BASHIR Ɗanrimi ya na ɗaya daga cikin marubutan labarin fim da su ke sharafin su a wannan lokaci. Sanannen marubucin littafi ne kafin ya dawo fagen fim inda damawa da shi. Ya na ɗaya daga cikin masu labarin fim ɗin nan mai dogon zango na ‘Daɗin Kowa’ da fim mai dogon zango na ‘Kwana Casa’in’, waɗanda ake nunawa a tashar talabijin ta Arewa 24.
A hirar sa da mujallar Fim, Bashir Ɗanrimi ya bayyana cewa irin nacin karatun da ya ke da shi tun ya na yaro ne ya kai shi ga samun nasarar zama marubucin da a yanzu ake damawa da shi. Ya ce: “A gaskiya tarihin rubutu na ya fara ne tun ina ƙarami, don kuwa zan iya cewa tun ban shiga makarantar firamare ba, saboda yadda na tashi a gidan akwai yayye na mata da su ke da yawan karatun littattafai, don haka duk lokacin da su ke karatun sai na zauna ina sauraron su, da haka har na fara karanta littafin da kai na, don ko lokacin da na shiga firamare ina aji uku na fara rubutu har ma idan ana so aji ya yi shiru sai a kirawo ni na karanta labari. To da haka na taso da son karatu da rubuta labari, da na fara girma kuma sai na fara sayen littafi da kuɗi na ina karantawa. Sai ya zama duk wani littafi da ya fito sai na karanta shi.
“Kullum ina hanyar kasuwar Sabon Gari ko bakin Asibitin Murtala wajen sayen littafi. Har ma na ke ƙure su, don sai na je na ga babu sabo
“Sai na koma karanta jarida. A nan ma sai ya zama babu wata jarida ko mujalla ta Hausa da ba na karanta ta.”

A game da yadda ya zama marubuci kuwa, cewa ya yi, ” Na fara rubutu ne a mujallar Inuwar Marubuta wadda ƙungiyar Marubutan Hausa ta ke bugawa a wancan lokacin. Sai na yi rubutu a kan wani littafi da na karanta na ga akwai kuskure.
“To, wannan rubutun ya yi tasiri sosai. Haka ya sa na fara rubuta littafi na mai suna ‘Baƙar Aƙida’, wanda ya shiga kasuwa a 2010. Daga nan sai na yi na biyun mai suna ‘Sharholiya’.
“Da na ga na ƙara samun ƙaruwa sai na yi na uku mai suna ‘Munawwara’. To wannan littafin shi ne silar zama na marubucin labarin fim.
“Don ba zan manta ba, a lokacin na kai wa Hajiya Umma Ali ta karanta, sai ta ce ta na son ta mayar da shi fim. Amma ba a yi fim ɗin da shi ba. Sai ta ba ni wani labarin na rubuta mata mai suna ‘Mizani’, kuma ina jin shi ne fim na ƙarshe da ta yi; ba ta ƙara yi ba har Allah ya yi mata rasuwa.
“To bayan shi sai aka ba ni aikin rubuta wani labari mai suna ‘Ɗan Baiwa’, to wannan rubutun labarin shi ne ya zamar da ni marubucin labarin fim da aka fara sani na har ake kawo mini aikin rubuta labari.”
Shin a cikin manyan finafinan da Bashir Ɗanrimi ya rubuta labarin su, wanne ne wanda ba zai manta da su ba? Amsa: “Akwai ‘Malam Zalimu’, ‘Idan Haka Ne,’ ‘Biki Budiri’, ‘Ana Bikin Duniya’. Waɗannan manyan finafinai ne da manyan jarumai su ka fito a cikin su. Don haka babu wani babban jarumi da bai fito a cikin labarin da na rubuta ba, har ta kai a yanzu an koma ana rubuta fim mai dogon zango ana damawa da ni, don a yanzu ina cikin marubutan labarin ‘Daɗin Kowa’ da ‘Kwana Casa’in’, tsawon lokaci mu mu ke rubuta labarin.
“Sannan ina yin wasu rubutun na gajerun labarai da na tarihi wanda wasu ƙungiyoyi da kamfanoni su ke ba ni aikin.”
Tunda kuwa haka ne, tilas Bashir Ɗanrimi ya san bambancin rubutun labarin fim da na littafi. Da mu ka tambaye shi kan hakan, sai ya ce: “A gaskiya akwai bambanci sosai, saboda shi rubutun littafi labari ya fi yawa, don a rubutun littafi ne za ka rubuta mutum ya tafi Amerika amma na fim sai ka kalli abin da za a kashe a wajen aikin, amma a littafi za ka iya rubuta abin da ya zo a zuciyar ka saboda tunani ne ya zo maka, kamar ka rubuta gida mai hawa uku ya ruguje amma a fim za ka yi tunanin ma yadda za a samar da gidan da yadda za a ruguza shi.

“To, gaskiya akwai bambanci sosai a tsakanin rubutun labarin fim da na littafi.
“Abu mai muhimmanci dai shi ne duk wanda zai yi harkar rubutun, to dole ne ya zama mai yawan karatu da bincike, don ta nan ake samun ƙwarewa da gano abubuwa masu muhimmanci.”
![]()







