• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, July 1, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

by MUKHTAR YAKUBU
June 30, 2025
in Tattaunawa
0
MOPPAN: Za mu haɗa kai da ‘yan siyasa don kawo cigaban Kannywood – Shehu Hassan Kano

Alhaji Shehu Hassan Kano

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

Bayan rasuwar zaɓaɓɓen Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Malam Maikuɗi Umar (Cashman) kwanan baya, Kwamitin Amintattu na ƙungiyar suka zaɓi Alhaji Shehu Hassan Kano a matsayin Shugaban Riƙo.

Mujallar Fim ta tattauna da Shehu a gidan sa da ke unguwar Fagge, Kano, inda ya bayyana matsayin shugabancin nasa da kuma abubuwan da ya sa a gaba.

FIM: Alhaji Shehu Hassan Kano, kai ne a yanzu aka bai wa riƙo na shugabancin ƙungiyar MOPPAN. Masu karatun mu za su so jin matsayin shugabancin naka.

SHEHU HASSAN KANO: To, a yanzu dai ni a matsayi na na shugaba, shi wannan shugabancin da nake yi ne a matsayin na riƙo kafin shugabanni su zauna nan gaba su zartar da hukunci a kan tsarin tabbatar da shugabanci mai cikakken iko, don a yanzu wani abu ne mai wahala da za a ce har an samu damar gudanar da zaɓe. Kuma da man wannan ƙungiyar a tsarin shugabancin ta akwai mataimaka da suka fito daga shiyyoyi uku: Arewa-maso-gabas, Arewa-maso-yamma, Arewa-ta-Tsakiya, wanda ya kasance ni nake a matsayin Mataimaki mai kula da Arewa-maso-yamma.

To kuma bayan rasuwar zaɓaɓɓen Shugaban ƙungiyar, sai shugabanni suka zauna suka ga ba za a ci gaba da tafiya babu shugaba ba, don haka a zaɓi wanda zai riƙe zuwa wani lokaci don a ga zaɓe za a yi ko kuma tabbatarwa za a yi. Kuma da aka zo Allah da ikon sa ni wani na zaɓa, don so na shi ne a maida wasu ‘yan Jihar Kaduna tunda Shugaban daga can ya fito. Sai kuma aka ce ni kujerar tawa za a mayar Kaduna na koma matsayin Shugaban Riƙo zuwa nan gaba. Don haka a dai wannan lokacin ina matsayin shugaba na riko, su kuma Jihar Kaduna aka ba su damar su bayar da wanda zai hau Kujerar mataimakin Shugaba na Arewa maso yamma.

FIM: Wato kenan babu wani lokaci da aka tsara na tsawon zaman ka a matsayin Shugaban Riƙo.

SHEHU HASSAN KANO: E, ba za a ce babu lokaci ba, amma dai abu ne wanda zai iya ɗaukar lokaci mai tsayi, kuma za a iya warware shi a cikin ƙaramin lokaci, don a yanzu abin da yake gaban mu shi ne mu shirya karɓar gudanar da mulki daga hannun waɗanda suka sauka, mu karɓi duk wasu takardu da ya kamata mu karɓa.

Don haka sai mun kammala wannan za a zo maganar tabbatar da shugabanci. Amma dai ba muna son abin ya ɗauki dogon lokaci ba, don ka ga zama ɗaya muka yi na shirin karɓar mulki saboda yanayin rashin lafiyar Shugaban. Amma duk da haka su Kwamitin Amintattu suka ba mu damar za mu ci gaba da yin wasu ayyuka.

Sai dai wajen da muka samu matsalar shi ne an gabatar da shi a matsayin Shugaba, don haka idan muka je wani waje sai mun tsaya wani dogon jawabi, don haka sai muka koma muna yi daidai abin da ya sauwaƙa kafin Allah ya ba shi lafiya. Sai kuma Allah ya ƙaddara cuta ba ta tashi ba ce. To wannan dai shi ne abin da ya faru .

FIM: A matsayin ka na Shugaban Riƙo, ko akwai iya hurumin da kake da shi?

SHEHU HASSAN KANO: Ai a matsayi na na shugaba babu wani hurumin da ba nawa ba. Don haka ba ni da wata iyaka don ni Shugaban Riƙo ne. Duk amana ce aka ba ni, kamar Kantoma ne a mulkin siyasa, ka ga komai yana gudanarwa.

FIM: Yanzu ina ka sa gaba a tafiyar ka ta Shugaban Riƙo?

SHEHU HASSAN KANO:To, kamar yadda ka sani, ita ƙungiyar MOPPAN ba sabuwa ba ce, ta shafe shekaru masu yawa, kuma ta yi shugabanni daban-daban, kuma kowa yana zuwa da irin nasa tunanin na yadda zai tafiyar da ƙungiyar. Kuma ana ƙoƙari na yadda za a ciyar da wannan masana’antar gaba, kowa yana da irin nasa tunanin.

To, mu a tamu tafiyar za mu yi ƙoƙari mu samar da tallafin da zai ɗago na ƙasa ya yi sama a cikin masana’antar, da mawaƙa da suka yi ƙasa, da masu shirya fim ɗin waɗanda suka zamo ƙashin bayan harkar, duk za mu yi ƙoƙari wajen samar da tallafin da za a ci gaba.

Shugabanni da aka yi a baya kowa ya yi nasa ƙoƙarin wajen bunƙasa ƙungiyar don a san ta. Wannan ƙoƙari ne ba ɗan kaɗan ba, saboda MOPPAN a yanzu tana cikin ƙungiyoyi da aka sani a ƙasar nan. Mu a wajen mu cigaba ne aka samu sosai.

Wasu shugabannin sun ƙoƙarin samar wa da ƙungiyar wani hurumi na shiga cikin ƙungiyoyi da za su rinƙa samun tallafi wanda Gwamnatin Tarayya take ware kaso na musamman ga masu harkar nishaɗantarwa. Sun yi iya ƙoƙarin su, kuma sun kai iya matsayin da suka kai.

To mu yanzu a wannan gaɓar tamu, da muka zo sai muka ce mu yi wata dabara tunda a yanzu a lokacin siyasa muke, kuma duk mutumin da yake wata harka ta sana’a ko kasuwanci a ƙasar nan, to sai ya haɗa kan sa da siyasa. Don haka a yanzu cikin wuraren da za mu rinƙa kai ƙafar mu, kuma muna miƙa hannun mu, to gaskiya ne har da wajen ‘yan siyasa domin samar da abin da masana’antar za ta ci gaba.

Ba kuma za mu yi ne don kan mu don muna son mu amfana ba, don haka za mu yi abin mu a buɗe ne ta yadda duk inda za mu je, to sai ƙungiya a matakin jiha ta sani da sauran ƙungiyoyi da suke ƙarƙashin MOPPAN, don mu samu damar tare kowa ya sani.

Don akwai damarmaki ga su nan; ana tura yara ƙasar waje suna yin karatu a kan fim, to sai ya zama karatun da ake samarwa sai ya zama ana yi musu iyaka, duk da dai ba mu raina ta ba, sai muke ganin ta yi mana kaɗan.

Amma muna da hanyar da za mu bi muke ganin harkar ta zama buɗaɗɗiya, mai faɗi wadda duk inda kake a faɗin ƙasar nan za ka samu abin zai zo garin ku wanda idan kai ba ka samu ka amfana ba, to ɗan’uwan ka zai samu ku amfana. Don haka wannan yana cikin ƙudirin da muka saka a gaba.

FIM: Da ka kawo maganar siyasa, wasu za su ce MOPPAN za ta shiga wata jam’iyyar siyasa ne?

SHEHU HASSAN KANO: Ba jam’iyya za mu shiga ba, ba kuma wani ɓangare na siyasa za mu yi ba. Ai abin da ya sa na faɗi haka, ita masana’antar finafinai ta Kannywood, akwai ‘yan siyasa, kuma ba jam’iyya ɗaya suke yi ba. Za ka ga wasu suna bin wani ɓangare, wasu suna bin ɓangare daban.

To mu a tsarin mu na MOPPAN kowa namu ne, ɗan masana’antar mu ne. Ko wanne idan ya ga akwai wani abu da za a yi harkar fim ta ci gaba, ya kawo mana shi a ƙungiyance mu shige gaba. Idan masana’antar za ta amfana, to mu a shirye muke. Don haka mu ba wani ɓangare guda za mu bi mu riƙe ba, don yin hakan akwai haɗari, don so muke in dai ɗan fim ne duk wata tafiyar da yake ta siyasa ya zama ya amfana da tafiyar ita ma masana’antar ta amfana, ko da kuwa ba jam’iyyar sa ba ce take mulki, saboda shi ɗan ƙungiya ne, ya amfana da abin da aka samu. Don haka za mu haɗu ne a matsayin ‘yan fim mu amfana da junan mu a wajen tafiyar siyasa. Kowa kuma ya tsaya a jam’iyyar siyasar da yake, idan an zo maganar harkar fim da yadda za a ciyar da masana’antar gaba, sai mu haɗu a nan. Idan aka je aka samo a zo a yi yadda kowa zai amfana. Illa iyaka mu kiran da muke yi kowace jiha ‘yan ƙungiya su buɗe ido su kai ƙafar su ga gwamnatin da take mulki a jihar, kuma kowacce jam’iyya take gwamnati a jihar don su shiga su nemo abin da ƙungiyar za ta amfana da shi. Wannan shi ne ƙudirin mu, kuma a kan haka za mu tafi. Muna fatan Allah ya yi mana Jagora.

FIM: To, madalla. Mun gode.

SHEHU HASSAN KANO: Ni ma na gode sosai.

Loading

Tags: MOPPANShehu Hassan Kano
Previous Post

Tawagar Gwamnatin Tarayya ta miƙa saƙon ta’aziyya daga Tinubu tare da yin addu’o’i a gidan Ɗantata a Madina

Related Posts

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 
Tattaunawa

Ba faɗuwar zaɓen MOPPAN ta sa muka kafa ƙungiyar NEKAGA ba, inji Ability 

March 1, 2025
Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah
Tattaunawa

Za mu kawo sauyi ga matan Kannywood da tallafin NITDA, inji Mansurah Isah

November 13, 2024
Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala
Tattaunawa

Bikin auren ‘ya’ya na ya ɗaga daraja ta – Aminu Ala

August 2, 2024
Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde
Tattaunawa

Buri na in samar wa MOPPAN tsarin shugabancin da za a riƙa tunawa da ni – Habibu Barde

March 13, 2024
Mahaifiyar Afakallahu ta kwanta dama
Tattaunawa

Afakallahu: Abin da mahaifiyar mu ta karantar da mu

March 11, 2024
Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV
Tattaunawa

Gaskiyar abin da ya faru gare ni a haɗarin da na yi – Jarumar Kannywood Maryam CTV

February 14, 2024
  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!