MUSA Abdullahi Sufi ba boyayye ba ne a harkar fim, domin kuwa ya dad’e ya na bada gudunmuwa a harkar a bangarori da dama. Jarumi ne, kuma furodusa, sannan mai tsara labarin fim ne. To sai dai an d’an shafe lokaci ba a ganin sa. Sai a kwanan baya da aka gan shi ya dawo a matsayin furodusa, inda ya d’auki nauyin shirya wani fim mai suna ‘Juyin Rayuwa’. Domin jin ko wanene Musa Abdullahi Sufi da kuma ayyukan da ya ke yi a cikin masana’antar Kannywood, wakilin mujallar Fim a Kano ya tattauna da shi.
FIM: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatu.
MUSA ABDULLAHI SUFI: To, assalamu alaikum. Da farko ni dai suna na Musa Abdullahi Sufi, kuma an haife ni a unguwar Dakata da ke cikin garin Kano. Na halarci makarantar firamare ta Kawaji da ke Jigirya, daga nan na yi babbar sakandire ta Kawaji, duk dai a nan Dakata. Bayan na gama, na tafi kwalejin share fagen shiga jami’a. Bayan na gama, na shiga Jami’ar Bayero inda na yi digiri na na d’aya da na biyu. A halin yanzu ina kan ci gaba da karatu a Jami’ar Maryam Abacha.
FIM: Ya aka yi ka samu kan ka a cikin harkar fim?
MUSA ABDULLAHI SUFI: To, harkar fim ina ganin zan iya cewa na samu kai na a cikin ta ne tun a shekarar 1997 zuwa 1999, inda na had’u da kamfanin Ummi Production mu ka yi wasu finafinai, koda yake tun kafin sannan tun ina makarantar firamare idan mu ka zo aji na kan yi k’ok’arin kwaikwayon abin da na kalla daga fim d’in Indiya wajen tsalle-tsalle da calikanci. Don haka duk wad’anda mu ka yi makaranta da su a lokacin sun san ni don ya kasance kullum na kan karya abin zama saboda rashin ji! Don haka ina da sha’awar harkar tun a wancan lokacin. To kuma daga baya sai na samu dama, mu ka yi wasu finafinai kamar su ‘Gumurzu’, da su ‘Rijiya’ da sauran makamantan irin wad’annan.
FIM: Amma tun daga wancan lokacin ba a sake jin ka ba sai a yanzu da ka fito da wani sabon salo a harkar fim a wani fim da aka shirya.
MUSA ABDULLAHI SUFI: E, gaskiya haka ne. Saboda yanayin karatu ne ya sa ban samu damar yin fim sosai ba, sai a wannan lokacin Allah Ya k’ara dawowa da ni inda a yanzu na shirya wani fim mai suna ‘Juyin Rayuwa’.
FIM: A yanzu ka fito a matsayin jarumi kuma mai d’uakar nauyin shiryawa. Ko a can baya ma irin wannan matsayin ka rik’e?
MUSA ABDULLAHI SUFI: E, to, fim d’i na na farko na fita ne a matsayin mugu, sai a ‘Rijiya’ kuma na fito a matsayin mai tallafa wa jarumi. To irin wannan dai matsayi na rik’e a baya, musamman ma a rol d’in mugun jarumi. Koda yake a fim d’in ‘Noor’ na fito a bangaren sarauta ne, duk da yake na kan yi wasan dabe, musamman a wajen da na yi bautar k’asa.
FIM: To bayan lokacin da ka shafe ka na gefe, me ya ba ka sha’awar dawowa harkar kuma a matsayin furodusa kuma jarumi?
MUSA ABDULLAHI SUFI: To, da yake ina yin finafinai da su ka shafi tarihin rayuwa da sauran abubuwa da su ke na gaske ne, ba k’irk’ira ba, kuma ina yawan tafiye-tafiye zuwa k’asashen duniya, hakan ya sa na ga akwai masu sha’awar finafinan mu, don haka sai na ga yaya za a yi na bada tawa gudunmawar. Don haka na fito da wasu abubuwa. Sannan su kan su masu kallon fim d’in namu su na da sha’awar su ga an shigo masu da sabbin abubuwa, domin ka san akwai bambanci tsakanin fim da kuma dirama. To su kuma yawancin mutane su na so su ga ana yin fim kamar yadda ake yin dirama. To kuma gaskiya ba haka ba ne, domin shi fim abu ne da ya ke nuna zamananci, don haka akwai abin da in a dirama ne za ka boye shi, amma a fim sai ka d’an fito da shi. Don ta haka ne zai nuna k’warewar aikin. Kamar misali, idan a dirama ne akwai inda misali in mace ta na zuwa makaranta idan za ta fita daga gidan su da doguwar riga, amma a ciki kuma k’ananan kaya ne. To ka ga idan a dirama ne watak’ila sai dai a fad’a da baki, amma a fim sai ka nuna cewa ga ta nan ta d’ora doguwar riga, sannan ka nuno ta lokacin da babu doguwar rigar a jikin ta. Wannan kad’an ne daga bambancin fim da kuma dirama.
Don haka na ke ganin wannan dama ce da na ke da ita don na ga wad’anne labarai za mu fito da su domin a ci gaba da ilimintar da mutane al’amuran da su ke faruwa a cikin al’umma. Saboda haka na yi amfani da wannan kamfani, Final Cut Studios, wajen fito da wannan fim da kuma sauran wad’anda za su zo a nan gaba.
FIM: Me ya sa ka d’auki salon ganin yadda sauran masu harkar su ke jin tsoron su zuba kud’in su su yi fim da ba na soyayya ba?
MUSA ABDULLAHI SUFI: To ni dai tun da na tashi a gida iyaye na sun nuna min sadaukar da abu don ka tallafa wa ’yan’uwa da sauran jama’a. To wannan dama ce da na ke da ita domin na saki kud’i na fito da wani abu da ake ganin cewar zai amfani jama’a. Don haka tare da tallafin iyali na mu ka yi wannan aiki don mu fito da abubuwan da ke damun jama’a a wannan lokacin. Kamar yadda mak’asudin abin shi ne yadda yara su ke yin shaye-shaye, su ke barin gidan su, da sauran su, wanda yawanci za ka ga ana ganin duk wanda ya ke aikata wannan abin shi ne ya ke da laifin. Sai a manta da dalilin da ya sa ya samu kan sa a irin wannan rayuwa. Saboda haka za ka ga cewa a labarin wad’annan yaran su biyu kowacce ga sanadin da ya sa ta fad’a harkar da ta ke ciki. Don haka shi wannan fim d’in mun yi k’ok’ari mun fito da wani abu wanda ya ke faruwa a cikin al’umma; sai ka ga uba ya mutu, k’anin uba ko wan uba ya hana wad’annan magada hak’k’in su, da sauran su.
FIM: Ganin ka d’auki lokaci ba ka yi fim ba, lokacin da ka tashi yin wannan aikin yaya ka samu kan ka a cikin ta?
MUSA ABDULLAHI SUFI: To, da yake kafin lokacin an rubuta kuma na samu abokan aiki da mu ke tare da su, kamar Abubakar Sulaiman Edita, Galadima Mahmud Ranriri, duk mun yi amfani da su a cikin wannan shiri. Kuma sun bayar da shawarwari, da kuma wanda ya bada umarni Habibu Yaro, da sauran su, wad’anda da shawarwarin su ne shirin ya samu nasara.
FIM: Me ya sa da ka tashi aikin ba ka d’auko manyan jarumai wad’anda ake yayi ba?
MUSA ABDULLAHI SUFI: To haka ne, wato za a ce ba a ga su Ali Nuhu, Sadiq Sani da sauran su ba. Gaskiya kamar yadda na fad’a, shi wannan fim an yi shi ne kamar somin tabi, kuma duk da haka jama’ar da su ka gani su na turo sak’wanni na godiya a kan yadda fim d’in ya amfanar da su. Domin har a zamantakewar aure fim d’in ya amfanar. Don haka mun samu nasarori sosai tun daga wajen aikin har zuwa kammaluwar sa. Domin su ma kan su abokan aikin nawa ban samu matsala da su ba. Wannan kuma ya samu ne sakamakon an bai wa kowa hak’k’in sa. Kawai dai jinkirin da aka samu shi ne wajen shigar da shi kauwa. Saboda ni na kasance mai abubuwa da dama a rayuwa ta, saboda ka ga kamar misali, ina yawan rubuce-rubuce, ga tafiye-tafiye da sauran aikin al’umma, don haka samun lokacin da za mu zauna mu fitar da shi sai ya zama aiki. Amma dai ina ganin nan ba da dad’ewa ba zai fita kasuwa.
FIM: Ba ka ganin hakan zai shafi kasuwar fim d’in ganin an dad’e ana tallar sa? A harkar fim d’in Hausa an saba a yi sauri a gama fim a shigar da shi kasuwa.
MUSA ABDULLAHI SUFI: To gaskiya babu gaggawa a cikin tsarin mu, domin duk inda gaggawa ta ke kamar yadda mu ka sani ana tare da shaid’an. Abu mai muhimmanci shi ne bayan ka gama aiki ka bai wa wad’anda za su kalla su ba ka shawara, shi ma wannan wani bangare ne da ya sa fim d’in bai fita ba har yanzu, kuma har yanzu ban gama rubuta yadda za a fassara shi zuwa Turanci ba. Kuma ya na cikin tsarin fim d’in, kuma a cikin wannan aikin na fasara har da wani farfesa da ya bada tasa shawarar kan yadda za a tsara fassarar zuwa Turanci.
![]()







