HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana sabon matsayi kan gayyatar Tijjani Gandu da ta yi dangane da fitar da wata da ya yi ba tare da tacewa ba, abin da take zargin ya saɓa wa dokokin ta.
A wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar yau Talata, 6 ga Oktoba, hukumar ta ce ta karɓi rahoton da ke tabbatar da rashin lafiyar mawaƙin ta hannun lauyan sa.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ruwaito cewa lauyan ya gabatar da rahoton ne a matsayin dalilin da ya sa Tijjani bai samu damar halartar gayyatar da hukumar ta yi masa a lokacin da aka tsara ba.
Sabuwar sanarwar ta ce bayan jami’an lafiya sun tabbatar wa da hukumar sahihancin rahoton, ta gamsu da bayanan da aka gabatar, tare da amincewa da rashin lafiyar a matsayin sahihin dalilin da ya hana mawaƙin amsa gayyatar.
Hukumar, wadda fitaccen jarumin Kannywood Alhaji Abba El-Mustapha yake shugabanta, ta ce za ta ci gaba da sanya lamarin a ido har sai Tijjani Gandu ya samu sauƙi, domin tabbatar da bin dokar da ta kafa hukumar.
Hukumar ta yi wa mawaƙin fatar samun sauƙi, tare da addu’ar Allah Ya ba shi cikakkiyar lafiya mai ɗorewa.
![]()






