KWANA biyu yau da rasuwar fitacciyar zabiya Magajiya Ɗambatta, Jami’ar Maryam Abacha ta ƙasar Nijar (Maryam Abacha American University of Niger, MAAUN) ta bayyana cewa za ta ba ta digirin girmamawa.
Haka kuma jami’ar, mai reshe a Kano, ta raɗa wa ginin sashen Tsangayar Shari’a ɗin ta da ke Kano sunan zabiyar.
Shugaba kuma mamallakin jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, shi ne ya bayyana haka a cikin takardar ta’aziyya da ya aiko wa manema labarai daga ƙasar Faransa a yau Lahadi, 10 ga Oktoba, 2021.
A saƙon nasa, ya bayyana rasuwar shahararriyar mawaƙiyar a matsayin babban rashi ga ɗaukacin al’ummar arewacin Nijeriya.
A saƙon, Farfesan ya ce bayan sun yi la’akari da gudunmawar da marigayiyar ta bai wa al’umma ta hanyar faɗakarwa ne hukumar gudanarwa ta jami’ar ta sanya wa ginin sunan ta baya ga niyyar su ta karrama ta da digirin girmamawa na bayan rasuwa, wato ‘posthumous honorary degree’.

Ya ce, “Don girmama marigayiya Magajiya Ɗambatta (Halima Malam Lasan) da gudunmawar da ta bayar a fannin ilimi, mun yanke shawarar karrama ta da digirin girmamawa bayan rasuwa.”
Ya ƙara da cewa, “Mun yi shirin karrama ta a lokacin ta na da rai, amma sai ta rasu kafin lokacin taron.”
Kuma ya ce, “Za mu yi rashin barkwancin ta da shahararrun waƙoƙin ta.”
Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Jami’o’i masu Zaman Kan Su ta Afirka, ya bayyana rashin Magajiya Ɗambatta a matsayin abin takaici.
Ya ce a madadin iyalan sa da hukumar gudanarwar ‘Maryam Abacha American University’ da ‘Franco-British International University’, ya na miƙa ta’aziyya ga iyalai da abokan arzikin marigayiyar da ma ɗaukacin al’ummar Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah maɗaukakin sarki ya saka wa marigayiyar da gidan Aljannar Firdausi kuma ya ba iyalin ta juriyar haƙurin rashin ta.

Ita dai Halima Malam Lasan, wadda aka fi sani da Magajiya Ɗanbatta, ta rasu ne a shekaranjiya Juma’a, 8 ga Oktoba, 2021, a babban asibitin garin Ɗambatta da ke Jihar Kano, ta na da shekaru 85 a duniya.
![]()







