• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, June 6, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Yadda na ji da aka naɗa ni Sarkin Mawallafa – Ado Gidan Dabino

by MUKHTAR YAKUBU
October 23, 2024
in Labarai
0
Yadda na ji da aka naɗa ni Sarkin Mawallafa – Ado Gidan Dabino

Ado Ahmad Gidan Dabino, M O N, bayan an naɗa shi a matsayin Sarkin Mawallafa

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHAHARARREN marubuci kuma jarumin Kannywood, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana jin daɗi dangane da naɗa shi Sarkin Mawallafa da wata ƙungiyar matasa da cigaban mata ta yi kwanan nan.

An yi naɗin ne a ranar 20 ga Oktoba, 2024 a lokacin wani gagarumin taro da aka gudanar a wajen shaƙatawa na dajin Yankari da ke cikin Jihar Bauchi.

A lokacin da yake bayyana wa mujallar Fim yadda taron ya gudana, Gidan Dabino ya ce, “To, shi wannan taro na naɗin kamar yadda aka gani, ya gudana ne a dajin Yankari da ke cikin Jihar Bauchi inda Mataimakin Gwamnan Bauchi ya zo a matsayin gwamna, sai kuma Ministan Wasanni Da Al’adu shi ma ya zo, da sauran mutane masu yawa.

“Kuma ba ni kaɗai aka yi wa naɗin ba, don akwai sauran mutane mata da maza da ƙungiyar ta naɗa a wasu muƙamai don girmama su bisa ƙwarewar su a wani fanni na rayuwa.

“Kuma ni gaskiya a nawa ɓangare su masu ƙungiyar ban san su ba. Kamar dai yadda ake ba ni wata shaida ta girmamawa a baya haka aka yi mini, don kusan duk wata karramawa da aka yi mini su masu yi suna cewa sun duba cancantar da na yi ne suka ba ni, ba don na san su ba, to su ma waɗannan haka suka kawo mini takarda.”

Ya ƙara da cewa, “Kuma da aka je naɗi, kamar yadda ake yi, za a zaunar da ku a naɗa muku rawani a saka muku alkyabba, to duk sun yi irin wannan. Kuma bayan an gama mun tashi mun je mun gaishe da Mataimakin Gwamna da Minista, a matsayin mun kawo gaisuwa kenan.”

Dangane da ko zai kasance yana da fada a matsayin sa na Sarki kuwa, cewa ya yi: “To, ita wannan sarautar ba za ta zama ina da masarauta ba, zan kasance dai a matsayin Sarkin Mawallafa ne. Don ka ga akwai sarautu da muke da su a ƙasar Hausa da masu sarautar ba su da fada, kamar Sarkin Fawa, Sarkin Maharba, Sarkin Wanzamai, da dai sauran su. Don haka sarauta ce ta harkar mawallafa, kuma ita za mu gudanar ba sai da wata masarauta ba.

“Kuma a matsayi na na marubucin da na yi shekaru arba’in ina cikin harkar wallafa, har kuma wata ƙungiya ta hango na bayar da gudunmawa, to ka ga wannan abin zai ƙara maka ƙarfin gwiwa kuma zan ji daɗi, saboda an kula da abubuwan da na ke yi wa adabin da kuma irin gudunmawar da na bayar. Don haka na ji daɗi sosai da na ga duk abubuwan da nake yi za a gani wata rana kamar yadda aka ba ni kambun girmamawa na ƙasa a lokacin Jonathan.

“Kuma gaskiya abin da ya fi burge ni shi ne yadda wasu daman a baya su kan kira ni da irin wannan sunan, suna cewa Katibi, wasu su ce Sarkin Marubuta, wasu su ce Sarkin Mawallafa, da sauran su.

“Don na san akwai wani taro da aka yi a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua na ɗaliban Sashen Hausa, wanda har wasiƙa sun turo mini da wannan irin naɗin sarauta da za a yi na adabin Hausa, amma dai sai ya zama taron bai yiwu ba. To ka ga hakan bai samu tabbata ba sai a wannan lokacin da ita wannan ƙungiyar ta shirya taron naɗin aka zo kuma aka tabbatar da naɗin.

“Kuma abin da nake so mutane su sani, ita wannan sarautar ta dukkan marubuta da mawallafa ce, don haka ba ni kaɗai aka bai wa ba, tamu ce gaba ɗaya. Don haka ina roƙon Allah ya sa wannan naɗin da aka yi ya zama alheri a gare ni da kuma su marubuta da kuma rubutun gaba ɗaya.”

Loading

Tags: Adabin HausaAdo Ahmad Gidan DabinomarubutasarautaSarkin Mawallafa
Previous Post

Jarumin barkwanci a Kannywood, Gidigo ya yi rashin mahaifi

Next Post

Tsohuwar jaruma a Kannywood, Zulai Illah, ta riga mu gidan gaskiya

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Tsohuwar jaruma a Kannywood, Zulai Illah, ta riga mu gidan gaskiya

Tsohuwar jaruma a Kannywood, Zulai Illah, ta riga mu gidan gaskiya

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!