NAFISA Abdullahi, jarumar Kannywood wadda tauraruwar ta ke haskawa a cikin shiri mai dogon zango na ‘Labari Na’, a yau ta bayyana janyewar ta daga shirin.
A yammacin yau ne Nafisa ta faɗi cewa ba za ta ci gaba da fitowa a shirin ba.
Ta bayyana hakan a cikin wata wasiƙa da ta aike wa mashiryin shirin, Malam Aminu Saira, kuma ta wallafa kwafen ta a Facebook.

Haka kuma ta bai wa dubban masoyan ta haƙuri, tare da faɗa masu cewa ta janye daga shirin ne saboda ƙarancin lokaci da ta ke da shi.
Jarumar ta ce ta na so ta maida hankali kan kasuwancin ta da kuma kamfanin ta har ma da shirin fim da ta ke yi na ƙashin kan ta.
Da man dai jama’a sun daɗe su na ta raɗe-raɗin cewa Nafisa za ta daina fitowa a cikin ‘Labari Na’, ganin yadda ta fi maida hankali yanzu a harkokin ta na kasuwanci ba tare da ta na bai wa harkar fim lokaci ba kamar da.
‘Daya daga matsalolin shiri mai dogon zango kenan…akwai mutuwa wanda dole a canza jarumi, kuma ko ba mutuwa akwai irin hakan wanda dole a canza jarumi, ko a finafinan qasashen duniya ma na faruwa…Allah yasa mu dace