SHAHARARREN marubuci kuma ɗan wasan fim, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya bayyana dalilan da ke dakushe harkar rubutun Hausa, musamman a wannan zamanin.
Ya ce rashin haƙuri, rashin bin ƙa’idojin rubutu, rashin biyayya, rashin kuɗi da kuma abin da ya kira “kutse” su na daga cikin matsalolin da adabin Hausa ke fuskanta a yau.
Marubucin ya yi wannan maganar ne a cikin jawabin da ya gabatar a ranar Juma’a, 15 ga Nuwamba, 2019 a wurin taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa mai taken “Daidaitacciyar Hausa Da Ƙa’idojin Rubutun Hausa”, wanda Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ya gudanar.
A jawabin nasa, wanda mujallar Fim ta samu a wurin taron, Malam Ado ya ce, “Abin da ke damun marubuta, wanda wataƙila in aka haɗa ƙarfi za a iya magance shi.
“Na farko, akwai sauri da rashin haƙuri ga sabbabbin marubuta.
“Yau mutum zai fara rubutu, so ya ke a wannan watan ya kai littafin sa kasuwa. Dole a samu matsala. Ba shi da lokacin da zai kai wa mai dubawa.
“Ko da bai samu manyan malamai a jami’a ba, idan ya samu wanda ya san ya fi shi fahimta a ɓangaren adabi, idan ya ba shi, zai iya taimaka masa.
“Sannan na biyu kuma akwai rashin biyayya. Mafi yawa sababbin marubuta ba su yi biyayyar da mu mu ka yi ba. Na kan bada littafi na ga Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, Allah Ya jiƙan sa, ya yi wata shida ban karɓa ba; in ma ina da uzuri in je in dawo.
“Na uku shi ne rashin kuɗi da su marubutan su ke fama da shi. Wataƙila N100,000 ya ke da shi, wataƙila mai gyaran zai biya shi N30,000.
“Littafi kala biyu ne, akwai na sadaka, akwai na biya. Mu na sadaka mu ka rinƙa nema, shi ya sa sai mu jira har wata shida, kuma ana yi mana kyauta, saboda mu samu ƙaruwar kuskuren da mu ka yi.
“Amma yanzu in ka zo ka ce ga malamin Hausa ko ga ‘orthography’ ka ba shi a cikin wata ɗaya zai yi maka saboda aiki ne na kuɗi.
“Zan iya tunawa, akwai littafin da mu ka yi da Hausa da Fulfulde, na kashe kuɗi sama da N400,000.
“Na ƙarshe shi ne kutse da son rai da wasu marubuta a jaridu da mujallu su ke yi, na rubuta kalmar ‘muke’, ‘kake’ ‘suke’, sai su ke rarraba mana su a yanzu, kuma malaman jami’a su na gani a makaranta. Me ya kamata a yi?
“In da an yi wannan kalmomi an rarraba su, ‘yake’, ‘kake’, ‘suke’, ‘muke’, an zo an yi zama an tattauna, an ce a tattauna a yarda ga yadda tsayayyiyar Hausa ta ke, don me wasu za su dawo da jiya baya, bara bana, a ce haka za a rinƙa yi?
“‘Leadership Hausa’ su na daga ciki, kuma babbar jarida ce, ta na shiga duk duniya, an san ta. Haka ta ke rubuta, ‘ta ke’, ‘ya ke’, ‘su ke’, ‘mu ke’. Duk kuskure ne ni a fahimta ta ga yadda ƙa’idar rubutu ya ke. Da fatan in an ga waɗannan dole a gyara su.
“Wani ya yi maganar ‘billboard’, masu yin ‘billboard’ ɗin nan ba mutanen mu ba ne. Ba za ka rubuta ‘billboard’ da Inyamiranci ba kai ba Inyamiri ba, ba za ka yi da Yarbanci ba in kai ba Bayarabe ba ne. Don haka masu rubutun nan ba Hausawa ba ne, su ke rubuta mana yadda su ka ga dama.
“Ina bada shawara ko dai a ɗauki mataki ko kuma duk inda aka ga irin wannan kuskuren a sa ɗalibai su karya ‘billboard’ ɗin”.