MASU shirya bikin baje kolin finafinai ɗin nan na kudancin ƙasar nan mai suna Best of Nollywood Awards, sun bada tabbacin cewa a Kano za a yi bikin na bana.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in yaɗa labarai na bikin BON na 2019, Victor Ojelabi, ya saki, ya ce za a yi bikin ne a Kano a ranar 14 ga Disamba, 2019.
Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shi ne zai kasance babban baƙo.
Ganduje da kan sa ya ce Kano, wadda babbar cibiyar kasuwanci ce, a shirya ta ke ta karɓi baƙuncin mahalarta bikin.
Ya ce: “Mun yi murna da ya kasance masu shirya bikin karramawa na BON za su kawo ‘yan fim na ƙasar nan, na kudu da na Hausa, zuwa Kano, inda za su ga irin kyawu da kuma zaman lumana da Allah ya ba mu.
“Kano, wadda ita ce cibiya ta biyu a ƙasar nan wajen kasuwanci, bayan Legas, ta na da wuraren yawon shaƙatawa don baƙin mu su sha kallo.”
Gwamnan ya ba mashirya taron tabbacin cewa
gwamnatin sa za ta ɗauki nauyin dukkan bikin.
Ya ce, “A yayin da ake ƙoƙarin jawo jikin shugabannin shirin su tabbatar an yi taro an ƙare lafiya, mutan Kano na murnar karɓar ‘yan masana’antar Nollywood da hannu biyu-biyu.”
Shi bikin na Best of Nollywood Awards, a kan yi shi ne a duk shekara don bai wa masu ruwa da tsaki a harkar kyauttukan girmamawa na musamman.
An yi biki na farko ne a 2009 a bisa ɗaukar nauyin gwamnatin jihar Kano.
A bara, an yi bikin a ɗakin taro na Kakanfo da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
A lokacin, gwamnan jihar, Sanata Abiola Ajimobi, shi ne babban mai masaukin baƙi.
Ya zuwa yanzu an yi irin wannan bikin har guda tara a sassa daban-daban na Nijeriya.
Tags: Finafinai