A SAFIYAR yau aka yi jana’izar shugaban Ƙungiyar Mawaƙa ta Jihar Kaduna (NALSU) kuma memba a haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Muhammad Sani Shu’aibu (Ciyaman), wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren jiya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Sani Ciyaman ya rasu ne a gidan sa da ke Titin Maƙera, unguwar Rigasa, Kaduna, da misalin ƙarfe 7:30 na dare a jiya Talata, 21 ga Satumba, 2021.
Shekarun sa kimanin 39 a duniya.
Marigayi Sani ya rasu ya bar mahaifiya sa, da matar sa ɗaya da kuma ‘ya’ya huɗu duk mata.


Wakilin mu ya gano cewa marigayin ya ɗan kwana biyu ya na jinyar ciwon hanta, amma ba ya faɗa wa mutane.
Hakan ya sa ba kowa ne ya san ba shi da lafiya ba, sai dai kawai labarin rasuwar sa ya riski mutane.
Mutane sun kaɗu da jin labarin wannan babban rashi da aka yi domin kuwa Sani bango ne majinginar jama’a da dama, ba a iya ƙungiyar mawaƙan Jihar Kaduna ba, har ma ga Kannywood baki ɗaya.
An yi masa sallah a ƙofar gidan sa da misalin ƙarfe 8:30 na safe, daga nan aka wuce da shi maƙabartar unguwar, wadda ba ta da nisa daga gidan.

Wasu daga cikin ‘yan fim da su ka halarci jana’izar sun haɗa da shi Maikano da Abubakar Yarima, Ali Baiti, Sagir Baban Kausar, Malam Yahaya Makaho, El-Mu’az Birniwa, Dikko Yakubu, Musa Mairabo, Ibrahim Ɗanguziri, M. Suraj, Sulaiman Sha’ani, Musa Aminu Carlos, Muktar SS, Murtala Aniya da MD Anas.
Bayan an rufe shi an dawo, sai tsohon shugaban MOPPAN na ƙasa, Alhaji Abdullahi Maikano Usman, ya tara dukkan ‘yan Kannywood da su ka halarci jana’izar, ya yi masu nasiha tare da jan hankali kan rayuwa.
A cikin jawabin, Maikano ya ce, “Ya kamata mu yi wa kan mu faɗa, mu so junan mu, mu guji dukkan abin da bai da kyau, mu yi ƙoƙari wurin aikata ayyukan ƙwarai.”


Ya ƙara da cewa: “Ya kamata mu yi ƙoƙari mu taimaki iyalan mamacin nan. Sannan ba sai mun yi a ƙungiyance ba, duk wanda Allah ya hore masa ko da N1,000 ne, ba na raina N1,000 ba ne, a’a wannan N1,000 ko N500 da ka bada za ka ga sakamakon da za ka samu a kan ta. Kuma idan za ka bada ba sai ka bari wani ya sani ba, ka yi tsakanin kai da Ubangijin ka, ba sai wani ya sani ba.”
Mutane daga masana’antar fim da wajen ta sun ci gaba da tururuwa zuwa gidan mamacin domin yin ta’aziyya.

Daga cikin su akwai Hajiya Fatima Lamaj, wato shugabar MOPPAN reshen Jihar Kaduna a yanzu.
Allah ya jiƙan Sani Ciyaman, amin.
ALLAH KAYIWA SANI CHAIRMAN RAHMA, KA KYAUTATA KWANCIYARSA YA ALLAH.