• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Rasuwar jarumin barkwanci Kamal S. Aboki ta girgiza Kannywood

by DAGA ABBA MUHAMMAD DA MUKHTAR YAKUBU
January 16, 2023
in Labarai
1
Marigayi Kamal S. Aboki

Marigayi Kamal S. Aboki

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

ALLAHU ya yi wa matashin jarumin barkwanci a Kannywood, Kamal S. Aboki, rasuwa a yau.

Kamal wanda ɗan asalin Maiduguri ne kuma mazaunin Kano, ya rasu sanadiyyar haɗarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar sa ta zuwa Kano daga Maiduguri.

Rasuwar Kamal ta ɗaga hankalin ‘yan fim, domin duk inda ka leƙa a soshiyal midiya hotunan sa ne da bidiyoyin sa ke yawo a jimamin rashin sa, musamman ganin shi yaro ne matashi.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa Kamal ya fara wasan barkwanci ne a Instagram, inda ya ke yin gajerun bidiyoyi ya na ɗorawa a shafukan sa, daga nan kuma ya koma YouTube. 

Marigayin ya na da masoya da mabiya da dama, kasancewar wasannin da ya ke yi su na nishaɗantar da jama’a.

Jarumi Abdullahi Amdaz, wanda ya na da kusanci da marigayin, ya bayyana jimami kan rasuwar Kamal, ya na cewa: “Kamal ɗaya ne daga cikin mutanen da su ka ɗauke ni tamkar ciki ɗaya mu ke. Ya na karɓar shawarat’ ta, ya kan kira ni ya gai da ni, ya zo inda na ke. Babban abin da yake burge ni da shi girmama mutane da fara’a.

Motar da ta yi haɗari da su Kamal S. Aboki

“Ba zan manta wannan ranar ba. Kamal Aboki ya ce da ni , ‘Oga bari na yi maka hoto, zan ajiye tarihin na yi tafiya da kai zuwa Maiduguri!’ Mu na wasa da dariya, na ce, ‘Ka ji ka da zolaya sai ka ce ka yi tafiya da wannan babban mutum!'”

Da ya tuno da wannan abu, sai Amdaz ya ce: “Cikin hukuncin Allah, ashe hoton ne zai zama tarihin ka a guri na. Allah ya yi maka rahama Kamal, domin Kamal ba ɗan barkwanci ba ne kawai, mutum ne mai hankali l, natsuwa da girmama mutane.

“Allah ya sani, ban san wani aibun Kamal da zan iya faɗa a duniya ba. Wannan ta sa dole mun ji zafin mutuwar sa, amma duk son da mu ke yi masa Allah ya na masa wanda ya fi namu, shi ya sa ya kira shi zuwa gare shi.

“Allah ya gafarta masa yasa aljanna makomar sa.”

To, amin ya Allah.

Kamal ƙwararre ne wajen wasan barkwanci a soshiyal midiya

Loading

Tags: Abdullahi Amdazhaɗarin motajimamiKamal S. AbokiKannywoodmutuwa
Previous Post

Abin da ya sa Kannywood ta ke samun koma-baya a kowane zamani – Mahmud Daneji

Next Post

Sabon salo: Daso na neman tallafi a bikin zagayowar ranar haihuwar ta ta

Related Posts

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta karɓi uzirin Tijjani Gandu

October 6, 2026
Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola
Labarai

Tinubu da Remi sun halarci bikin fara nuna fim kan gwagwarmayar Abiola

October 1, 2026
Cewar Ability: Ba mu kafa KAFIGAN don sharholiya a Kannywood ba
Labarai

Za a ƙaddamar da reshen Kaduna na KAFIGAN ranar Asabar

October 1, 2026
Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu
Siyasa

Zaɓen 2027: Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan fim da mawaƙan Arewa wajen sake zaɓen Tinubu

September 30, 2026
Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa
Siyasa

Ina roƙon Rarara ya saka ni cikin ‘Triple R’ domin in samu na abinci – Baba Duduwa

September 30, 2026
Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa
Siyasa

Guguwar zaɓen 2027: Sanata Barau Jibrin ya kori jaruma Rasheeda Maisa’a daga tafiyar sa

September 29, 2026
Next Post
Saratu Giɗaɗo (Daso)

Sabon salo: Daso na neman tallafi a bikin zagayowar ranar haihuwar ta ta

Comments 1

  1. Abba yakubu Ibrahim says:
    4 years ago

    Comment:Allah yagafartamasa yasa aljanna makoma intamu tazo Allah yasa mucika da imani Amen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!