Fitacciyar jarumar masana’antar finafinai ta Hollywood, wato Ashley Judd, ta na daga cikin ‘yan fim da su ka bayyana farin ciki da kama wani babban furodusa da ‘yan sanda su ka yi bisa zargin ya yi wa mata ‘yan fim fyaɗe ko kuma ya sanya su sun aikata masa wasu nau’o’i na jima’i ba tare da son ran su ba.
A jiya ne ‘yan sanda a birnin New York su ka kama Mista Harvey Weinstein, ɗaya daga cikin manyan furodusoshin duniyar nan, su ka gurfanar da shi a kotu.
Ashley Judd ta ce wannan kamu da aka yi masa ya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da mazan Hollywood da ke cin mutuncin mata yadda su ka ga dama.
Ta ce buga masa ankwa da aka yi wata alama ce da ke nuna nasarar da matan da ya keta wa haddi su ka samu a kan maza irin shi.
Haka kuma ta yaba wa ‘yan jarida da su ka dinga bada labaran abubuwan da su ka faru tsakanin matan da kuma furodusan.
Bugu da ƙari, Judd ta na nan ta na shirin shigar da wata ƙara a kotu a kan yadda a cewar ta Weinstein ya ɓata mata sana’a saboda ƙin amince masa ya yi amfani da ita.
Kamun da ‘yan sandan su ka yi samakon kukan da wasu ‘yan fim mata su biyu su ka kai wa ‘yan sanda.
Shi dai Weinstein, ya shiga cikin ruɗu ne lokacin da wata jaruma ta fasa ƙwai game da shi, ta ce ya taɓa yi mata fyaɗe.
Tun daga nan ne fa, a cikin 2016, wata tsohuwar ‘yar wasa ta ƙaddamar da kamfen a dandalin Twitter mai taken #MeToo inda ta yi kira ga duk wata mace da ta san Weinstein ko wani ɗan fim namiji ya yi wa fyaɗe ko ‘kan-ta-waye’ da ta fito fili ta fallasa shi.
Manufar su ita ce, fallasar za ta hana a ci gaba da musguna wa mata ta hanyar yin zina da su a masana’antar shirya finafinan.
Aƙalla mata 12 sun amsa kiran, su ka fito su ka fallasa manyan daraktoci da furodusoshi da sauran manyan Hollywood bisa zargin sun taɓa keta masu mutunci.
Wasu fitattun jaruman da su ka ce Weinstein ya ci zarafin su ta fuskar jima’i sun haɗa da Kate Beckinsale, Gwyneth Paltrow da Lysette Anthony.
Jaruma Rose McGowan, wadda ta ce Mista Weinstein ya taɓa yi mata fyaɗe, ta ce wannan kamu da aka yi wa babban furodusan “mataki ne na farko, kuma idan mu ka kai har ƙarshen wannan kes, ina fatan za mu cimma nasara.”
Mujallar FIM ta gano cewar waɗannan zarge-zarge da ake wa Mista Weinstein dai sun jawo masa fitintinu. Tun da farko dai kamfanin shirya finafinai na Weinstein Company, wanda shi ne ma ya kafa kamfanin, sun kore shi daga aiki, sannan aka rushe kamfanin baki ɗaya.
Sannan hukumar da ke gudanar da gasar Oscar ta ce babu ruwan ta da shi daga yanzu.
A watan Janairu na bana, sama da ‘yan fim mata su 300, da marubutan fim da daraktoci su ka yi karo-karon kuɗi, su ka tara dala miliyan ɗaya cikin wata ɗaya kacal don biyan lauyoyin da za su tafka shari’a a madadin ‘yan wasa mata da aka keta wa mutunci.
Amma shi Weinstein ya ƙaryata zargin da ake masa, ya na faɗin cewa duk macen da ya tara da ita, to da amincewar ta ne.
A kotu a jiya Juma’a, ya nanata matsayin sa na cewar duk ƙazafi ne ake masa.
Lauyan sa, Ben Brafman, ya ce za su yi hanzarin ƙaryata wannan zargi ta hanyar kawo ƙwararan hujjoji. Ya ce, “Mun yi amanna da cewa ba a bisa hujja aka gina zargin ba.”
Kotu ta bada belin Weinstein a kan kuɗi dala miliyan ɗaya tare da bada umarnin a laƙaba masa wani ƙarfe mai aiki da wutar lantarki a hannun sa domin a sa ido kan duk inda ya tafi, don kada ya gudu.
Wannan abin terere dai ya daɗe a kwance ba a fallasa shi ba. ‘Yan wasa mata (wani lokaci har da maza), musamman matasa sabon shigowa harkar fim, su kan ci karo da furodusa ko daraktan da zai buƙaci ya tara da su kafin ya sa su a fim, abin da a masana’antar finafinan Hausa ake kira da ‘kan-ta-waye’. Idan sun ƙi amincewa sai a danne su da ƙarfin tsiya.
Sau da yawa, su waɗanda aka danne ɗin su kan dake, ba su kai ƙara, saboda jin kunya ko kuma kada ƙoƙarin su na zama fitattun taurari ya samu cikas.
(Fim ta rubuta labarin tare da rahotannin wasu kafofin yaɗa labarai)