ƊAN Kannywood ɗaya kacal daga cikin uku ne ya halarci gagarumin bikin karrama gwarazan Nijeriya tare da bajekolin saka tufafin zamani karo na 8 da gidan talbijin na Tozali ya shirya a Abuja a daren yau Asabar, 31 ga Oktoba, 2026.
An yi bikin a Los Angeles Events Centre da ke Ahmadu Bello Way, Abuja.
Alhaji Isa Bello Ja (Dattijon Arziki) shi kaɗai ne ya halarta ya karɓi awad ɗin sa. Sauran biyun, wato jaruma Amal Umar da mawaƙi Naziru Ahmad (Sarkin Waƙa) ba su samu damar halarta ba. Yayin da Naziru yana wajen aikin Umrah, ita kuwa Amal a ranar taron ma ta bar Abuja ta koma Kano saboda wani uziri.

Alhaji Isa Ja ya karɓa wa Naziru awad ɗin sa, yayin da Fati Nijar, wadda aka gayyato musamman ta yi waƙa a taron, ta karɓa wa Amal tata awad ɗin.
Bugu da ƙari, an karrama gwarzon soshiyal midiya ɗin nan mai suna Hausa Guy.
Sun karɓi kyaututtukan daga hannun Sardaunan Dutse, Alhaji Nasiru Haladu Danu, OFR.
Bayan waɗannan manishaɗantan, an karrama manyan mutane da kuma ƙungiyoyi waɗanda suka ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban Nijeriya ta fannoni daban-daban.

Taro ne na gani na faɗa. Matan tsofaffin shugabannin ƙasa guda biyu, wato Hajiya Maryam Sani Abacha da Hajiya Turai Umaru Musa Yar’Adua, sun halarta.
Akwai kuma Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara da tsohon gwamnan Jihar Neja, Dakta Babangida Aliyu (Talban Minna), da Ministar Al’adu da Ƙirƙira, Hajiya Hannatu Musa Musawa, da tsohon Minista Alhaji Bashir Ɗalhatu (Wazirin Dutse), tsohon Ministan Abuja, Alhaji Aliyu Umar Modibbo (Ɗanburam na Gombe), da Sardaunan Dutse Alhaji Nasiru Haladu Danu, da shugaban Jami’ar Baze, Alhaji Datti Baba-Ahmed, da sauran manyan baƙi da suka haɗa da ‘yan kasuwa da ‘yan jarida da malamai maza da mata da sauran su.
Bayan jawabai kan maudu’in taron, wato ceton waɗanda ta’addancin ‘yan bindiga ya shafa, musamman ma ‘ya’ya mata da ƙananan yara, an kuma yi gwajin ɗinkin tudafi na zamani.
Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Ɗalhatu, shi ne Ciyaman na Taron, yayin Hajiya Maryam Sani Abacha ita ce Uwar Taro.
Jagorar shirya bikin dai ita ce shugabar rukunonin kamfanonin Tozali Media Group, Hajiya Maimuna Yaya Abubakar.
An ci abinci da ruwa da lemuka.
An dai yi taro an kammala lafiya, kowa ya tafi cikin murna da annashuwa.
![]()







