FITACCEN lauya a Kano, Abba Hikima Fagge, ya shaida wa Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano cewa ba ta da hurumin gayyatar mawaƙa ko tuhumar su da aikata laifi wajen shirya muƙabala.
Hikima ya yi wannan bayanin ne a Facebook a yau bayan ya raka mawaƙin yabo Shehi Mai Tajul Izzi zuwa hukumar don amsa gayyatar da ta yi masa kan zargin sun shirya muƙabala tsakanin sa da Malam Usman Mai Dubun Isa ba bisa ƙa’ida ko neman izinin ta ba.
Mujallar Fim ta ba ku labari jiya cewa an yi muƙabalar ne a Kano a ranar Lahadi da ta gabata.
A wani saƙo da ya saki a Facebook, lauyan ya faɗi yadda suka yi da shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, Abba Hikima ya ce,
“Mun yi tattaunawa ta fahimta da ES Abba El-Mustapha a kan muƙabalar Mal. Shehi Mai Tajul Izzi, da Mal. Usman Mai Dubun Isa yau a ‘Censorship Board‘ wanda ya biyo bayan raɗin-raɗin hana dukkan wata muƙabala tsakanin sha’irai da kuma gayyatar mutanen biyu.
“Ina da fahimtar cewa duk da gyaran fuskar da aka yi wa dokar Hukumar Tace Finafinan ta Kano na shekarar 2025 ya ba ta hurumin kula da wani ɓangare na ayyukan sha’irai. Abin da ya faru tsakanin Mal. Shehi Mai Tajul Izzi, da Mal. Usman Mai Dubun Isa, duk da sha’irai ne, abu ne da ya shafi ‘yancin su na addini, tunani, muhawara, da bayyana wata fahimta, wadda dokokin ƙasa ya ba su damar yi. Kuma hakan idan aka yi shi cikin doka da oda zai taimaka wajen ilmantar da mutane.
“Saboda haka hukumar Shari’a Commission ko ma’aikatar addinai ita ta fi dacewa ta shiga wannan lamari ba Hukumar Tace Finafinai ba.
“Misali, duk da hukumar kula da likitoci tana da hurumi kan likitoci, za ta iya ɗabbaka wannan ƙarfi ne kawai yayin mu’amala da likitoci a aikin likitanci, ba a matsayin su na manoma ba ko ‘yan kasuwa ba.
“Saboda haka, sha’irai na da ‘yanci kamar sauran mutanen gari. Kuma kare musu ‘yanci abu ne mai muhimmanci kamar yadda taimaka musu wajen tafiyar da ayyukan su cikin bin doka da oda yake abu mai muhimmanci.”

A zaman nasu na yau, Malam Usman Mai Dubun Isa bai samu zuwa ba, sai dai wakilin sa ya nema masa uzirin rashin amsa gayyatar.
![]()







