BURIN jaruman Kannywood, Abdul’azeez Muhammad Shareef (Abdul M. Shareef) da Maryam Muhammad Ƙaura (Maryam Malika) ya cika a yau domin kuwa an ɗaura masu aure.
An ɗaura auren Abdul da tsaleliyar sahibar tasa a yau Juma’a da misalin ƙarfe 1:15 na rana, bayan an gama sallar Juma’a a Masallacin Sani Zangon Daura da ke Unguwar Kaji, Kaduna, a bisa sadaki N200,000.


Wasu daga cikin ‘yan fim ɗin da suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, da Malam Tijjani Faraga, Malam Musa Muhammad Abdullahi, Sanusi Oscar 442, Daddy Hikima, Mustapha Nabraska, Naziru Ɗanhajiya, Nasiru Naba, Nura MC Khan, Umar Gombe, Lawal Ahmad, Waziri Garba Bado, Hannafi Rabilu Musa, Hamza Talle Maifata, Salisu S. Fulani da ƙanen ango, wato Umar M. Shareef.
Kafin ranar ɗaurin auren, an yi shagulgula da suka haɗa da wankan amarya (bridal shower), ƙwallon ƙafa da dina.
A ranar Talata da ta gabata ne aka gudanar da wankan amarya ɗin a ɗakin taro na otal ɗin Hamdala da ke Titin Muhammadu Buhari. Sai dai bikin na mata ne zalla.
A shekaranjiya aka buga wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci tsakanin abokai (friendly match), a filin wasa na otal ɗin Hamdala. ‘Yan fim da dama, musamman na Kaduna, sun halarta.
Sai kuma jiya aka gudanar da ƙasaitacciyar dina, inda ‘yan Kannywood maza da mata daga jihohin Kano, Katsina, Jos da Kaduna suka haɗu.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Abdul yana da mata ɗaya da ‘ya’ya biyar, ita kuma Maryam tana da ‘ya’ya uku a gidan tsohon mijin ta.
