ALƘAWARI ya cika. A jiya Asabar, 7 ga Janairu, 2023 aka ɗaura auren mai ɗaukar sauti a Kannywood, Bilal Muhammad Naseer (Lion).
An ɗaura auren su da abar ƙaunar sa, Jamila Isah Muhammad, da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gida mai lamba L.I. 18, Fulani Road, kusa da Ramadan Hospital, unguwar Nassarawa, Kaduna, a kan sadaki N100,000.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Shamsu Ɗan’iya, Abdul M. Shareef, Muhammad Maileri, Auta MG Boy, Rabi’u Rikadawa, Ramadan Booth da Tijjani Asase.
Kafin ranar ɗaurin auren, an buga wasan ƙwallon ƙafa a filin wasa na Kadwell da ke Barnawa.
Haka kuma, bayan ɗaurin auren, da misalin ƙarfe 8:00 na dare aka yi walima a Marafa Road, unguwar Ɗirkaniya.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.


![]()







