FITACCEN mawaƙin siyasa Dauda Adamu Kahutu (Rarara) ya raba zunzurutun kuɗi har naira miliyan uku ga wasu zaɓaɓɓu daga cikin jarumai maza da mata a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood su sittin.
Kowannen su zai karɓi N50,000 a matsayin tallafin azumin Ramadan da ake ciki.
Rarara, wanda kuma shi ne shugaban kamfanin Rarara Multimedia da ke Kano, ya yi hakan ne a ranar Laraba, 14 ga Afrilu, 2021.
Da ma mawaƙin ya saba bayar da irin wannan tallafin a duk shekara a daidai lokacin da ake fara azumin.
Babban sakataren kamfanin na Rarara Multimedia, Aminu Yusuf Afandaj, ya shaida wa mujallar Fim cewa, “Akwai labaran da wasu daga cikin ‘yan soshiyal midiya ke yaɗawa na cewa Rarara ya ba wa mutane hamsin tallafi na naira dubu arba’in. Ba gaskiya ba ne. Rarara ya bada umarnin zaɓo wasu daga cikin ‘yan masana’antar waɗanda su ka tsufa da kuma matsakaita a cikin ta domin ba su wannan tallafin da za su yi amfani da shi a cikin wannan watan mai albarka na Ramadan.”
Maza 20 da mata 40 aka zaɓa domin amfana da tallafin.
Mazan sun haɗa da Malam Haruna Aliyu, Bashir Nayaya (Ɗanmagori), Malam Inuwa, Bala Anas, Ɗan Azumi Baba, Hankaka, Sani Idris Kauru (Moɗa), Sani SK, Sa’idu Gwanja, Mijinyawa da AGM Bashir.
Akwai kuma Ishaq Sidi Ishaq, Ibrahim Mandawari, Bello Ibrahim (Billy O), Shehu Hassan Kano, Isa Bello Ja, Garba Gashuwa, Bawa Maikanwa, Bashir Bala (Ciroki) da Auwalu Zomuleƙa.
An umarci duk wanda ya ji sunan sa a maza da ya garzaya zuwa wajen furodusa Abubakar Bashir Maishadda domin karɓar tallafin.
A ɓangaren mata kuma akwai Hajara Usman, Asma’u Sani, Rabi Sufi Hajiya Nas, Bilkin RK, Hajiya Sadiya Arewa24, A’ishatu Mahuta, Ladidi Tubeless, Matar Mamman, Baba Duduwa, Ladidi Fagge, Halima Kara da Kiyashi, Maryam CTV da Lubabatu Madaki.
Akwai kuma Safiya Kishiya, Hindatu Bashir, Anty Fandy, Hajiyan Aisha, Rahama MK, Ummi Nuhu, Zakiyya Ibrahim, Farida Jalal, Suwaiba Makauniya, Fati Baffa Fagge, Hadiza Kabara da Hajara Abubakar (Dumɓaru).
Akwai kuma Abida Muhammad, Hafsat Shehu, Fati Al-Amin, Maryam Giɗaɗo, Jamila Gamdare, Hauwa Waraka, Fati Slow, Maimuna Mohammed (Watayarinya), Maijidda Abdulƙadir, Fati Muhammad, Zuwaira Juda, Hafsat Iliyasu da Rahama Sirace.
Alfandaj ya ce su ma matan an umarce su da duk wadda ta ji sunan ta ta karɓi nata tallafin a wurin Aisha Humaira da Ummi Ibro.
Kafin wannan tallafin, a ‘yan watannin baya mawaƙin ya bai wa wasu daga cikin maza da mata iyaye a cikin wannan masana’anta su kimanin ashirin N50,000 kowannen su.
Haka kuma ya bai wa wasu daga cikin jaruman kyautar motoci da kuɗaɗe. Tijjani Asase da Jamila Nagudu na daga cikin waɗanda ya ba kyautar mota.







