TUN shekaranjiya aka gina kabarin da aka rufe shahararren marubuci kuma ɗan wasan kwaikwayo a ciki, Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina (Kasagi), wanda Allah ya ɗauki ran sa a yau, inji wanda ya haƙa kabarin.
Kasagi ya rasu ne da asubahin yau bayan gajeruwar rashin lafiya, ya na da shekara 71 a duniya.
Mai haƙar kabari a maƙabartar Sabuwar Unguwa da ke Katsina, Malam Musa Ibrahim, ya faɗa wa mujallar Fim jim kaɗan bayan jana’izar Kasagi cewa an gina kabarin kwana biyu da su ka gabata don rufe wata mata da ta rasu, to amma sai ba a kawo matar wannan kushewar ba.

Ya ce: “Wannan kabari kwanan shi biyu. An yi shi ne da niyyar wata mata. An ce ta na da kauri… aka kawo tukunya guda aka rufe, ka gan ta can. Sai yanzu da sahe sai su ka ce mani ai Alhaji Allah ya yi mashi wa’adi. Shi kenan, sai na ce ai ko akwai ƙabarin. Su ka sawo tukwane, aka zo aka cire wa’incan aka sa nasu. To wa’incan su ne za a maida ga wancan ɗan gudun hijira.”
Ya yi addu’ar Allah ya yi wa Kasagi rahama.
Wakilin mujallar Fim ya ziyarci gidan mamacin a Sabuwar Unguwa cikin birnin Katsina, sai dai bai samu damar zantawa da wani daga cikin iyalin sa ba saboda halin kiɗimewar da su ke ciki.
Wakilin namu ya tarar da taron mutane masu zaman makoki da karɓar gaisuwa, ciki har da tsohon abokin diramar Kasagi ɗin, wato Alhaji Najume Muhammed (Idon Mujiya a wasan ‘Samanja Mazan Fama’) wanda ya bayyana alhini kan wannan babban rashi da aka yi.
Alhaji Najume, wanda cikakken sunan sa shi ne Lawal Muhammed Sani, ya bayyana cewa Kasagi ɗan’uwan sa ne na jini, kuma ɗan’uwa ne na harkar dirama inda su ka shahara.

Ya ce marigayin mutumin mutane ne, mai barkwanci, kuma bai rufe magana idan ya na so ya faɗe ta. Ya ce waɗannan halaye su na daga cikin dalilan da su ka sa ya ke ƙaunar shi.
Alhaji Najume ya ce haɗuwar su ta ƙarshe da Kasagi zai kai wata huɗu yanzu.
Game da dalilin rasuwar sa, ya ce da farko dai Kasagi ya yi fama da ciwo na ƙafa tsawon lokaci, ga girman shekaru, to kuma sai ya gamu da rashin lafiya inda har aka ɗan kwantar da shi a asibiti sannan da ya samu sauƙi sai aka sallamo shi. “Ashe sauƙin tafiya be,” inji shi.
Shi dai Kasagi, ya taɓa yin cikakkiyar hira da mujallar Fim wadda aka buga a watan Mayu na shekarar 2014 inda ya bayyana tarihin rayuwar sa da ayyukan da ya yi da yadda ya shiga harkar dirama da kuma yadda ya rubuta littattafan sa na wasan kwaikwayo, wato ‘Kulɓa Na Ɓarna’ da ‘Ai Ga Irin Ta Nan’.

Ya bayyana cewa an haife shi ne a Katsina a wajen 1950. Ya yi firamare ta ‘Central Elementary’ daga 1960-1965.
A 1965 ya shiga ‘Provincial Secondary School’, Katsina, ya gama a 1972 bayan wani tsaiko da ya samu sakamakon rashin lafiya.
Ya fara aiki a Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Kaduna a 1973. A lokacin ne su ka riƙa yin wasan kwaikwayo da su Ƙasimu Yero.
Da aka ƙirƙiro Hukumar Raya Al’adun Gargajiya sai aka maida shi can.

A 1975 ya je Ingila karatun aikin silima da talabijin. Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bi shi can ta ɗauke shi aiki a cibiyar ta ta raya al’adun mutanen Arewa. An ɗauke su tare da Ƙasimu Yero.
A nan ya ci gaba da aiki har zuwa lokacin da aka ƙirƙiro Jihar Katsina a 1988, wanda ya sa ya koma Hukumar Raya Al’adun Gargajiya ta jihar a matsayin Mataimakin Darakta.
A 1992 ya sake komawa Jami’ar Ahmadu Bello, ya ci gaba da aiki har zuwa 1992 lokacin da ya yi ritaya daga aikin gwamnati. Daga nan jami’ar ta ɗauke shi aikin kwangila, ya na koyar da yadda ake shirya dirama.

Marigayi Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina ya rubuta wasannin kwaikwayo ba iyaka, daga ciki aka wallafa biyu a matsayin littafi, wato ‘Kulɓa Na Ɓarna’ da kuma ‘Ai Ga Irin Ta Nan’.
Kasagi ya ce akwai ma wasu littattafan nasa da dama waɗanda ba a buga su ba.
Memba ne a Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Katsina.
Kasagi mutum ne mai tsananin son kyautata al’adun gargajiya, kuma bai gamsu da yadda ake shirya finafinan Hausa na wannan zamani ba.
Ganin sa na ƙarshe da jama’a su ka yi shi ne a wajen taron baje kolin littattafan Hausa wanda Farfesa Ibrahim Malumfashi ya shirya a Gidan Arewa, a Kaduna, mako biyu da su ka gabata.

Labarin rasuwar sa ya bazu kamar wutar bazara a kafafen yaɗa labarai, inda ake ta yi masa addu’a.
Allah ya jiƙan shi, ya sa mutuwa hutu ce a gare shi, amin.
Allah ya rahamshe shi