A YAU ne Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya cika shekara huɗu da rasuwa. Allahu Akbar! Allah ya jiƙan maza!
Ba za mu gaji da tuno da ayyukan sa na alheri ba. Haka kuma ba za mu gaji da sauraren yadda mawaƙa su ka kambama shi ba, su ka fito da martabar shi. Cikin su har da Alhaji Mamman Shata, wanda ya yi masa waƙoƙi da su ka haɗa da ‘Don Darajar Ado Ɗan Bayero’, ‘Mulki Sai Ado Ɗan Bayaro’, da kuma ‘Ado San Kano Ɗan Abdu’.

Daga cikin waɗannan waƙoƙi uku, ni dai babu wadda ke tsuma ni kamar ‘Don Darajar Ado Ɗan Bayaro’. Shi ya sa na zauna na rubuta ta, kamar haka:
AMSHI: “Don Darajar Ado Ɗan Bayaro”
–
Don darajar Ado ɗan Bayaro (2x)
–
Alhaji Shata zai tafi Birnin Kano,
Ni dai zan tafi Birnin Kano,
Don in gano Ado ɗan Bayaro.
–
A yanzu kowa ya sauka Birnin Kano,
Kowa ya kwana Birnin Kano,
Ya san an yi sarauta daidai,
In ya ishe Ado ɗan Bayaro.
–
Ya yi hawa uku ɗan Bayaro,
Cikon huɗu shi ya ka yi yanzu nan:
Farko yaz zama Ado Midil,
Kana ya yi Wakilin Gadi,
Ado ya zama Embasada,
A yanzun ya zama Sarkin Kano.
–
Mai daraja Ado ɗan Bayaro.
–
Tsofaffin birni na faɗi,
Dattawan birni na faɗi,
Rannan ina ta yawo birni,
Na’ ishe tsofaffi na fira,
Dattawan Birni na faɗi,
Tsofaffin Birni na faɗi:
“Mu dai tun daga Dabo na farko,
Hay yaz zo ga Ado ɗan Bayaro,
Hay yau ba ai ba yaron Sarki,
Tun lokacin Alu Mai Saje,
Sai kai Ado ɗan Bayaro.”
–
Shi dai Ado ɗan Bayaro,
Adalcin shi kamar Bayaro,
In yai hawa, kamar Bayaro,
In yai zaune, kamar Bayaro,
Hawan motas sa kamar Bayaro,
Hat tahiyas sa kamar Bayaro,
Amma halin sa halin Alu ne,
Halin yaƙi tamkar kakan sa.
–
Mai daraja Ado ɗan Bayaro.
–