ALI Nuhu a yau ya bayyana shauƙin so ga iyalin sa a daidai lokacin da matar sa ke murnar zagayowar haihuwar ta.
Ya wallafa saƙo a soshiyal midiya kwana ɗaya bayan ɗan sa Ahmad ya wallafa nasa saƙon taya murnar ga mahaifiyar sa, Hajiya Maimuna Garba Ja Abdulƙadir, kuma a ranar da ita ma ‘yar sa Fatima ta wallafa nata saƙon taya murnar.
A rubutun da ya yi da Turanci, fitaccen jarumin, wanda ake wa laƙabi da Sarkin Kannywood, ya ce: “In a family life, love is the oil that eases friction, the cement that binds closer together, and the music that brings harmony.”
Mujallar Fim ta fassara wannan kalami da cewa: “A rayuwar iyali, soyayya ita ce man da ke sauƙaƙa saɓani, shi ne simintin da ke ɗaure ma’aurata su kasance makusanta, sannan shi ne sautin da ke kawo fahimtar juna.”

Shi kuwa Ahmad Ali Nuhu, ya wallafa saƙon sa game da wannan rana ta murna game da Hajiya Maimuna da cewa: “Happy birthday mom, you fill my days with joy and laughter, with you by my side I’m capable of anything, thanks for always comforting me when I was sad and making me laugh whenever I cried, thank you for all the years of love and affection. Happy birthday mom.”
Wakilin mu ya fassara saƙon kamar haka: “Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki mama ta. Ki na cika rayuwa ta da farin ciki da dariya. Kasancewar ki tare da ni ya sa ina jin zan iya tunkarar komai. Ina gode maki kan yadda a ko yaushe ki ke kwantar mani da hankali a lokacin da na shiga baƙin ciki, kuma ki na saka ni dariya a duk lokacin da na yi kuka. Ina gode maki saboda dukkan shekarun nan na so da ƙaunar da ki ke mani. Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki, mahaifiya ta.”
Ahmad ya ƙawata rubutun nasa da alamomin shauƙi masu nuna ƙauna, balo-balo, kek, sumbanta, murmushi, da kuma kyautar zagayowar ranar haihuwa.
Fatima kuma cewa ta yi, “It takes a special kind of lady to care for me. Happy birthday Mom.”
Manufa: “Sai mace ta musamman ce ta ke kula da ni. Barka da zagayowar ranar haihuwar ki, Mama.”
Ta ƙawata saƙon da alamun hoton kofin shan madara da kuma zuciya.
Ali ya tura saƙon sa tare da hoton da ya ɗauka tare da Maimuna da kuma ‘ya’yan su, wato Fatima da Ahmad, su na yanka kek ɗin murnar ranar. Su kuma Ahmad da Fatima kowanne ya tura nasa saƙon ne da hoton mahaifiyar sa ita kaɗai.

Dubban masoya sun tofa albarkacin bakin su kan waɗannan saƙwanni da mijin Maimuna ‘ya’yan ta su ka wallafa, inda su ka taya ta murna tare da yi wa iyalan ta addu’ar fatan alheri.
Su ma ‘yan fim ba a bar su a baya ba wajen taya maiɗakin ta Ali Nuhu murna, domin kuwa da yawan su sun yi rubutu a ƙasan saƙwannin, yayin da wasu kuma su ka sake wallafa hotunan da jaruman su ka tura a shafukan su.