• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Wednesday, May 6, 2026
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Membobi mata: Halisa da Tubeless sun shiga kwamitin zaɓen MOPPAN

by DAGA IRO MAMMAN
September 7, 2021
in Labarai
1
Membobi mata: Halisa da Tubeless sun shiga kwamitin zaɓen MOPPAN
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinai a Kannywood (MOPPAN) na ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya amince da a ƙara fitattun jaruman nan Halisa Muhammed Abdullahi da Ladidi Abdullahi (Tubeless) a cikin Kwamitin Zaɓe na ƙungiyar.

Kakakin ƙungiyar, Malam Al-Amin Ciroma, shi ne ya bayyana haka a cikin takardar sanarwa ga manema labarai wadda ya fitar a yau.

A sanarwar, wadda mujallar Fim ta samu kwafen ta, Ciroma ya ce wannan mataki da aka ɗauka “ya biyo bayan waɗansu ƙorafe-ƙorafen da aka samu daga wasu ‘ya’yan masana’antar na buƙatar a sanyo mata a ciki.”

Ya ce sakamakon tattaunawa da ta gudana a zauren shugabanni na MOPPAN a mataki na ƙasa da wasu masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood dangane da buƙatar ƙarin membobi mata a cikin kwamitin zaɓen ne ya sa aka yanke shawarar a “ƙara wasu daga cikin zaratan membobin Kannywood mata cikin kwamitin.”

Ciroma ya ce ba tare da ɓata lokaci ba, zauren na shugabanni ya amince da cewa shugaban Kwamitin na Zaɓe, Malam Ahmad Alkanawy, ya sanya waɗanda aka ƙara a cikin kwamitin, wato Hajiya Halisa da Hajiya Ladidi Tubeless, cikin membobin sa domin gudanar da aiki, bisa ƙa’idojin aiki da aka shimfiɗa masu. 

Idan ba a manta ba, mujallar Fim ta kawo labarin kafa kwamitin zaɓen da MOPPAN ta yi, inda aka bayyana sunayen mutum biyar a matsayin membobin kwamitin.

To amma labarin na fita, sai fitacciyar furodusa kuma marubuciya, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, ta yi nuni da cewa an ware mata a cikin lamarin, kuma ta yi kira da a gaggauta yin gyara ko kuma su matan industiri su yi abin da ta kira “tawaye” ta hanyar yin zanga-zanga.

A cikin wani saƙon gaggawa da ta tura a guruf ɗin ƙungiyar matan Kannywood (Kannywood Women’s Association of Nigeria, K-WAN), mai taken “Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga K-WAN”, Hajiya Balaraba ta faɗa a cikin ɓacin rai cewa: “Ina ‘yan tawayen ‘ya’ya na na gidan nan? To yanzu ga ranar ku! Ban taɓa goyon bayan ku yi zanga-zanga ba sai yau. 

“An kafa kwamiti babu mace ko ɗaya.

“Ku fito mu ƙwaci ‘yancin mu. Idan ba a saka mace ba, duk mu yi tawaye!”

Hajiya Balaraba ta turo wannan saƙo ga mujallar Fim, kuma ta tura shi a guruf ɗin shugabannin masana’antar, wanda hakan ya sa aka tattauna a kan lamarin.

A ƙarshe, shugaban MOPPAN, Dakta Sarari, ya bada sanarwar cewa kwamitin zartaswa na ƙungiyar zai duba koken da Hajiyar ta kawo domin yin gyara.

Yanzu dai membobin kwamitin su ne:

1. Ahmad Salihu Alkanawy – Ciyaman
2. Ahmed S. Bello – Sakatare
3. Bello Shehu Achida – Memba
4. Haruna Mohammed Godowoli – Memba
5. Mohammed Ibrahim Gumel – Memba / Ma’aji
6. Halisa Muhammed Abdullahi – Memba
7. Ladidi Abdullahi (Tubeless) – Memba

A sanarwar farko da ya fitar kan kafa kwamitin, Ciroma ya yi fatan Allah ya yi wa ‘yan kwamiti jagora ya kuma ba su ikon gudanar da zaɓe mai tsafta da zai amfanar da ƙungiyar MOPPAN da ‘ya’yan ta.

Copyright © Fim Magazine. All rights reserved.
www.fimmagazine.com

Loading

Tags: Ahmad Muhammad SarariAhmad S. AlkanawyAl-Amin CiromaBalaraba Ramat YakubuHalisa Muhammedhausa filmsKannywoodKwamitin ZabeLadidi TubelessMOPPAN
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta haramta mutunta mugaye a cikin finafinai

Next Post

Hotunan Adamu Nagudu da iyalin sa tare da fatan alheri

Related Posts

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim
Labarai

Rasuwar dattijon Kannywood, Nura Shareef, ta girgiza ‘yan fim

February 22, 2026
Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza
Labarai

Daraktar fim ta ƙi karɓar awad saboda kisan gillar da Isra’ila take yi a Gaza

February 21, 2026
Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai
Labarai

Fitaccen furodusa Kunle Afolayan ya yi haɗin gwiwa da Jamhuriyar Benin kan shirya finafinai

February 19, 2026
An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa
Labarai

An naɗa Farfesa Tengya matsayin sabon shugaban Cibiyar Koyon Finafinai ta Ƙasa

February 15, 2026
Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6
Labarai

Alƙali ya ci Samha Inuwa tara ko ta je kurkuku wata 6

February 13, 2026
Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira
Labarai

Hukumar EFCC ta kama jarumar Kannywood, Samha Inuwa, saboda goge majina da takardun naira

February 3, 2026
Next Post
Hotunan Adamu Nagudu da iyalin sa tare da fatan alheri

Hotunan Adamu Nagudu da iyalin sa tare da fatan alheri

Comments 1

  1. Jamila Adamu Yaro says:
    5 years ago

    Ah masha Allah Allah kara tsawon kwana mai albarka Hajiya Balaraba, kinyi abun daya dace sosai, dukkan tafiyan rayuwa babu yanda za a gama shi ba tare da mace ba, amma dayawan abubuwa sai ana mantawa da mace. To masha Allah da Dr Ahmad ya karbi gyaran kuma gyara yayi kyau. Allah taya riqo gaba daya, Allah ya kawo mana karshen wan nan masifa ta shaye shaye aminn Ya Hayyu Ya Qayyum..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!