JAGORORIN harkar finafinan Hausa sun amince da naɗin furodusa kuma darakta Ahmad Salihu Alkanawy a matsayin shugaban Kwamitin Zaɓe na uwar ƙungiyar su ta ƙasa, wato MOPPAN.
Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin takardar sanarwa ga manema labarai wadda kakakin ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, ya rattaba wa hannu a jiya.
A takardar, wadda mujallar Fim ta samu kwafen ta, Ciroma ya bayyana cewa zaɓen Alkanawy a wannan matsayin ya biyo “bayan doguwar tattaunawa da shawarwari da kuma tuntuɓar wakilan kwamiti.”
Ya ƙara da cewa shugaban MOPPAN na ƙasa, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, ya amince da matsayar da aka cimma a tarukan shugabanni game da naɗin kwamitin zaɓen.
Ciroma ya bayyana sunayen membobin kwamitin kamar haka:
1. Ahmad Salihu Alkanawy – Ciyaman
2. Ahmed S. Bello – Sakatare
3. Bello Shehu Achida – Memba
4. Haruna Mohammed Godowoli – Memba
5. Mohammed Ibrahim Gumel – Memba / Ma’aji
Bugu da ƙari, ya ce uwar ƙungiyar ta ba su sharuɗɗa da ƙa’idojin gudanar da aikin su kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙungiya ya gindaya, ciki har da yadda za su gudanar da zaɓen da yadda za su tantance ‘yan takara da masu zaɓen su, da sauran su.

A cewar sa, sharuɗɗan da ƙa’idojin su na da dama, amma dai mafi muhimmanci su ne:
1. Gudanar da zaɓe a kan doron kundin tsarin mulkin MOPPAN.
2. Tabbatar da adalci yayin gudanar da harkokin zaɓen gaba ɗayan su.
3. Tabbatar da cewa halastattun ‘ya’yan MOPPAN masu rijista da ƙungiya ne za su tsaya takara kuma su ne za su yi zaɓe.
4. Tabbatar da cewa duk wanda ya taɓa yi wa kundin tsarin mulkin MOPPAN karan-tsaye ko ya taɓa cin amanar ƙungiya bai fito takara ba.
5. Samar da zaɓe da sabon shugabanci kafin wa’adin wannan zagon mulki ya ƙare.
Ciroma ya ce, “Idan kuwa bisa wasu dalilai an samu jinkiri, to majalisar amintattun MOPPAN ce kawai ta ke da ikon ƙara masu lokaci ko ɗaukar matakin da ya dace.”
Ya yi fatan Allah ya yi wa ‘yan kwamiti jagora ya kuma ba su ikon gudanar da zaɓe mai tsafta da zai amfanar da ƙungiyar MOPPAN da ‘ya’yan ta.
Nayi farin cikin ganin Alkanawy a matsayin Shugaban zabe na MOPPAN Alkanawy mutunne Mai kwazo da kishin Kungiyar MOPPAN Nayi aiki dashi nasan ko shi wanene
Allah ya tayasu wannan aiki