IYAYE da ‘yan’uwa sun yi bikin taya Halima Abdulƙadir, wadda aka fi sani da Aisar, ‘yar fitacciyar marubuciya Ummulkhairi Sani Panisau, murnar cika shekaru biyar a duniya.
Aisar jika ce har ila yau ga tsohuwar marubuciya Sadiya Garba Yakasai.
Domin murnar zagayowar ranar, Hajiya Sadiya ta shirya mata bikin cika shekara a ranar Juma’ar da ta gabata.
An gudanar da bikin ne a gida a Kano, inda ‘yan’uwa na kusa, dangi da abokan arziki suka halarta domin taya Aisar murna.
Ummulkhairi tana daga cikin fitattun marubuta mata na wannan zamani, musamman a soshiyal midiya da intanet, inda ta yi fice wajen rubuce-rubucen adabi.
Sadiya Garba Yakasai (ta 2 daga hagu) da Ummulkhairi Sani Panisau (ta 2 daga dama) a lokacin bikin
A nata ɓangaren kuwa, Sadiya tana daga cikin tsofaffin marubutan Hausa da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa adabin Hausa tsawon shekaru masu yawa.
Masu bibiyar harkar adabi na ganin Ummulkhairi ta gaji basirar rubutu daga mahaifiyar ta, lamarin da ya sa ake kallon iyalin su a matsayin abin koyi wajen gadon fasahar rubutu a ƙasar Hausa.
Mahalartan taron sun yi wa Aisar fatan alheri tare da addu’ar Allah ya ƙara mata shekaru masu albarka, lafiya da nasara.