• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, June 4, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Abin da ya sa Kannywood ta ke samun koma-baya a kowane zamani – Mahmud Daneji

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
January 16, 2023
in Labarai
1
Mahmud Mukhtar Daneji

Mahmud Mukhtar Daneji

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AN bayyana cewa rashin karɓar cigaba a duk lokacin da ya zo a kan lokaci da masu sana’ar shirya finafinan Hausa su ke yi shi ne ke jawo wa masana’antar su koma-baya wajen gudanar da harkar fim da ma kasuwancin sa.

Furodusa a Kannywood, Malam Mahmud Mukhtar Daneji, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke tattaunawa da mujallar Fim dangane da halin da masana’antar ta shiga.

Daneji, wanda sanannen darakta ne kuma jarumi, sannan marubucin labaran fim, ya ce: “Irin wannan  mizanin idan aka ce za a auna a tsakanin jiya da kuma yanzu, to sai ka koma baya ka ga me aka yi a bayan sai kuma ka auna da yanzu.

“A can baya ana ta kokawar abubuwan ba su karɓu ba ne. Kuma a tsakiya sun karɓu, saboda a lokacin ana samun kasuwanci na kai-tsaye.”

Daraktan ya bayyana abin da ya ke nufi a nan, ya ce: “Farko an yi fafutikar gina harkar. Mataki na biyu ta karɓu, ana samar da fim a kai shi kasuwa, wanda hakan ya sa ƙasashe da dama masu jin yaren Hausa da ma waɗanda su ke son su ji kamar Nijar, Kamaru, Chadi, kai har ma a Turai mutanen da su ke zaune a can da su ke so su ga gida su kan kalla don ya tuna masu gida da ƙasar su, don haka a lokacin ake samun cinikayya ta kai tsaye. 

“Abin da ya sa na ke cewa da kai ta kai-tsaye, saboda a wancan lokacin za ka buga abin ka ne a kaset ka kai shi kasuwa a ba ka kuɗin ka ko kuma a saka maka lokaci ka je ka karɓa.

“To amma a yanzu cigaban zamani da aka samu, ya sa komai ya sauya. Kamar na farko da ake amfani da kaset aka daina amfani da shi aka koma sidi; shi ma aka daina aka koma dibidi, yanzu kuma duk an daina amfani da wannan hanyoyin an koma onlayin. 

“Saboda haka a yanzu idan ba gidajen talbijin da su ke sayen kayan mu ba, yanzu sai dai YouTube channel, su ne yawancin ‘yan fim su ke yin amfani da su don cin riba.”

Daneji ya ce tun asali ita ƙasar Hausa da ma mutanen ta na da gardama wajen karɓar sabon abu idan ya zo. “Sai an ja, shi ma ya ja, ya ke karɓa, kuma sai ka samu kafin sannan duniyar ta ci gaba an bar shi a baya,” inji shi. “To, wannan ita ce matsalar da ta samu harkar fim.”

Daneji ya yi nuni da cewa lokacin da aka koma sidi ƙin karɓa aka yi har sai da lokaci ya ƙure aka karɓa. 

“Haka lokacin da aka koma dibidi, nan ma aka ce za a dunƙule fim uku a waje ɗaya, nan ma aka ƙi karɓa sai da lokaci ya ƙure, da duniya ta bi da mu, mu ka karɓa.

“To da kuma aka koma onlayin sai kawai mu ka koma mu ka zuba ido mu na cewa kasuwancin fim ya mutu saboda babu kasuwa ta kai-tsaye, mu ke ta fama da masu satar fasaha har sai da aka yi mana nisa sannan mu ka fara shiga mu ka yi tsalle zuwa YouTube, wanda kafin shi an ci kasuwa a onlayib da dama babu mu.

“A yanzu dai ya zama babu wata hanyar da za mu yi kasuwancin fim mu mayar da kuɗin mu har mu ci riba in ba a YouTube channel ko a sinima ba, saboda a sinima ana mayar da kuɗin da aka zuba a fim har ma a ci riba. Sai dai matsalar ita ce har yanzu sinima ba ta karɓu ba a ƙasar Hausa, don haka ba za ka je ba saboda ana kallon wajen a matsayin wajen iskanci, saboda ana yi mata kallon baya can, don haka ba ta karɓu ba. Amma a yanzu akwai sinima ta zamani da za ka je da iyalan ka ku zauna ku yi kallo.

“Sai kuma VOD (video on demand) wanda za ka biya kuɗi ka kalla kamar Northfilx da Kallo TV  wanda mai Kallo TV da ta zo ta kashe kuɗi sama da miliyan biyu, amma saboda bai karɓu ba kuɗin da ta samu har yanzu bai taka kara ya karya ba, saboda ba su da wannan al’adar.

“Haka shi ma YouTube idan ka bi dokokin su da tsarin da su ke tafiya a kan sa, idan yawan masu kallon ka su ka kai, to za su rinƙa biyan ka, amma dai ba hanyar samun kuɗi ba ne kai-tsaye, sai ka raini YouTube ka tara masu kallo ba kamar yadda za ka kai fim kasuwa a baya ka samu kuɗi kai-tsaye ba. 

“Wannan ya sa ake ganin ai harkar fim ta mutu. Kuma gaskiya ba mutuwa ta yi ba, ta zo da ci lgaban zamani ne. Kuma har yanzu masu samun kuɗi su na samu a cikin harkar fim, don akwai waɗanda duk wata su na samun kuɗi sama da miliyan biyu kuɗin Nijeriya, kuma a baya su ba wata tsiya su ke samu ba.

“To wannan shi ne cigaban da zamani ya kawo mana. Don haka ya zama dole masu harkar fim su yi haƙuri su karɓi cigaban zamani duk ta inda ya zo. In Allah ya yarda ba za a samu koma-baya ba.

“Don haka masu gudanar da harkar fim a Kannywood sai mu karɓi duk wani cigaban da ya zo mana cikin sauƙi, ba sai an yi mana nisa mu zo mu na kale ba.”

Loading

Tags: furodusaintanetKannywoodkasuwancin fimMahmud Mukhtar Danejionlayinsoshiyal midiyazamani
Previous Post

Akwai bambanci tsakanin rubutun labarin fim da na littafi – Bashir Ɗanrimi

Next Post

Rasuwar jarumin barkwanci Kamal S. Aboki ta girgiza Kannywood

Related Posts

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim
Labarai

MOPPAN ta ba gwamnan Kebbi lambar yabo a madadin ‘yan fim

June 2, 2025
Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22
Labarai

Ƙungiya ta ja kunnen gwamnatin Kano kan dakatar da finafinan Kannywood 22

May 20, 2025
Hukuma ta rufe gidajen gala a Kano har sai bayan Ramadan
Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da haska finafinan Kannywood 22 a intanet da talbijin 

May 19, 2025
Labarai

Gwamnan Kano ya ɗauki nauyin ‘yan Kannywood 5 zuwa Hajjin bana

April 17, 2025
Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu
Labarai

Sabuwa, matar Ɗanmaraya Jos, ta rasu

March 28, 2025
Next Post
Marigayi Kamal S. Aboki

Rasuwar jarumin barkwanci Kamal S. Aboki ta girgiza Kannywood

Comments 1

  1. Mohammed kawu ceto says:
    2 years ago

    Gaskiya kannywood batasamun cigaba sakamakon akawi wayanda basai sunyi karatu na shouting ba suke shiga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!