A DAREN ranar Juma’a, 1/5/2020, Allah ya ɗauki ran mahaifiyar marubuci Khalid Imam, wato Malama Maryam Shu’aibu.
Ta rasu a Asibitin Mohammed Abdullahi Wase da ke Kano inda ta shafe tsawon kwana takwas ta na jinya.
Marigayiyar, mai shekara 72 a duniya, ta bar ‘ya’ya shida, wato Khalid, Amina, A’isha, Hafizu, Sulaiman da Abubakar wanda malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen, shi ya jagoranci yi wa marigayiyar sallah a gidan ta da ke unguwar Yakasai.

‘Yan’uwa da abokan arziki sun shaidi marigayiyar da kyawawan halaye, waɗanda su ka haɗa da sadar da zumunta.
Da fatan Allah ya jiƙan ta, ya bai wa ‘yan’uwa da abokan arziki jimirin jure wannan babban rashi.
![]()







