nijeriya, rana ce da aka ta’allaƙa ta da Ranar Dimokiraɗiyya, wanda da ma tun a da a ranar aure na ma na ce ranar M.K.O. Abiola.

“Sannan kuma ga shi ranar auren Abba El-Mustapha da Fatima M. Shuwa. Rana ce ta farin ciki.

“Allah mun gode, Allah mun gode. Ka ci gaba da maimaita mana irin waɗannan ranaku, wanda za mu duba mu yi nazarin abin da su ka faru a baya mu kuma gode wa Allah kan haƙuri, juriya, sadaukarwar da mu ka rinƙa yi tare, wanda har mu ka kai yanzu.”

Da wakilin mu ya tambaye shi sirrin zaman auren su da su ka kai har tsawon waɗannan shekarun, sai ya amsa da cewa, “Wato duk inda aka ce bawa zai yi aure, to ya na da kyau duk wacce za ka aura ku yi ƙoƙari ku fahimci juna. Ban da soyayyar, ‘at least’ a fahimci juna sosai, idan ku ka fahimci juna sosai da ita, tabbas zamantakewar ku za ta yi daɗi.

“Kowa ya gane irin abin da wannan ba ya so. Kai miji ka gane abin da matar ba ta so, ita matar ta san abin da ba ka so, abin da ka ke so, abin da ke yawan sa ka fushi, abin da ke sa ka farin ciki, abin da ke yi maka daɗi, wane irin abinci ka fi so, da duk dai abubuwa waɗanda za su ƙara danƙon ƙauna, danƙon zumunci a tsakanin ku biyu.

“Ya zamo cewa kun fifita haƙuri a kan komai. Duk abin da ya zo a yi haƙuri da shi, in a cikin samu ne a yi haƙuri, in a cikin rashi ne a yi haƙuri.

“Sannan kuma ku mutunta juna, ku yi ‘respecting’ juna. Kada wani abu na cin mutunci ya shiga tsakanin ku har ya fara wanzuwa. Tsakanin ku ya zamo cewa kowane lokaci ku na girmama juna, ku na yin abin da ya dace, domin ganin cewa dangantakar ku ya ƙara ƙarfi, ya ƙara ƙarfafa zumuncin ku da kuma soyayyar ku ta na ƙara ƙarfi a kullum. Ya zamo cewa duk abin da ta yi mara kyau za ka faɗa mata gaskiya, ita ma idan ta gano za ta faɗa maka cikin nasiha, kai ma cikin nasiha, cikin ƙauna dai faran-faran, wanda harshe da haƙori ana samun saɓani, to amma in aka samu irin wannan saɓanin sai a koma gefe a ga menene ya faru, ta yaya za a gyara.

“Shi ‘mistake’ ana so ya faru saboda a gane ya matsalar take, ya za a yi a gyara. Sannan kuma idan aka gyara, sai a kiyaye duk abin da aka yi har aka samu wannan ‘mistake’ ɗin.”

El-Mustapha ya ba da shawara ga sauran ma’aurata, ya ce, “Shawara ga ma’aurata na faɗa a baya: haƙuri. Ya zamo cewa kuma kun fahimci juna, ku fahimci juna sosai kafin aure. Ta gane abin da ke sa ka farin ciki, abin da ka fi so a zamantakewa, yaya ka ke, me ke ɓata maka rai, irin dai ku fahimci juna dai sosai da sosai. Ku zama kamar ‘yan’uwa, ku zama aminai wanda ba su rabuwa, da sauran su.

“Sannan kuma mutum ya riƙe gaskiya. Haƙuri shi ne babban jigo, a yi haƙuri da juna, a yi haƙuri da juna. Zaman ibada zama ne na haƙuri, a fara samun zuri’a, a haɗa kai gaba ɗaya a taru wajen yin tarbiyya.”

Yabanya ta yi kyau: Abba El-Mustapha da iyalin sa

El-Mustapha sun haifi ‘ya’yan uku, wato A’isha, wadda ake yi wa laƙabi da Lateefa, sai Muhammad, wanda ake yi wa laƙabi da Janaral, sannan kuma su na da Bilkisu, wadda ake yi wa laƙabi da Malika.

Ya yi wa ‘ya’yan nasa addu’a da cewa: “Allah ya albarkace su, Ubangiji ya sa mahaddata Alƙur’ani ne, Allah ya sa su yi wa addinin Musulunci hidima, Allah ya sa su yi wa al’ummar Musulmi na duniya baki ɗaya hidima, Allah ya sa mu dace. Sai godiya.”

Loading

Tags: Abba El-MustaphaaureFatima Mohammed ShuwaWedding Anniversary
Previous Post

Gwamnati na so NLC ta amince da albashin da ba zai gurgunta tattalin arziki ba kuma ya jawo rage ma’aikata

Next Post

Bikin Sallah: Tinubu ya taya murna tare da yin kira a yi tunani kan sadaukarwa, alhaki da kuma haɗin kai

Related Posts

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5
Ranar Murna

An taya Aisar, jikar marubuciya Sadiya Garba Yakasai, murnar cika shekaru 5

July 15, 2026
Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Ranar Murna

Jarumin Kannywood Tijjani Faraga ya aurar da ‘yar sa ta biyu

July 12, 2026
Mawaƙi Sa’eed Ja’afar ya samu ƙaruwa da ‘ya mace
Ranar Murna

Mawaƙi Sa’eed Ja’afar ya samu ƙaruwa da ‘ya mace

July 6, 2026
Furodusa Alhaji Sheshe da Khairiyyah sun zama ɗaya
Ranar Murna

Furodusa Alhaji Sheshe da Khairiyyah sun zama ɗaya

July 4, 2026
Abokai sun shirya yin walima don taya jarumin Kannywood AS Bello murnar zama Farfesa
Ranar Murna

Abokai sun shirya yin walima don taya jarumin Kannywood AS Bello murnar zama Farfesa

July 2, 2026
Furodusan Kannywood Alhaji Sheshe zai angwance ranar Asabar
Ranar Murna

Furodusan Kannywood Alhaji Sheshe zai angwance ranar Asabar

June 29, 2026
Next Post
Bikin Sallah: Tinubu ya taya murna tare da yin kira a yi tunani kan sadaukarwa, alhaki da kuma haɗin kai

Bikin Sallah: Tinubu ya taya murna tare da yin kira a yi tunani kan sadaukarwa, alhaki da kuma haɗin kai

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!