• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, April 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Amira Souley, ‘yar shekara 24, ta lashe Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2022

by DAGA IRO MAMMAN
November 3, 2022
in Marubuta
0
Malama Amira Souley ta na karɓar kyautar karramawar ta a matsayin Gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022 daga hannun Hajiya Gumsu Abacha Buni, matar gwamnan Jihar Yobe (Hoto: BBC Hausa)

Malama Amira Souley ta na karɓar kyautar karramawar ta a matsayin Gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022 daga hannun Hajiya Gumsu Abacha Buni, matar gwamnan Jihar Yobe (Hoto: BBC Hausa)

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

AMIRA Souley, ‘yar shekara 24 daga ƙasar Nijar, ita ce ta lashe Gasar Hikayata ta Sashen Hausa na gidan rediyon BBC ta bana. 

An bayyana sakamakon gasar ne a wajen wani gagarumin biki wanda gidan rediyon ya shirya a ɗakin taro na Yar’Adua Centre da ke Abuja a daren yau.

Ban da satifiket da garkuwa, an kuma ba gwarzuwar gasar tukwicin dalar Amurka 2,000.

Wasu marubutan biyu, Hassana Labaran Ɗanlarabawa da Maryam Muhammad Sani, su ne su ka rufa mata baya a gasar, inda Hassana ta zo ta biyu, ita kuma Maryam ta zo ta uku.

Kamar yadda mujallar Fim ta ba ku labari a safiyar yau, Amira, wadda ‘yar shekara 24 ce, ta shiga gasar ne da labarin ta mai suna ‘Gudun Gara’ wanda ta shirya kan al’adar garar biki a ƙasar Hausa. 

Ita kuwa Hassana ta shiga ne da labarin ‘Haihuwar Guzuma’, yayin da Maryam ta shiga da labari mai taken ‘Al’umma Ta’.

An ba Hassana tukwicin dala 1,500, aka kuma ba Maryam dala 1,000.

Maiɗakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Hafsat Ganduje, ita ce ta ɗauki nauyin ba su waɗannan kuɗaɗen.

Hagu zuwa dama: Hassana Ɗanlarabawa, Amira Souley da Maryam Muhammad Sani (Hoto: BBC Hausa)

A yayin da ya ke bayyana zakarun gasar, Babban Editan BBC Hausa, Malam Aliyu Abdullahi Tanko, ya sanar da cewa a bara ma Amira ta shiga gasar har ta zo ta 12.

Amira ta samu takardar shaidar malanta ta NCE daga Makarantar Bawa Jangwazo da ke Maraɗi, yanzu kuma ta na koyar da Larabci a wata makarantar firamare a Maraɗi ɗin.

Waɗanda su ka miƙa mata kyautar a kan dandamalin taron su ne Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, da maiɗakin Gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Gumsu Abacha Buni, da Dakta Mohammed Sani-Gwarzo, Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Inganta Rayuwa ta Tarayya.

Gwarzuwar gasar ta yi jawabi a madadin abokan karawar ta, inda ta yi godiya ga BBC Hausa domin yadda gidan rediyon ke ba da dama ga mata su amayar da abin da ya ke cikin cikin su. Ta yi nuni da cewa matan Hausawa da dama su na da buƙatar su faɗi abin da ke ran su, amma ba su samun dama.

A wannan taro, har ila yau, an bayyana gwarazan gasar waƙar taya BBC Hausa murnar cika shekara 65.

Sha’irin da ya lashe gasar shi ne Shu’aibu Ibrahim Muhammad, wanda aka haifa a cikin 1972 a garin Lau, Jihar Taraba.

An ba shi tukwicin $2,000.

Na biyu shi ne Musa Abubakar Tunga, wanda zaɓaɓɓen kansila ne a Jihar Kebbi. An ba shi $1,500.

Ta uku ita ce fitacciyar zabiyar Kannywood, Zainab A. Baba, wadda aka ba tukwicin $1,000.

Hajiya Gumsu Abacha Buni, da tsohon Babban Hafsan Askarawan Nijeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, su ne su ka miƙa masa kyautar sa.

A jawabin da ya yi a madadin sauran sha’iran, Shu’aibu Ibrahim Muhammad ya ce: “Ba za mu iya kwatanta irin gudunmawar BBC Hausa ga adabin Hausa ba.”

A taron dai an gabatar da maƙaloli guda biyu a kan nasarori da tasirin Sashen Hausa na BBC, wato daga bakin Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da Mataimakin Jami’ar Tarayya ta Kashere, Farfesa Mohammed A. Pate. Dukkan su sun kawo tarihin BBC Hausa tare da kambama tashar rediyon, kuma sun ba tashar shawarwari kan aikin da ke gaban ta a sabon ƙarni na soshiyal midiya.

Masanin waƙoƙi, Farfesa Sa’idu Muhammad, ya yi jawabi kan alƙalancin gasar mawaƙa da ya jagoranta, yayin da Dakta A’ishatu Maimota ta gabatar da jawabi kan alƙalancin Gasar Hikayata da ta gabatar.

Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, ya na ba Amira Souley satifiket ɗin zama Gwarzuwar Gasar Hikayata ta bana

Alƙalan Gasar Hikayata ta bana dai su ne ita Dakta Maimota da Dakta Bashir Abu Sabe da Hajiya Hauwa Lawan Maiturare da Malam Minjibir na BBC Hausa.

A tsakiyar taron an kira sananniyar mawaƙiyar nan, Khairat Abdullahi, ta rera waƙar da ta yi wa BBC Hausa kan cika shekara 65.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ɗimbin jama’a maza da mata sun halarci taron, kuma an ƙarƙare da cin abincin dare wanda aka wadatar da shi ga mahalarta.

An tashi daga taron ana ta haba-haba da juna.

Shu’aibu Ibrahim Muhammad (na 2 daga hagu) lokacin da ya karɓi kyautar zama gwarzon gasar mawaƙan taya BBC Hausa cika shekara 65. A dama, shugaban BBC Hausa ne, Malam Aliyu Abdullahi Tanko
Wani sashe na mahalarta taron (Hoto: BBC Hausa)
Mawaƙiya Zainab A. Baba lokacin da ta karɓi kyautar karramawar ta

Loading

Tags: A'ishatu MaimotaAliyu Abdullahi TankoAliyu Muhammad BunzaAmira SouleyGasar HikayataGumsu Sani Abacha BunigwarazaHassana ƊanlarabawamarubutaMaryam Muhammad SanimatamawaƙaMohammed A. PateSa'idu Muhammad GusauYar'Adua Centrezakarun gasa
Previous Post

Shin ƙungiyar 13×13 ta yi tuntuɓe a tafiyar ta ne?

Next Post

BBC Hausa za su bayyana gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022 a yau

Related Posts

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro
Marubuta

Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya: Sanarwar Bayan Taro

January 10, 2026
Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama
Marubuta

Taron Ranar Marubutan Hausa ta Duniya ya gabato, shirye-shirye sun kankama

December 25, 2025
‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa
Marubuta

‎Sanata Shehu Sani ya ba gwarazan gasar Hikayata kyautar miliyan ɗaya a taron liyafa

December 25, 2025
Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo
Marubuta

Ban san farin ciki yana hana barci ba sai da aka ce ni ce ta ɗaya a gasar Hikayata – Fadila Lamiɗo

December 24, 2025
Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu
Marubuta

Buri na shi ne saƙonnin da suke cikin rubutu na su zama masu tasiri ga al’umma – Hauwa Shehu

December 19, 2025
Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata
Marubuta

Gidauniya ta ƙaddamar da littattafai biyu domin inganta rayuwar mata

December 8, 2025
Next Post
Hagu zuwa dama: Hassana Labaran Ɗanlarabawa, Amira Souley da Maryam Muhammad Sani a ofishin BBC Hausa a Abuja (Hoto: Ibrahim Sheme)

BBC Hausa za su bayyana gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022 a yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!