• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Friday, July 25, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Sai da aka biya N5m kafin ‘yan bindiga su sako ni – furodusa Ali Bulala Gusau

by DAGA MUHAMMAD LAWAN RANO
July 26, 2021
in Labarai
0
Sai da aka biya N5m kafin ‘yan bindiga su sako ni – furodusa Ali Bulala Gusau
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

* Ashe ‘yan bindiga na kallon finafinan Hausa!


TSOHON shugaban ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), reshen Jihar Zamfara, Alhaji Aliyu Abdullahi  Gusau, ya bayyana cewa sai da aka biya kuɗin fansa naira miliyan biyar kafin ‘yan bindigar da su ka sace shi a makon jiya su sako shi.

Furodusan, wanda kuma aka fi sani da Ali Bulala Gusau, ya kuma faɗa bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kashe wasu mutum biyu da su ka tsare a gaban sa a sansanin su.

Idan kun tuna, a ranar 22 ga Yuli, 2021 mun ba ku labarin yadda aka kama furodusan tare da matar sa da ‘ya’yan sa a kan hanyar zuwa Sakkwato daga Gusau, amma daga baya iyalin nasa su ka kuɓuta.

A lokacin da ya ke labarta wa mujallar Fim yadda wannan ibtila’i ya same shi, Ali ya fara da cewa, “A ranar, Laraba 22 ga Yuli, 2021, wato 2 ga Babbar Sallah, na ɗauki ‘ya‘ya na huɗu da niyyar na kai su Sakkwato su gaida kakannin su tare da sabuwar amarya ta wadda ita ma zan kai ta gidan su a can ƙasar Nijar, su gaisa da ‘yan’uwan ta. 

“Mu na kan hanya mu na tafiya, wanda da man ni tun farko tafiyar ba na son ta kuma ba na so na ce ba zan je ba domin ita amarya ta lokacin da aka yi auren ta da ni dangin ta ba sa nan, to kuma da Sallah dangin ta za su zo. Haka ne ya tilasta aka yi tafiyar.  

“To a kan hanya ina tafiya, wanda mun zo daidai wani wuri da ake kira Lambar Makuwa, kafin a kai Dogon Ƙarfe, da misalin ƙarfe 11 na safe, sai na ce da iyalin nawa kowa ya fara addu’a saboda hanyar ba ta da kyau,.

“Haka nan mu ka shiga addu’a mu na tafiya. Mu na tafiya, sai na ji kamar na yi faci. Na faka. Ashe harbin bindiga ne! 

“Nan fa mu ka ga mutane su takwas ɗauke da bindigogi sun nufo mu su na harbi. Ni kuma sai faɗin, ‘Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un!’ na ke har su ka ƙaraso wurin mu.

“Ana cikin haka, sai ga wata mota ta fito daga Sakkwato su na gudu domin su kauce musu, amma haka su ka harbi motar ta faɗi. Su ka je su ka kashe na kashewa, sannan su ka dawo inda na ke su ka fara duka na a nan bakin titi.

“Su ka ce mu kwanta kafin nan kuma su tafi da mu cikin daji da ni da yara na da mata ta.

“Mu na cikin tafiya, kafin mu ƙarasa gun babban su, sai su ka tambaye ni mu su waye? Sai na ce masu, ‘Ni Babarbare ne bawan ku; in kun kashe ni kun kashe bawan ku. Waɗannan kuma yaran ‘yan’uwan ku ne, dukkan su Fulani ne, don ni ba na buƙatar Bahaushe ba na hulɗa da Bahaushe, ba na mu’amala da su ballantana na aura.’ 

“Daga nan kuma bayan mun yi haka da su sai su ka yi wa matata Fillanci, su ka ji ta mayar masu, da yara na. Sai su ka ce to a dakata, inji babban. ‘Tunda waɗannan ‘yan’uwan mu ne, mu yanzu ba ruwan mu da Babarbare. Aka ware ni gefe. Abin mamakin kuma shi ne ba mu da nisa da titi domin kuwa ina hango titi; daga gun da mu ke bai fi kilo mita ɗaya ba.”

Da yake bayani kan yadda matar sa da ‘ya’yan sa suka kuɓuta, Ali Bulala Gusau ya ce, “Bayan sun gama yare da mata ta da ‘ya’ya na guda biyu, da mu ke hannun su, sai babban su ya ce bari ya je ya kai su ya nuna musu wurin da ‘yan sanda su ke tsayawa domin bincike. Bayan ya nuna masu, ya ɗauki dubu uku ya ba su ya ce su nuna wa ‘yan sandan don su sa su a mota su koma gida. Yadda aka yi su ka kuɓuta kenan.

“Amma kuma da man tun da fari ban nuna masu cewa ina da wani alaƙa da harkar tsaro ba domin kuwa na ɓoye duk wata shaida da za ta nuna haka. Sannan su ka ɗauke ni su ka shige da ni dajin.

“Akwai kuma ‘ya’ya na biyu da su ka ɓace a daji lokacin da abin ya faru. Yaran su biyu ne, maza, da babba mai shekara 13 da kuma wani mai shekara 6. Amma su daga baya sai babban ya dawo gun mota ta ɗauke da yaron a bayan sa, ya shiga ya ɗauke mani duk wata shaida da za ta nuna cewa ina da alaƙa da jami’an tsaro. Sannan ya fito kan titi da yaron a bayan sa. 

“Su na jiran masu abin hawa, sai ga jami’an tsaro sun yo gangamin motoci za a raka Yariman Bakura. Sai su ka tsayar da su, amma kuma ba su tsaya ba, kuma sun gan su. Haka dai yaron nawa ya yi ta yi har sai da ya samu ya dawo gida.”

Bugu da ƙari, furodusan kuma ɗan kasuwa ya faɗa wa mujallar Fim abubuwan da su ka wakana bayan da masu garkuwar su ka yi awon gaba da shi zuwa cikin dajin da ke kusa da Lambar Makuwa, kusan nisan kilomita 60 daga Sakkwato.

A cewar sa, “Bayan mun shiga dajin, sun tambaye ni cewa a ina na ke aiki? Sai na ce masu ni malamin makarantar firamare ne a ƙauyen Cakal. 

“Su ka tambaye ni a wane wuri na ke zaune? Sai na ce ina zaune ne a Zauren Ɗangiwa, wato kusa da ƙauyen ne. Sai su ka tambaye ni me ya kawo ni cikin ƙauye da zama ina ɗan birni? Sai na ce masu kuɗin haya ne ya yi mani tsada, ba ni da kuɗin da zan iya kama haya. 

“Sai ya ce mani ya na zuwa. Nan take su ka kira a waya su ka tambaya wani mai ba su bayanai, su ka ce a gaya masu waye Ali? Aikin me na ke yi? Cikin minti goma aka kira su a waya aka gaya masu wanene ni. Su ka faɗi suna na, su ka ce kuma yaya na tsohon kwamishina ne na ilimi a Zamfara, sannan kuma ya na harkokin fim, ina da kuɗi.

“To bayan an faɗa masu, sai su ka ce tunda haka ne sai an bayar da miliyan 30 za a ba su. Su ka kira yaya na su ka gaya masa.

“To Allah ya sa shi yayan nawa da su ka kira shi lokacin da ya na kwamishina na ilimi ya gina masu makarantu a daji. Su ka ce, ‘Mu na da labarin yadda ka taimaka wa Fulani a daji, to za a yi maka sauƙi, darajar shi ba za a taɓa ka ba, ba za a kashe ka ba, ba za mu yi maka komai ba.”

“Su ka ce mani, ‘Saboda mu na da labari yayan ka ya na da kirki,” wato Ibrahim Abdullahi Spirow.

“Kafin nan kuma da man babban su ya gaya mani cewa ba sa kashe yaro ko mace ko tsoho; idan mutum aka gaza kawo kuɗin sa a fanshe shi to su na da haɗaka da ƙungiyar Boko Haram da ISWAP da kuma ƙungiyar Asiri duk wanda su ka kirawo su ka haɗa shi da mutum su yi ciniki su karɓi kuɗin su, su ba ruwan su. Amma dai ba sa kashe waɗannan mutane da na lissafa maka.”

Ali Bulala Gusau jim kaɗan da isowa gida bayan ‘yan bindiga sun sako shi

Har wa yau, Ali Bulala ya ce, “Bayan sun yi yarjejeniya da shi yaya na saboda mutuncin sa da su ke gani ya sa aka daidaita kan cewa za a bada kuɗi miliyan biyar.

“Haka dai ‘yan’uwa na su ka taru su ka zauna aka haɗa. Bayan haka yaya na ya tashi direban mota ya kawo kuɗin don a sake ni. 

“Shi ma a kan hanya ya na tafiya motar ta yi hatsari garin sauri, su ka faɗi da motar da kuma kuɗi a ciki da sauran kayan lemo wanda su ka buƙaci a taho masu da shi.

“Sai direban, bayan ya samu ya fito daga motar bai ji ciwo ba, ya tsayar da wata mota ya kira su ɓarayin da wata wayar ya gaya masu cewa ya yi hatsari. Sai su ka ce su ba su yarda ba.

“Nan take su ka ɗora mani bindiga a kai na, su ka ce masa nan da awa ɗaya idan ba a kawo kuɗin nan ba za su kashe ni. Sannan sai su ka kira yaya na a waya su ka gaya masa, su ka ce da man abin namu ƙarya ne, to idan ba a kawo kuɗin nan ba za su zo su ɗauki gawa ta. 
“Ana faɗin haka, sai yaya na ya suma. Ya san cewa da ƙyar aka haɗa wannan kuɗi, inda kuma ya yi sauri, aka tashi wata motar ta bi su hanya domin a cim masu a samu a kai kuɗin.

“Hakan kuwa aka yi. Nan da nan su ka zo, aka kawo kuɗin. Su ka rako ni wurin mota tare da ba ni dukkan kayayyaki na, su wayoyi na da sauran su.

“Kafin su sake ni ma sai da su ka roƙe ni a kan cewa in dinga yi masu addu’a a kan Allah ya shirye su, kamar yadda ogan nasu mai suna Kacalla ya gaya mani, kuma shi ne hatsabibin cikin su, kuma ya ba ni haƙuri da cewa don Allah in yafe masu; tunda ba su yi mani komai ba kuma ba su taɓa mutuncin iyali na ba in yi haƙuri in yafe masu. 

“Sannan na yi ta addu’a Allah ya yafe masu. Sannan ya ba ni labarin dalilin da ya sa su ka shiga wannan harkar; kamar yadda ogan su ya gaya mani, cewa wata rana ya je garin su ya ga ‘yan sintirin sa-kai sun shiga ƙauyen su sun yanka iyayen sa da ‘yan’uwan su, shi ya sa shi ma ya ɗauki alƙawarin hana Hausawa noma da kuma rungumar ɗabi’ar satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.”

Da wakilin mu ya tambaye shi batun kashe mutane biyu da aka ce masu garkuwa da mutanen sun yi a gaban sa, sai ya ce, “Haka ne, a gaba na sun kashe mutane biyu waɗanda ni na je na tarar da su a can a ɗaure, saboda sun nemi kuɗi, an kawo masu dubu ɗari uku. 

“Hakan ya sa su ka ce a mayar wa da iyalan su su raba gado, su ka zagaya da su baya su ka harbe su. Sannan su ka dawo inda na ke su ka ce in zo in ga yadda su ka kashe su. Sai na ce ba zan iya zuwa ba domin kuwa in na gani zan iya mutuwa. Su ka ce to idan ni ma ba a kawo kuɗi ba ni ma haka za su yi min.”

Ya kuma bayyana irin darasin da ya koya a wurin waɗannan mutane. Ya ce, “Gaskiya babu tsaro a Nijeriya, saboda ya za a yi daga wurin da mu ka kwana ina gano titi, sannan gaba kaɗan ga ‘yan sanda na musamman, wato ‘Special Task Force’ waɗanda aka kawo su daga Abuja su na duba ababen hawa, kuma lokacin da motar da za ta kawo kuɗin fansar ta gaban su ta wuce amma ba a tare ta an ce menene a cikin mota ba. 

“Hatta lokacin da aka sake ni, mun wuce da motar mu ta wajen, mun kuma tarar da ‘yan sanda su biyu da bindiga a hannu, su ka ɗaga mana hannu da cewa Allah ya kiyaye. Shi ya sa na ce babu tsaro. 

“Kuma su kan su mutanen nan su na cikin bala’i, sannan kuma na lura da cewa mutanen nan fa ba za su iya daina wannan ta’addancin ba saboda wanda ya saba kawai cikin minti biyar ya samu miliyan biyar ya za a yi ya koma kiwo a daji? Abin da ba zai taɓa yiwuwa ba kenan.”

Bugu da ƙari, Ali Bulala Gusau ya bayyana cewa bai samu wani taimako na kuɗi daga hannun wani ɗan fim ba, sai dai kawai su na ta yi masa addu’a da jaje.

Ya kuma bayyana cewa waɗanda su ka yi garkuwa da shi dukkan su matasa ne waɗanda shekarun su ba su wuce 17 zuwa 20 ba, sai babban su wanda shekarun sa ba za su wuce 25 a duniya ba.

Da ya ke ba gwamnati da sauran al’umma shawari kan wannan matsala, cewa ya yi, “In dai da gaske ake yi, dole ne a ɗauki matakin tsaro. Mutanen nan su nawa ne da jirgi ba ya iya ganin su ga su a filin Allah? Kuma idan ba kawar da su aka yi gaba ɗaya ba, ba za a samu zaman lafiya ba.

“Sannan kuma su na kallon finafinai da yawa, domin har a gaba na su na kallon finafinan su Ali Nuhu, Ibro da waƙoƙin su da dama, har da wa’azi ma sawa su ke yi su na ji.”
.A ƙarshe, ya gargaɗi jama’a da su kula da waɗanda su ke ma’amala da su saboda su na da masu kai masu bayanai daga cikin jama’a da dama. Ya ce lokacin da aka tambaye shi sunan sa da aikin sa, mutanen gari aka kirawo su ka bada bayanan sa.

Aliyu Abdullahi Gusau (Bulala)

Loading

Tags: Ali Bulala GusauAliyu Abdullahi Gusauhausa filmsInsecurity in NigeriaKannywoodMOPPANMotion Picture Practitioners Association of NigeriaZamfara
Previous Post

Hausawa Ko Turawa?

Next Post

Hirar mujallar Fim da Maryam Yahaya da mahaifin ta kan rashin lafiyar ta

Related Posts

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar
Labarai

‘Yan Kannywood sun kaɗu da rasuwar Abdoulfatah Omar

July 23, 2025
Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa
Labarai

Allah ya yi wa mahaifiyar darakta Salisu Mu’azu rasuwa

July 17, 2025
Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano
Labarai

Hukumar Shari’a da Hukumar Tace Finafinai za su haɗa gwiwa don tsaftace tarbiyya a Kano

July 11, 2025
Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 
Labarai

Jarumin Kannywood, Baba Ƙarami ya yi magana kan ganin sa da aka yi kan keken guragu 

July 10, 2025
Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a
Labarai

Tsohuwar jarumar Kannywood, Halisa tana neman addu’a

July 9, 2025
Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu
Labarai

Mawaƙin Manzon Allah, Abdullahi Ɗan Gano ya rasu

July 7, 2025
Next Post
Hirar mujallar Fim da Maryam Yahaya da mahaifin ta kan rashin lafiyar ta

Hirar mujallar Fim da Maryam Yahaya da mahaifin ta kan rashin lafiyar ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!