GWAMNAN Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya naɗa jarumi kuma mawaƙi a Kannywood, Alhaji Sani Musa Danja, a matsayin mai ba da shawara na musamman a kan harkokin matasa da wasanni.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Lahadi, an lissafa mutane guda takwas da gwamnan ya naɗa a muƙamai daban-daban, ciki har da Sani Musa Danja.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Sani yana cikin ‘yan fim da suka daɗe suna cikin harkar siyasar rundunar Kwankwasiyya da ke mulkin jihar.
Baya ga kasancewar sa ɗan fim na farko da ya shiga harkar siyasa tun kafin kowa ya shiga.
Jama’a da dama dai suna yi wa Sani Musa Danja fatan alheri da samun wannan muƙamin.