• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, August 25, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta haramta mutunta mugaye a cikin finafinai

by DAGA IRO MAMMAN
September 7, 2021
in Labarai
0
Alhaji Adedayo Thomas

Alhaji Adedayo Thomas

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

GWAMNATIN Tarayya ta ce daga yanzu ba za ta bari wani fim mai mutunta mugaye ya fito ba.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa mugaye a cikin wasan fim dai su ne mutane da ke aikata ta’asa kamar sata, fashi, fyaɗe, kashe-kashen rayuka, ta’addanci da sauran su. Da Turanci ana kiran su ‘villains’.

Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta ce daga yanzu ta haramta duk wani fim mai nuna cewa irin waɗannan ɓatagarin sun yi galaba ko kuma abin koyi ne.

Shugaban hukumar, Alhaji Adedayo Thomas, shi ne ya bayyana haka a cikin jawabin da ya yi a jiya Litinin, 6 ga Satumba, 2021 a wajen buɗe wani taro na kwana biyar na ƙara wa juna sani a kan tsarin tace finafinai da karkasu su don masu kallo wanda aka shirya wa wasu zaɓaɓɓun ɗaliban Jami’ar Kalaba.

A jawabin, wanda mujallar Fim ta samu kwafen sa, Thomas ya ce: “Ya dace finafinan Nijeriya su nuna gaskiyar abin da ke faruwa, to amma a ƙarshe su koyar da darussan tarbiyya. Ya kamata finafinan mu su ɗauki wata matsala, su yi aiki a kan ta amma fa a ƙarshe su nuna abin da ya faru ga masu aikata mugun abu a cikin fim.

“Amma idan ka shirya fim inda a ciki ka kambama ko ka nuna jin daɗi kan abin da wani wanda ya aikata ta’asa a kan al’adu ko zamantakewar ɗan’adam ba tare da hukunci a kan sa ba, ba za mu amince da irin waɗannan finafinan ba.”

A lokacin taron, Thomas ya bayyana cewa kamar yadda gwamnatin Buhari ke ƙoƙarin sanya ido kan muggan kalamai da ake yaɗawa a soshiyal midiya, ita ma tasa hukumar ta na duba abin da finafinan da ake turawa a Google da YouTube su ka ƙunsa.  Ya ce haka kuma hukumar za ta sa ido kan yadda ake rubuta labaran fim (wato ‘scripts’). 

Bugu da ƙari, shugaban ya gargaɗi masu shirya finafinai da ke zagaye hukumar su na sakin fim ba tare da an ba su izini ba.

Ya ce, “Duk da yake mu na sane da wasu da ke karya doka su na fitar da finafinai ba tare da sun biyo ta hukumar NFVCB ba, mu na so ɗalibai su fahimci ayyukan hukumar saboda su ilmantu da su.”

A cewar sa, gwamnati na so ta ga cewa masu shirya finafinai su na fito da finafinan da su ka dace da tarbiyya da nufin kare ƙananan yaran Nijeriya daga illolin da ke faruwa a cikin al’umma.

Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: adedayo thomasCensorship in NigeriaHukumar Tace Finafinaimovie villainsNational Film and Video Censors BoardNFVCBNigerian filmsUniversity of Calabar
Previous Post

An naɗa Ahmad Alkanawy shugaban kwamitin zaɓen MOPPAN

Next Post

Membobi mata: Halisa da Tubeless sun shiga kwamitin zaɓen MOPPAN

Related Posts

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe
Labarai

Mutuwar aure na ƙaddara ce – Jaruma Khadija Yobe

August 23, 2026
Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi
Labarai

Aina’u Ade ta raba wa tsofaffin jaruman Kannywood tallafin kuɗi

August 23, 2026
Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti
Labarai

Ƙungiyar ‘Triple R Kannywood’ ta ziyarci jarumi Tanimu Akawu a asibiti

August 23, 2026
Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000
Labarai

Ƙungiyar Triple R ta ba jarumin Kannywood Mustapha Musty tallafin N500,000

August 18, 2026
Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye
Labarai

Yadda na gamu da ibtila’in karaya a ƙafa – Jarumi Ɗan’azumi Kamaye

August 14, 2026
Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba
Labarai

Tozali TV zai yi bikin Henna Ball da karrama masu ƙwazo da tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-hare a ranar 31 ga Oktoba

August 8, 2026
Next Post
Membobi mata: Halisa da Tubeless sun shiga kwamitin zaɓen MOPPAN

Membobi mata: Halisa da Tubeless sun shiga kwamitin zaɓen MOPPAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!